← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 168

Sashe 156

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

zuciya yayi sannan yace yana zuwa. Zainab kuwa tana riƙe da kaskon turaren wuta tana yi suna waya da Inaya, dariya kawai take yi saboda tambayar da Inaya ke mata, Mummy ce ta shigo tana matse ƙwalla tana kiran Kabir tana cewa “Kabir kana ina? Nikam ina Senate ɗina tun bayan kwanciyarshi nima zazzabi ya rufeni daga asibiti nake kwanana bakwai ana yi mini ƙarin ruwa…” ganin Zee ne yasata yin turus, Zee ta kalleta ta kawar da kai ta cigaba da wayarta kamar bata ganta ba, kai tsaye ɗakin Daddy ta nufa tana cigaba da matse ƙwalla. Ta kai hannu zata buɗe Zee ta riƙe handle ɗin, da mamaki ta kalli Zee tace “Auta oyoyo Allah yayi kin dawo ya jikin Senate? Har yanzu jiri nake ji.” Bayan wuyanta Zee ta shafa tare da waigawa sai kuma ta juyo tace “Wa zai mayar dake asibiti?” Tayi murmushi tace “Na warke ai.” Kai Zee ta girgiza tace “Ahh a hakan?” Da yake Mummy bata shirya barin gidan yanzu ba sai cewa tayi “Zainab please kar mu tsaya sa’in sa.” Hannu tasa ga mamakinta key ta ciro cikin aljihun wandonta, a gaban Mummy tasa key a kofar ɗakin sannan ta girgiza mata key ɗin tasa a aljihunta tace “A gaida Inna, kar ki manta ki kwashi kayanki,” tana kai nan ta maida waya kunnenta suka cigaba da hira da Inaya, a fusace Mummy ta fice ta bar gidan. Kabir ne ya fito daga ɗaki yana dariya ashe tunda ta shigo yazo fitowa ya jisu da Zainab yace bari ya ƙyalesu, kallonta yayi yace “Bani key ɗin zan zauna wurin Daddy please taimaka ki amso mini saƙo wurin wani abokina a Gusto yazo daga Abuja zai wuce ni kuma Daddy na buƙata ta kinga har text yayi min, kallon shi tayi kafin tace “Kai dai baka so na huta wallahi,” tayi maganar tana bashi key ɗin bata wani canza kayanta ba kawai abaya tasa baƙa a sama tayi rolling tare da sa sun glasses ta fito. Baqeer ne ya fara isa ya shiga sai dai bai ga inda mutumin yake ba, gashi waiters har sun bashi wurin zama, ruwa ya sha yana duba agogon hannunshi na apple watch, ganin har minti ashirin ga Salim yaƙi ɗaukan wayarshi yasa kawai ya yanke shawarar tafiya gida, turo electric wheelchair ɗinshi yayi yana zuwa jikin ƙofar fita ya ja ya tsaya saboda abinda idanunshi da zuciyarshi suke hango mishi, Zee ce tafe ɗauke da waya a kunnenta da alama Kabir take kira ganin bai ɗauka ba yasa taja tsaki tana waigawa idanunta ya sauka akan abinda zuciyarta ta daɗe tana muradin gani, nan da nan zuciyoyin mutanen biyu ta karye, kallon juna suke kamar yau suka fara ganin juna, wasu mutane ne suka zo shigowa ɗaya saura kaɗan ta buge Zee, Baqeer da sauri ya mata alama da hannunshi akan ta matsa, matsawa tayi tana waigawa sannan ta sake maida ido kanshi, wani abu ya haɗiya yana jin kamar yaje ya rungumeta sai dai ya sani wannan lokacin akwai saura. Takowa ta fara yi shima yana turo kekenshi har suka haɗu a tsakiya, hawaye ne suka gangaro saman kuncinta ta saki wani murmushi wanda kana gani kasan kuka ke neman ƙwace mata tace “Ya Baqeer?” Ji yayi sunan ya ratsashi don abinda ya dade yana begen ji kenan, murmushi ya sakar mata yace “Zainab!” Ido ta runtse ta sa bayan hannunta ta goge bayan idonta tace “Ka canza.” Ta nuna kekenshi tana dariyar dake ɗauke da gudun hawaye, kai ya daga mata yace “Hmm ba kya nan lokacin.” Kai ta sake jinjinawa tana share ƙwalla tace “Umm bana nan.” Kallon juna suka yi suka saki murmushin da su kansu sun san na missing ɗin juna ne. Kai ya nuna mata alamar su zauna, kai ta jinjina ba tare da ta musa ba suka wuce suka zauna. Menu aka kawo musu ya miƙa mata tare da ɗaga mata kai yace “Yi mana order.” Ta saki murmushi sai kuma tasa hannu biyu ta rufe fuskarta hawaye na zubo mata tace “Ya Baqeer kasan Daddy yayi hatsari?” Tausayinta ne ya rufeshi ya cire tissue ya miƙa mata yana cewa “Umm naji.” Amsa tayi tace “I am really scared in ya bar duniyar nan fa? Ya zanyi? Ina zani?” Ido ya zuba mata yana jin ƙauna da tausayita na dawo mishi sabo fil yace “Ko mu fita?” Kai ta ɗaga don ba abinci ne a gabanta ba ganinshi ya gama ƙosar da ita kuma tana son kaɗaicewa da Baqeer.
Chapter 156 · 0% Book details