← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 168

Sashe 13

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

An ɗauki lokacin tana yi mishi nasiha akan falalar haƙuri da karɓar ƙaddara a duk yadda ta zowa bawa har ya samu ƴar nutsuwa ya daina kukan da yake yi. "Umma Baba fa, ya zan yi dashi bayan ya kasa gane a yanzu babu abinda zan iya yi da hannuna, gani yake yi kamar da gangan naƙi yin abinda ya sakani?" Yayi maganar idanunshi akan hannunshi na dama yana jujjuyasu a hankali, yana ayyana ko sai yaushe zai fara amfani dashi wajen yin zane kamar da.
"Shima haƙurin zaka yi dashi har ya fahimci ba yin kanka bane ƙaddararka ce tazo a hakan ya sauko, kasan yadda ya ɗora dukkanin wani buri nashi a kanka lokaci guda hakan tazo ta faru dole abun ya dakeshi to amma ya zamu yi bayan muyi haƙuri mu fawwalawa Allah dukkanin al'amuranmu In Sha Allah yana sane damu ba kuma zai ƙyale mu a haka ba zai kawo mana mafita ta inda bamu yi tsammani ba, kayi haƙuri kaji ka cire komai daga cikin zuciyarka sai kaga Allah ya dafa maka."

Miƙewa tayi zata fita sai kuma ta dakata tace "Ko akwai abinda kake so nayi maka kafin na fita, ba dai wani daɗewa zan yi ba wanki kawai zan je in ƙarasa yanzu zan dawo, dazu na fara na ajiye." Girgiza kanshi yayi yace "Babu wani abu Umma har kin gama ki dawo ina nan ai ba wani wuri zan iya zuwa ba." Sai taji tausayinshi ya ƙara kamata, wai yau Baqeer ɗinta ne ya dawo haka, Ya 'Allah ka sauƙaƙa mishi ka bashi ikon ɗaukar wannan ƙaddarar daka sukar mishi' ta samu kanta dayi mishi addu'ar a cikin zuciyarta.
'"Ko dai zaka kwanta kafin na dawo don naga kamar ba wani jin daɗin zama akan kujerar kake ji ba?"

"A'a Umma barni a zaune kawai don na gaji da kwanciyar nan ciwon jiki take sakani."
"To ai shikenan, bari naje nayi maza na gama na dawo, don Allah ka cire komai daga cikin ranka kaji? Kada ka zauna kana tunane-tunanen da baza su ƙare ka da komai ba sai yawan damuwa."
"To" kawai yace mata cikin ranshi yana cewa tunani kam ai ya zama dole a wurinshi a yanzu tunda baya da wani abun yi da zai ɗauke mishi hankali daga halin daya samu kanshi a ciki.

*****

Baba kuwa yana fita ɗakinshi ya shige ya fara shirin fita kasuwar da duk kwanakin nan bai samu yaje ba don ma Allah yasa yana da yara masu kular mishi da harkokin kasuwancin nashi ai da ba ƙaramar asara ya tafka a cikin kwanakin nan da yayi ta sintiri a asibiti bai je ba gashi alamu sun nuna ba lallai ne ya samu abinda yayi sadaukarwar domin shi ba tunda Baqeer nema yake yi ya watsa mishi ƙasa a ido abinda bai taka kara ya karya ba na neman gagararshi, yayi fatali da dukkan wani ƙoƙarin shi da jajircewarshi wajen ganin sun cimma nasara ya cika burinshi. Har ya gama shiri ya bar gidan zuciyarshi bata daina tafasa ba hakan yasa ko sallam bai yiwa matan gidan ba yasa kai yayi ficewarshi. Koda yaje haka yayi tayi wa yaran nashi masifa, abu ƙalilan zasu yi mishi sai ya rufe su da faɗa, gaba ɗaya ya rasa nutsuwarshi tunanin ta yadda zai takura Baqeer yayi zane kawai yake yi, har tunani yayi to ko wani zai nema da ya iya zanen su tafi wajen gasar tare yayi zanen a madadin Baqeer idan yaso shi sai ya biyashi, tunane-tunane dai iri-iri babu wanda bai yi ba na neman mafita amma kasa samun matsaya guda ɗaya da zai kama. Dole ne ma Baqeer ya dage ya ƙarfafi zuciyarshi ya cigaba da zanen idan ba haka ba kuwa sai dai shi da uwarshi su biyashi duk abinda ya kashe akan harkar zanen Baqeer ɗin.

Yana cikin waɗannan tunanin ne aka kirashi a waya, sai da gabanshi ya faɗi daya duba yaga Yallaɓai ne ke kiranshi. Ido kawai ya zuba yana kallon screen ɗin wayar tana ta ƙara ya kasa amsawa saboda dai bai san kuma me zai faɗawa Yallaɓai ɗin ba, sai da ta kusa katsewa sannan ya amsa wayar cikin sallama. Ko gaisawa Yallaɓai bai bari sun yi ba yace "Haba Mallam Badaru, ta yaya zan yi ta nemanku a waya kuna raina mini hankali bayan kasan tafiyar nan ta matso, idan Baqeer ɗin ba zai iya ba tun wuri ba sai ka faɗa mini ba a nemi wani sai kayi ta yi mini yawo da hankali".

A ladabce kamar yana gabanshi don har ɗan russunawa yake yi yace "Kayi haƙuri Yallaɓai wallahi wata ƴar matsala aka samu shi yasa kaji har yanzu ban nemeka ba, amma ya za'a yi mu raina maka hankali".

"Yanzu ina Baqeer ɗin? Ina fata dai ya gama shiryawa don kasan gobe ne zamu je wajen deputy gwamna a game da batun tafiyar." ya katse shi ba tare da ya bari ya gama jin me zai ce ba. Shiru Mallam Badaru yayi yana juya ta inda zai fara faɗa mishi abinda ya samu Baqeer ɗin. A ɗan tsawace yace "Wai wani abu ya faru ne Mallam Badaru da kake ɓoye mini?"

"Wallahi Yallaɓai tsautsayi ne ya afku da Baqeer, yau sati guda kenan da mota ta kaɗeshi ya karye a ƙafa da hannu, zancen nan da nake yi maka ma dai ya zama gurgu don ance ƙafafun nashi sun tashi daga aiki," yayi maganar yana jin baƙin cikin halin da Baqeer ya sakasu a ciki, daya zauna a gida bai fita shegen yawonshi na tsiya ba ai duk da haka bata faru ba gashi nan yanzu suna nema suga samu suga rashi.

Cikin wani irin fushi Yallaɓai yace "What? Karaya? Kana nufin karaya dai? Kuma shine kayi shiru da bakinka kaƙi faɗa mini na nemi wani, wai me yasa mutane sam baku san ku rama alkhairi da alkhairi bane, ka barni anan sake da baki zamu je wajen taron nan da ɗanka ashe shi ya zama useless ni ban sani ba, sai kayi gaggawar dawo da kuɗin tallafin da kuka karɓa daga hannun gwamnati don kasan dai ba bar muku za'a yi ba tunda ba zuwa zai yi ba."

Shi dai haƙuri kawai yake bayarwa kamar ya ari baki, haka Yallaɓai ya kashe wayarshi yana ta masifa yana mamakin halin mutanen wannan zamanin da basu san komai ba sai son kansu da yayi musu yawa. Wayar Bello ya ƙira, Bello yana ganin Yallaɓai ne ya amsa da hanzari don yasan ba zai wuce yaji abinda ya samu Baqeer ba shine yake kiranshi. Cike da ladabi ya amsa yana gaisheshi, sai bayan sun gama gaisawa sannan Yallaɓai yace "Ni zaku maida karamin mutum? Ashe abinda ya samu abokinka kenan shine kuke ta ɓoye-ɓoye kuka kasa faɗa mini na nemi wani gashi gobe zamu je wajen deputy gwamna? Ƙaramin mutum kuke san maidani?"

"Wallahi kuwa Yallaɓai, accident yayi sai kuma abu yazo da tsautsayi ya rasa ƙafafun shi gaba ɗaya."

"Mts... Allah dai ya bashi lafiya amma ni damuwata ta yadda zan nemi wani contestant ɗin a tsakanin yau da gobe wanda zai maye gurbunshi kawai tunda ko be karye a hannu ba ƙafafunshi sun tashi daga aiki, taya zai shiga taro irin wannan akan keken guragu, wallahi Mallam Badaru ya ɓata mini rai don daya faɗa mini da wuri da tuni nasan abun yi, gashi mun riga mun aika sunanshi." Ya ƙarasa maganar rai a ɓace.

Dukkansu shiru suka yi kowa da abinda yake tunani a cikin zuciyarshi, Bello ne yayi ƙundunbalar cewa "Yallaɓai idan babu damuwa nace ko ni ba sai na wakilcemu? Tunda dai nima na iya zanen nan, asali ma abinda ya haɗa abotarmu da Baqeer ɗin kenan."

Wata nannauyar ajiyar zuciya Yallaɓai ya sauke kafin yace "Kuma fa haka ne Bello, ni ba na manta ba ashe kaima duk harkarku ɗaya, matsalar da za'a samu kawai wajen canja suna ne tunda mun riga mun miƙa sunan Baqeer a matsayin wanda zai wakilcemu, shi yasa ma abun ya dameni don sai da lokaci ya ƙure sannan aka samu wannan canjin amma In Sha Allah zan yi ƙoƙarin ganin an gyara komai ya koma da sunanka, kai dai ka zama cikin shiri don koyaushe zan iya nemanka, fatana kar canza sunan ya zama matsala.

"To Yallaɓai nagode Allah ya ƙara girma" yace cikin tsantsar farin ciki irin wanda bai taɓa tsintar kanshi a ciki ba "Yallaɓai in kana ganin sunan zai jawo matsala ina ganin ba matsala bane tunda ai dama da initials ake amfani to nima kuma sunana Bello Bala kaga Muhammad ɗin kawai za'a ƙara mini daga gaban sunan, kuma duk wani namiji ai Muhammad ne, ko ba haka ba?"

Wata irin dariyar farin ciki Yallaɓai ya saki ganin ya samu mafita yanzu-yanzu kamar ba shine ke tunanin neman replacement na wanda zai maye gurbin Baqeer ɗin da ke neman kassara shi ba.

(Wani abokin dai sai Allah, ga dai Bello ba kunya ba tsoron Allah, ga kuma mahaifin da ya kasa duba halin da danshi yake ciki.)

Baqeer
#Shalele
#Asiya
# RayuwadaKaddara
#Hawayena

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600 -
Uku 1200 -
Biyu 1000 -
Ɗaya 500 -

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

Promo zai kare zuwa wani satin, garzaya kisai naki🙌🏻💃🏻

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

BAQEER🦼
     NA
UMM ASGHAR
DA
AYUSHER MUHD

RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TARA

Dandano......

{9}
Chapter 13 · 0% Book details