← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 168

Sashe 26

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaye take a jikin balcony na gidansu wanda daga gefe take hango mutanen biyu wanda ta gansu kwanaki ta kuma ga na keken shekaran jiya, hannayenta a harɗe a kirjinta duk abinda ke faruwa akan idanunta, yanda taga yana kallon gaba kaɗan da inda yake ne yasa ta kalli wurin, dan hasken fitilun gidan su ya haska layin, idanunta ne ya sauka akan yarinyar da ta wulakanta gurgun kwanaki, kana kallonta kasan soyayya suke yi da wanda ke tsaye kusa da ita, wani murmushin takaici tayi tare da girgiza kai, ta rasa me yasa maza sam wasu basubsan me ya dace dasu ba, kalaman wanda ke kusa da gurgun ne ya katse ta yana cewa “Please ka furzar da iskar dake bakinka, ka taimaka kayi magana.”
Nan da nan takaici ya sake rufeta ta rasa me yasa ita bata ganin abu ta ƙyale, wayarta kawai ta ɗauka ta fito daga gidan, kusa dasu kaɗan ta tsaya tana yi kamar mai yin waya tana cewa “Some people are just helpless, sai su dinga zuwa inda ba’a nemansu, in kasan ba’ayi da kai you just need to move on, amma wasu kamar basu da zuciya, sannan gani suke kamar in Allah ya jarabcesu rayuwarsu ta riga ta tsaya kenan.”

Waigawa Baqeer yayi don kalamanta kaf cikin kunnuwanshi kuma tabbas muryar nan dai ita ce wacce tayi mishi magana sau biyu. Kafin yayi ƙoƙarin yin magana tayi gaba…..

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

#Baqeer
#Shalele
#Asiya
#Zeey
# RayuwadaKaddara
#Hawayena
#UMMASGHAR
#AYUSHERMUHD
*BAQEER*
     *NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*

*PAID BOOK*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA SHIDA*

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

08142800199
07068558096

{16}
Kallon Salim yayi bayan ya ɗauke kanshi daga kallon inda yarinyar ta suce, muryarshi cikin sanyi yace "Salim taimaka mu koma gida."
Babu musu Salim ya fara turashi, bai sake iya waiwayen su Bello ba don wani irin zafi da ƙuna yake ji a zuciyarshi, tabbas Asiya da Bello sun yi mishi abinda bai taɓa tunanin wani mahaluki zai yi mishi ba, yana gani ana cin amana amma bai taɓa kawowa zai zo kanshi ba.
A ƙofar gida suka tsaya ganin ƴar ƙofar shiga gidan a kulle, da mamaki suka kalli juna don ba'a kulle gidan sai ƙarfe sha ɗaya na dare, ya zaro wayar dake aljihun gaban rigarshi yaga tara da rabi, nan yasa hannu ya ɗan buga kofar gidan, basu jima ba aka zo aka buɗe, hankali a tashe suke kallon Baba dake tsaye a ƙofar, bai yi wani auni ba kawai ya tsinke Salim da wani irin mari, a razane Baqeer yace "Baba?" Ai bai tsaya saurarenshi ba yace "Kasan Allah in har na sake yi maka magana ka take umarnina gidana hana ka shiga zan yi, kai a duniyar Allah ba'a koya maka bin maganar manya bane? Nasan ka taso ba mahaifi ina yi maka uzuri tunda mahaifiyarka da tayi aure ajiyeka tayi gun iyayenta wanda dama kowa yasan tsofafi ba tarbiyar da zasu iya badawa, amma naga alama uzurin da nake baka sam baya shiga cikin kunnenka, to wallahi ka fita idona na rufe kaji na faɗa maka."
Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Salim ya kalli Baqeer da kunyar duniya ta rufe shi yace "Baqeer kayi hakuri amma ba zaka sake ganin na tako ƙafata gidan ku ba." Daga haka yayi gaba yana share kwalla, an daɗe ana ci mishi mutunci amma bai taɓa jin zafi ba kamar wanda mahaifin Baqeer yayi mishi duba da yadda yake tunani iya ƙoƙarin yana yiwa ɗan shi, to menene laifinshi? Banda yana tausayin Baqeer dama da tuni sun raba abota. Juyawa Baba yayi ya barshi a zaune akan kujera a ƙofar gida, Umma na ta safa da marwa a tsakar gida, Jamila na daga gefe tana kallonta, ita kuwa Abu yau banda shirin tarbar mai gida babu abinda take yi.
Baba yana shiga kai tsaye ɗakin Abu ya wuce ba tare da ya tanka musu ba.
Da sauri Fatima ta zura hijab ta leƙa waje, yana zaune yadda kasan ba mai rai ba ko motsi baya yi, tunani kawai yake yi ina ne zai je ya zauna yayi rayuwarshi bayan nan gidan? Ina yake dashi da zai tattara ya tafi ya zauna shi kaɗai? Ganin Umma ne yasa zuciyarshi ta ƙara karaya kawai ya damtse hannu yana jin wani abu na sake tokare mishi zuciya.
Haka ta turashi cikin ɗakin, Kamalu na zaune yana kallon ball a wayarshi, ta kalleshi cikin sanyin murya tace "Kamalu din Allah taimaka mishi ya kwanta."
Wani kallo ya watsa mata yace "Ya kwana a kujerar in dai ni ne zan taimaka mishi."
Wani kallo Baqeer yayi mishi zuciyarshi na takaicin yadda yake yiwa mahaifiyarshi magana sam babh respect, sai dai me zai ce? Bayan a dalilinshi ne ake faɗa mata magana?
Kallonshi tayi tace "Kana gani zaka iya in na taimaka maka?"
Zuciyarshi ce ke sake rauni tausayinta na ƙara kamashi a hankali ya ɗaga kai, haka ya dinga ƙoƙarin akan kar ya sakar mata nauyinshi gaba ɗaya wanda dalilin hakan yasa sai kifawa yayi, nan ya shiga jan jikin shi iya karfinsa, ganin yadda yake yi yasa bata ƙara takurawa akan sai ta taimaka mishi ba.
Haka ya kwanta kawai yayi shiru don yasan bacci kam yau ko barawo ne ba zai ɗauke shi ba.

******
Iska Zeey ta furzar iya karfinta cikin tsananin ɓacin rai ta fara fifita da hannunta tana dafa ? ɗin apple dake table ɗin ɗakin “Wai Zeey baza ki faɗa mini menene ya ɓata miki rai ba? Nasan dai ba shakkar gobe Daddy zai dawo kike yi ba? Balle nace kina tsoron abinda Najib zai je yace ne ya dawo kanki.”
Zama tayi a bakin gado tace “Aunty N please ki duba mun wannan abun, wani ne……” Sai kuma tayi shiru ta fasa maganar, to ita tace me? Wani wa? Baya kawai tayi da kanta kan katifa cikin ɓacin rai don tasan bakin Nabeela baya shiru in har tayi magana to yanzu zata ji maganar wurin Kabir azo ana tambayarta menene nata na shiga abinda bai dameta ba, wa zata faɗawa ko zata huce? Tsaki tayi da takaicin rashin amsar number Maryam da tayi dole gobe ta duba gidansu taje ta gaida Umma ta amso tun kafin Daddy ya dawo ya hanata fita.
Da wannan tunanin ta kwanta sai dai har tayi bacci takaicin saurayin ya isheta, ita a rayuwarta ta tsani taga ana wulakanta mutum yana mannewa a wuri.

******
A kafadar Mummy tasa kanta tace “Mummy please kinga ba dadewa zan yi ba.”
“Kuje ke da Nabeela ai tafiyar biyu dai tafi ko?”
“Please Mummy ni kaɗai nake son zuwa sannan ko 30minutes bazan yi ba zan dawo, i promise.” Zeey tayi maganar tana kallonta don tasan in har taji ina zata je tofa ko zata mutu ne ba barinta za ayi ta fita ba.
Cikin kokonto Mummy tace “Baby don Allah karki dade yau Daddynki zai dawo in har ya dawo ba kya nan bansan me zance mishi ba.”
Kiss ta manna mata a kunci tace “Max 1hr.” Tana kawai nan ta fito da sauri hannunta riƙe da key na motar Nabeela don Daddy ya hanata fita, balle in aka san inda zata je ko mutuwa zata yi babu mai barinta taje, sam itama ba son zuwa gidan take yi ba number Maryam kawai take son ta amso ta kuma gaishe da Umma daga nan kuma In Sha Allahu bazata sake komawa.
Da sauri ta fito ta faɗa mota sannan ta fita daga gidan, ta ina zata fara duba gidan? Don rabonta da gidan har ta manta, gaban yaron dake sayar da rake akan titi ta tsaya tace “Don Allah kasan gidan su Maryam?”
Da mamaki yace “Maryam wacce?”
Tace “Kanwar Hadiza?” Nan ma yace “Bangane ba.”
Ƙasan leɓenta ta ciza sunan dai da bata son ambata a dole ta kula sai tayi.
“Maryam ɗin Baqeer.”
Nan fa yaro yace “Oh na gane.” Ya shiga yi mata kwatance da hannu, tayi godiya tare da bashi 1k sannan ta ja mota ta tafi shi kam sai godiya yake zubawa.
A nesa da gefen gidan ta tsaya tana tunanin ta yadda zata taka kafafunta zuwa cikin gidan, gidan da sam tasa a ranta ba zata ƙara zuwanshi ba, sai dai darajar Umma da Maryam fa? Abinda yazo mata kenan wanda yasa ta shafar fuskarta, ta tabbatar Baqeer ba zai ganeta ba, kuma ƙila harta shiga ta fito ma bai san tana nan ba.
Chapter 26 · 0% Book details