Sashe 126
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zee tana shiga ɗaki akan gado ta faɗa ta kwanta, me yasa Ummi ke yi mata faɗa akan abinda tasan ba laifi bane, in ma ba haka ake yanka dankalin ba a matsayinta na uwa ai haƙuri zata yi tayi amfani da wanda ta ɓare amma sai ta hauta da faɗa? Mummy ce ta faɗo mata a rai don tasan tabbas da ita ce sai dai ma tace "Auta sannu, da fatan hannunki bai yi ciwo ba?" Kallon yatsunta tayi wanda har peeler ɗin ta ɗan karceta kaɗan amma gashi ita Ummi sam bata damu da tasan ma a wani hali ta fere dankalin ba, daga nan ɗaki take jiyo muryar Ummi da alama ita da Inaya ne don tana iya jiyo yanda suke magana cikin farin ciki, fitowa tayi da son sanin meke faruwa, nan ta taradda Inaya ce data dawo daga Tahfiz ta taho da kyauta taci na biyu, nan itama ta fara murna, sallama aka yi da gudu Inaya tayi waje tana kiran sunan Daada, Ummi ta kalli Zainab tace "Baban Inaya ne ki tashi ki sanyo mayafi." Tashi tayi tasa mayafi ta dawo, yana zaune a falo ya sa Inaya akan cinyarshi fuskarshi ɗauke da fara'a yana tsokanar Inaya, ganin Zainab yace "Ah ah ah ai ina ji ance Zainab tazo nace lallai dole na samu dama nazo wannan satin mu gaisa." Kanta ta sunkuyar kasa sannan ta rusuna ta gaisheshi tace "Ayi hakuri bamu zo mun yi gaisuwa da wuri ba." Har yanzu fuskarshi ɗauke da murmushi yace "Ah to kun dai san kun yi laifi, sai dai ita rayuwa wanda ya gane kuskurenshi yafe mishi ake yi." Ummi ce ta kira Inaya wacce ta ruga da gudu zuwa kitchen, ba daɗewa sai gata da tire da ruwa da cup a kai, ta ajiye sannan ta zuba ta miƙawa Daada tana cewa "Daada ka siyo min doll ɗin da kace? Mai gashi?" Gashin kanta ya ɗan ja kadan yace "To gashi ita kuma bata da gashi ina ga naki za'a gutsire a sa mata ko Ummin mu?" Shigowa tayi falon tana cewa "Kun fi kusa dai, baza kuji bakina ba." Bayan ya sha ruwan ya kalli Zee yace "Wai haka Yaya Babba?" Zee kanta tsaye tace "A'a kam bamu yarda ba." Ummy ce ta kalleta fuska a tamke, Zee a ranta tace "Me kuma na sake yi ni sarkin lefi." Kallon Ummi yayi ya ajiye cup ɗin hannunshi yana cewa "Daga ji dai girkin Yaya Babba zamu ci don wannan ƙamshin ma sai naji ya fita daban."
Ita dai Zee tayi ƙasa da kai sai take ganin kamar ma magana ake faɗa mata, Inaya ce tayi saurin cewa "Daada, Aunty fa tace mun bata iya girki ba." Wani kallo Ummi tayi mata wato har ma fariya take bata iya girki ba? Daada yayi dariya yace "Wasa take kin taɓa ganin babba kamar ta da bai iya girki ba?" Ita dai Zee sum-sum tayi ta bar falon don ji tayi bazata iya zaman ba, rai a ɓace ta ɗauki wayarta kawai idanunta ya gane mata kiran Baqeer har sau biyu, da sauri ta kira shi ta kishingida akan gado, har ta katse bai ɗauka ba, tana ƙoƙarin ajiye wayar ya kira, har ta kai hannu zata ɗauka sai ita ma taƙi ɗauka tana kallon kiran ya katse sai ta kira tana murmushi tana hasaso fuskar Baqeer, ga mamakinta ƙin ɗauka yayi har ta katse sannan ya kira. Cike da shagwaɓa ta ɗaga kiran tana ɗan gyara kwanciyarta, yace "Ƴar Ummi ana can ana zuba shagwaɓa ne?" Sakalce mishi tayi tace "Allah ni ina ji gida zan koma gaba ɗaya an takura mun a gidan komai nayi ba daidai ba."
Yayi ɗan shiru kafin yace "Hmmm kamar me da me kenan?"
Tace "Allah ni kawai komai ma, ciki har da girki." Ajiyar zuciya yayi yace "Ba dai wata a haka take son tayi aure bata iya girki ba? Kice akwai case a gaba."
"Case? Kamar na me? Nifa Mummy tace ba sai na koyi komai ba ko aure nayi da mai aiki na zata kai ni Allah ni bana son takurar da ake yi mini a gidan nan."
Cike da mamakin jin abinda take cewa yace "Ita Mummy haka aka koya mata? Ko haka aka yi mata?" Tambayar tazo mata a ba zata hakan yasa tace "Name?" Yana riƙe da wayar yace "Na komai, ko ita bata iya komai ba?"
Kai ta girgiza kamar tana gabanshi tace "Ta iya amma nice bata so na wahala."
Ya jinjina kai yana cewa "In kika auri talaka fa irin su mu?" Yayi maganar cike da bugar ciki, ido ta lumshe tana hango fuskarshi cikin ƙwayar idanunta tace "Da mai aiki na ai."
Ya ɗan murmusa yace "To kuma irin mu ina muka ga inda zamu saka mai aiki? Sai dai ke bana ji zaki auri talaka watakila shi yasa ba kya wannan tunanin." Da sauri tace "Allah a'a!"
Shafar sumar kanshi ta baya yayi yace "A'a me?" Ta gyara kwanciya tace "Ban ce komai ba."
"A dai faranta ran Ummi kinga dai shekaru kuka ɗiba ba kwa tare sannan abinda take nuna miki gata take yi miki don ko ni bazan yarda matata ta zauna bata komai ba," yayi maganar cike da son jin me zata ce, sai dai kawai ji yayi tace "Umm!" Jikinshi ne yayi sanyi da Umm ɗin da tace amma ya daure yace "Yaushe zaki dawo? Dada nata tambayarki da alama missing ɗinki take yi."
"Ita kaɗai?" Tayi tambayar itama tana son jin me zai ce, da yake ya dawo gida yana zane sai ya tura kujerarshi baya yace "Kila?" Zee tace "Kila kenan babu tabbas?" Kallon sketch na material ɗinta da yake yi yayi yace "Ko a tambayar miki?" Tace "In dai sai an tambaya na yafe kaga kenan ba ayi."
"A'a ai sai anji ta baki ake fahimta," yayi maganar cike da zolaya, Zee ta ɗan motsa baki kafin tace "A'a wannan daga zuciya ya kamata ya fito." Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta cilla ta gefe tare da binta da harara tace "Allah sai na fanshe, ni kam anya Ya Baqeer na so na?" Ta tambayi kanta idanuwanta na kan wayar kamar wayar take tambaya, sai dai kalaman Baqeer na sake dawo mata, to ita ya zata yi? Gaskiya ko zata koya gwara ta koya a gidan su ba dai nan ba bata son abinda zata yi ace ba tayi daidai ba.
******
Inna ce ta shigo ɗakin rai a ɓace ta yaye bargon da take lulluɓe dashi cikin takaici tace "Baza ki fito kici abinci ba?" Maida bargon tayi saman kanta tace "Bana ci."
Takaici ne ya sake rufe Inna tace "Wai na ɗauka zaki amshi laifinki ki nemi yafiya ashe shirme zaki aikata?" Kamar dama jira take ta tashi ta zauna a bakin gadon tana magana mai kamar ta kuka tana cewa "Inna wai menene laifina? Akwai aure tsakanin mu da Kabir sannan babu wani abu daya haramta, abu na biyu magana ta bayyana kowa ya sani to a barni na aureshi mana."
"Anƙi a barki ki aureshin, nace anƙi a barki, ja'irar yarinya, yanzu duk kyawawan halin ki dama akwai wani halayenki da kike ɓoyewa wai har kece zaki yiwa kanki sharrin ciki? Cikin ma na shege? Ke kinsan me cikin shege yake nufi?" Nabila kamta ta sunkuyar tace "Nifa saboda a haƙura a bar mu muyi aure na........"
Inna ce ta katseta da cewa "Kina ƙarasa maganar nan zan tsinkeki da mari, aure a gidan uban wa? To ki sani Halima tace shi ko a jikinshi sannan wacce ake so ya aura ma yaje ya ganta, sai naga abinda zaki yi, sokuwa wato ke ko tausayin mahaifiyarki ba kya yi." Inna tana kaiwa nan tayi hanyar waje, Nabila jan bargo ta sake yi zuciyarta na tafasa, in dai haka ne to lallai ba wanda zai zauna lafiya in har ita ba'a barta ta zauna lafiya ba, haushin kanta ne ya kamata tunowa da tayi bata san saurayin da Zee take so ba tabbas da ta kira Daddy ta sanar mishi don ta tabbatar bai san da wanda take so ba.
*****
Ɗaki Mummy ta shiga ta ɗan fara kaiwa da komowa, hankalinta sam baya jikinta don ta kasa nutsuwa gashi dai Senate ya dawo gida amma fa yanda suke yi kamar da ya daina, hira wannan ba sosai yake yi da ita ba, to yanzu matsalarta yanda zata jawo Zainab daga Ɗambatta wanda ta rasa ta wani hali zata aikata hakan, baya tayi saboda jirin da taji ya ɗebeta, a hankali ta janyo wayarta tana sauke numfashi ta kira Zee, sai dai har tayi ringing ta gaji bata ɗauka ba, kiran Kabir tayi akan yazo. Ba daɗewa sai gashi don dama yana gida, duk da shima bai gama sakewa da abinda ya faru ba amma shi yayi mata uzuri ya tabbatar fyaɗe aka yiwa Mummy kuma ba da saninta ta aikata hakan ba yana ma gani Inna ce hala ta tursasata. Yana shiga ya ganta a kwance a ƙasa hankali a tashe yace "Menene Mummy?" Kai ta girgiza tana lumshe ido tace "Kabir ƙirjina keyi mini wani irin nauyi nama kira Zainab bata ɗauka ba." Hankalinshi a tashe yace "Bari na kira Dr, ta girgiza kai tace "Kar ka damu kawai dai gani nake in na ganku zan samu nutsuwa ne, In Sha Allahu ba komai. Ran Kabir a ɓace ya kira Zainab, sai dai lokacin ita bata ma ɗaki tana falo a zaune, cike da tausayin halin da Mummy ke ciki yake yi mata sannu.