← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 168

Sashe 49

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*****
Baqeer ya ɗan jima kafin ya dawo, sai dai kafin ya dawo Zeey ta tafi don yana tsaye tazo ta wuce bai kula ba, sai ita data ganshi, ta dade a gefenshi daga baya sai da taga yana shirin tafiya sannan ita ma ta tada mota tayi gaba, zuciyarta duk ba daɗi. Gidan Inna ta wuce kai tsaye.
Inna na ɗaki tana ƙirga kuɗi tana jin Zeey ta ɗaga katifa ta sakasu sannan ta kuna radio tana ji kamar ba a gidan ake sallamar ba.
Zee ce ta shigo tace “Hajiya Inna tawa dama nasan kina ciki magana ce bakyajin yimin.”
Fuskar nan tata a ɗaure babu alamun fara’a tace “Tunda ke bakinki bazaiyi shiru ba sai kin faɗa ai ba laifi.”
Zama tai tace “Hmm Allah dai ya kawo randa zaki saki rai dani.”
Wani kallo ta mata tace “Yau kuma me ya kawoki? Bayan ba san zuwa kike ba?”
“Aunty Nabila fa? Batanan?”
“Ba’a sani ba, wai mai aikin ku ce Nabilan da baza’a barta tazauna a gidansu ba? Bayan in taje gidan naku banda aiki ba abinda kuke sata?”
Kai ta girgiza tace “Kedai Inna neman faɗa kike amma yaushe aka sakata aiki a gidan?”
A fusace Inna tace “Ke ai ba’a isa ai magana ba sai kin bada amsa san ranki, wannan halin naki yasa sam bana sake miki an bi an sangartaki ace komai ya fito daga bakinki sai kin faɗa? Sannan Nabilan karya akai ko gadan da kika kwana na zakice ba ita ke gyarawa ba?”
Mikewa Zeey tai tace “Bari na shiga ɗaki na huta in kin huce mayi maganar.”
Tana kainan ta fita nan fa Inna tahau faɗa Zeey kam ko a jikinta ɗaki ma ta shiga ta baje a kan gado tana tunanin abinda ya faru tsakaninsu da Baqeer.

******
Bayan magriba ne Daddy ya halarci babban falon bakinshi inda ya gayyato dattijan unguwar, anyi abinci kala-kala yadda kowa zai ci ya ƙoshi, sosai yaji dadi da aka ce Zeey bata nan shi yasa ko faɗa bai yi ba a ƙalla babu abinda zai bashi matsala.
Zama suka yi duk wuri ɗaya ana ci ana hira kowa na yaba miah da bashi tabbacin zai bashi gudunmawa ɗari bisa ɗari.
Badaru ne ya sauka gaban mai bread zai sayi na karin safe.
Mai bread ya kalleshi yace “Malam Badaru har kun gama taron ne?”
Da mamaki yace “Taron me kuma? Don ni dai daga kasuwa ma nake.”
Taro dai da za ayi a gidan Alhaji Suleiman Karaye ko da yake kai ai kowa yasan ba kwa shiri to na tabbatar shi ya hanaka zuwa.”
Nan da nan Baba ya gimtse fuska tamm, ranshi ya ɓaci sosai yace “Yanzun taro ake yi a unguwar babu ni?” Yana kaiwa nan ya amshi bread ɗin shi ya nufi gida, a waje ya bawa almajiri ya miƙa mishi ciki sannan ya wuce gidan Suleiman Karaye, dole ne yaci zarafinshi don ba zai yarda da wannan iskancin ba, ai ko ba zaije ba sai a faɗa mishi yace baya son zuwa yafi yaji a titi.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Muhd Ce*
*Da*
*Umm Asghar*

*BAQEER*
     *NA*
*UMM ASGHAR
      *DA*
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN*

{30}

Almajirin da Baba ya bawa saƙo ne ya shiga cikin gidan yana sallama, Jamila ce kaɗai a tsakar gidan tana alwala, Abu da Umman Baqeer duk sun shige ɗakunansu suna sallar isha'i. Miƙa mata ledar yayi yace "Wai gashi aka ce na shigo dashi ciki". Karɓa tayi ta latsa ledar sai taji biredi ne, ajiyewa tayi a gefe tace mishi "To jeka angode." Sai da ta gama alwalar sannan ta ɗauke ledar ta shige da ita ɗakinta ta buɗe durowa ta ajiye tana cewa "Wannan biredin dai ya shigo kenan wallahi sai dai ka sayi wani baƙin munafuki, da haka zaka ɗauka ka kai mata ku cinye ba tare da mun san anyi ba." Hijabi ta ɗauka ta kabbara sallah ranta fal farin ciki don wallahi babu mai karɓar biredin nan a hannunta yau, suma sun samu na karyawa da safe ita da yaranta.

Shi kuwa Mallam Badaru ya nufi gidan Alhaji Suleiman Ƙaraye yana ta zage-zage a hanya kamar wani sabon kamu. Tun daga gate maigadi ya tsayar dashi ya hana shi shiga nan ma ya rufe shi da masifa yana cewa "Da zaka hanani shiga ni ba dattijon unguwa bane? Ko kuwa ce maka aka yi kada ka barni na shiga wurin taron da ake yi? owoo wato kun san abinda kuka taka baku da gaskiya shi yasa kuke ƙoƙarin hanani shiga?"
Mamaki ya rufe mai gadi ganin ba zai iya da jidalin Mallam Badaru ba yasa ya buɗe mishi ƙofa tunda yasan ana taron da yace mishi yazo a cikin gidan. Wucewa yayi ciki yana ayyana tabbas sai yayi wa Suleiman Ƙaraye rashin mutunci irin wanda bai taɓa zato ba, don cin fuska da rashin mutunci har ya shirya taron manyan unguwa a kasa sanar mishi saboda munafurci, haka ma fa kwanaki da yazo ya saka mishi kuɗi a aljihu irin ga ɗan maula yazo, sannan shi fa har yanzu ba wai ya yarda da cewar da yayi ba ɗanshi bane ya nakasta mishi yaronshi ba kawai dai yayi shiru ne ganin baya da tartibiyar shaidar da zai gabatar.

Yana shiga parlourn da ake taron sai ya tarar da mutanen unguwar wanda yawancin su abokan hulɗar shi ne ana ta raha ana cin abinci babu wanda ya kula da shigowar shi wurin. A take yaji ranshi yayi wani irin ɓaci cikin fusata yace "Ehh yau na tabbatar da mutum mugun icce ne shine don munafurci za'a shirya taron manyan unguwa a kasa shaida mini saboda an mayar dani saniyar ware, ko kuwa kun cireni daga cikin dattijan unguwa?" Ya kalli makwabcin shi Mallam Nuhu dake ta yagar naman kaza yace "Au don munafurci har da kai ake cin dunduniyata, Mallam Hamza? Alhaji Kabiru? Ashe dukkan ku munafukai nake tare dasu ban sani ba, ai dai kun san ƴar tsamar dake tsakanina da wancan mutumin" yace yana nuna Suleiman Ƙaraye dake zaune akan doguwar kujera yana kallon duk abinda yake yi fuskarshi ƙunshe da murmushi kamar ba taro Mallam Badaru yazo ya ɓata mishi ba, ya cigaba "Amma shine don munafurci har da ku a halartar taron daya shirya? Eh wato gani ni ba kowan-kowa ba shi yasa aka shirya taro aka kasa sanar dani, ko?"

Kowa dai yayi tsit sun zubawa Mallam Badaru ido yana ta zuba tijara sai mahaifin Bello ne ya taso yace "Haba Mallam Badaru ya kamata fa idan an girma a riƙa sanin an girma, ta yaya abinda ya faru tun da ƙuruciya zaka yita riƙe dashi har yanzu?" A take ya taso mishi da masifa kamar zai kai mishi duka yana cewa "Dalla gafara can yi mini shiru baƙin munafuki da wani munafukin gantalallen ɗanka maci amana. Waye kai da har zaka taso ka tareni kana faɗa mini maganar banza, in banda ma Baqeer daya janyo mini masifa da bala'i ya haɗa sabga da ɗanka kai ka isa ka kalli inda nake shine har zaka zo kana yi mini zancen banza, dalla matsa ka bani wuri, ko sanda aka yi abun ka sani ne? Sai shishigi kamar an aikeka." Sai a lokacin Suleiman Ƙaraye ya taso cikin lumana saboda ya kare mutuncin shi dana kujerar da yake nema yace "Haba Mallam Badaru ya kamata mu manta duk wani abu daya faru lokacin ƙuruciya a yafi juna haka nan, bai kamata ace har girman nan namu da muka fara ajiye jikoki ana jin kanmu akan ɗan abinda bai taka kara ya karya ba."

Ai kuwa dai ranshi yayi mummunan ɓaci don yana ganin rainin wayo kawai Suleiman ɗin ke neman kawo mishi irin wanda ya saba yi mishi tun da can don haka yayi ta bala'i yana masifa har yana cewa in dai yana raye Suleiman Ƙaraye bai isa hawa kujerar senator ɗin da yake hari ba don sai ya tabbatar ya nunawa mutane asalin waye Suleiman Ƙaraye da ɓoyayyiyar manufarshi akan su. Da ƙyar dai aka samu aka fitar dashi daga cikin gidan yana ta zage-zage yana masifa, bayan fitarshi sai suka hau zancen ba'a san meke damun shi ba da sam baya so a zauna lafiya. Wani yace "Ai kun san tunda iftila'in nan ya faɗawa ɗan shi ya koma kamar wani zararre, watakila dan ganin burin da yaci akan ɗan ba zai cika ba ƙwaƙwalwar shi ta taɓu."
Chapter 49 · 0% Book details