Sashe 10
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ƙarfe shida da wasu Umma ta sauka daga adaidaita ta shiga cikin gidan, babu kowa a tsakar gidan wanda hakan yasa tayi tunanin ko sallah suke yi, sai data haɗa murhu tasa ruwa a tukunya sannan ta shiga ciki tayi alwala tayi sallah, a sujjadarta ta karshe addu’a kawai take yiwa Baqeer wanda ko miƙewa ta kasa yi, ta daɗe a haka sosai kafin ta dago ta ƙarasa sallar, ta cire hijab ɗinta sannan ta fito waje hannunta ɗauke da robar da zata yi amfani dashi gun yin talge, cak ta tsaya ganin ruwan nata babu alamun zafi bayan ta tabbatar yaci ace ya tafasa a lokacin, da mamaki ta ke kallon tukunyar.
“Umma ni na juye ruwan wanka zan yi, kin dai san tun jiya ina asibiti wurin Baqeer.”
Da sauri ta kalli Bashir cike da jin daɗin ganinshi tace “Bashir mun gode sosai Allah ya ƙara haɗa kanku, dan Allah gobe zaka iya komawa wurinshi? Yau Salim yace zai kwana.”
Jamila ce ta fito kamar wacce dama take jiran kiris tana tafa hannu kafin tafe “Tab! Yau naga abinda ya hanani sukuni. Ɗan lelen nawa ne kike maganar ya zama mai jinyar Baqeer? Ko kin manta yadda kuka dinga nuna mana mu bamu isa ba a gidan nan? Ko kin manta yadda Malam yasa ɗanki makarantar masu kuɗi ya maka namu a ta gomnati? Sannan duk abin nan kina kallo shine yanzu yaran nawa kun ganshi da lafiyarshi jinin da aka yashe mishi bai isa ba sai an haɗa ga gangar jikinshi?”
Sakato Fatima tayi kafin ta koma ta zauna kawai ta janyo garin tuwo dan tasan halinsu yanzu tana tankawa zasu maida gaba ɗaya laifin abinda ke faruwa kanta, wani banzan kallo Jamila ta mata sannan tayi wa Bashir alamar ya wuce yaje yayi wankanshi.
*******
A hankali ta kwankwasa ƙofar ɗakin sannan ta buɗe zaune yake akan gado hannunshi ɗauke da controller na game, yana ganinta yayi dariya yana yin game ɗin yana cewa “Mummy ni kam pretending ɗin rashin lafiyar nan ya isheni, I just wanna go out and chill.”
Zama tayi daga gefen gadon ta ɗan harareshi tace “Kasan da haka wa yace ka aikata abinda kayi?”
Cak ya tsaya sannan ya kalleta narai-narai da ido yace “Har kin gano?”
Hannu ta kai saitin kunnenshi da sauri ya rufe kunnen yace “Allah Mom I didn’t do it on purpose yaron ne kawai ya taho yayi jumping a gabana, ke kin san yadda nake tu(i da hankali, sannan tsoron ruining reputation na Dad yasa ban tsaya a wurin ba.”
Harararshi ta sake yi tace “Yanzu me kake tunanin zai faru in akwai wanda ya ganka? Sannan kama sa ɗan gidan waye?”
Da mamaki yake kallonta yace “Do I have to know?”
“Ɗan gidan Badaru…..”
Cikin ɓacin rai yaja tsaki yace “I just hate that guy wallahi tun muna yara, wai dama shine? Matslarshi ce sannan da nasan shine ma bayan na bige shin sai na takashi da mota zan wuce.”
“Kai dai baka ji ba kuma zaka daina ba ko? Yanzu da ban ɓoye akan kana gida ba me kake tunanin zai biyo baya?”
Kallonta yayi ya kwantar da kanshi a kafaɗarta (Wai su a dole turawa) yace “Sorry Mummy! Zan kiyaye.”
Ta dan shafi sumar kanshi tace “Yauwa please ka kula, sannan Zainab ta kusa dawowa ɗazu mu kayi waya da ita.”
Baki ya taɓe yace “I don’t care, kin san yadda yarinyar nan ta rainani, tana ganin yanda Nabila take girmamani ita da take Aunt ɗina ma.”
Murmushi kawai Mummy tayi don in da sabo sun saba, ta fito daga ɗakin ta nufi part ɗin mai gidan nata.
******
Baba ne ya kalli Dr yace “Ni dai koma menene ina so ku sallameshi gobe zan zo da safe mu tafi, yana da abubuwa da yawa a gabanshi wanda bazan iya barinshi a asibiti ba, sannan kuma bana ji kuna da wani abinda zaku iya yi mishi kuma, gwara ni in na dage zan koya mishi ya dawo yanda yake da.”
Da mamakin kalamanshi Dr yace “Wai Alhaji ni kam kasan risk na abinda kake magana akai kuwa? Taya za kai pushing ɗin shi bayan kasan wannan ciwon ba wai abin wasa bane? Magana fa nake yi maka akan ba zai iya komai da kafafun ba.”
Hannu ya ɗaga mishi yace “Ɗana ne kuma ni ke da iko dashi, yana da gasar da zai yi wanda ni bazan bari ku salwantar mishi da shi ba, zan zo gobe.” Yana kawai nan ya fito daga office ɗin kicibus suka yi da Bello wanda gabanshi ke faduwa na jin kalaman Dr dan ya zo duba Baqeer ya hango Baba shine ya zo yayi mishi ya mai jiki ya tsaya a waje akan su gama magana daga nan kunnuwanshi suka juyo mishi waɗannan kalamai.
Wani mugun kallo Baba yayi mishi yace “Nasan dama kana da ƙarancin tarbiyya amma ban san abin naka ya kai har ka dinga laɓe ba.”
Da sauri Bello yace “Baba ba haka bane nazo duba Baqeer ne na ganka shine nazo na gaisheka.”
“Kaine ka kira Baqeer akan yaje majalisa ranar da abin nan ya sameshi?”
A tsorace Bello ya kalleshi ya fara neman tattaro amsa, juyawa kawai Baba yayi ya wuce ya barshi anan wajen a tsaye.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
Umm Asghar Ce
Da
Ayusher Muhd
BAQEER
NA
AYUSHER MUHD
DA
UMM ASGHAR
RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA BAKWAI