← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 168

Sashe 110

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Fitowa Daddy yayi yana ƙwala ƙiran Zainab lokacin ta fito daga ɗakin Kabir kenan, sai da taji gabanta ya faɗi saboda irin ƙiran da yake yi mata. A parlourn shi ta tarar dashi a tsaye ya goya hannayenshi a baya sai kaiwa da kawowa yake yi, tashin hanakalin da ya samu kanshi a ciki yasa ya kasa zama a wuri ɗaya, idan ba gani yayi ba ya samu mafitar wannan badaƙalar da ƴaƴanshi ke neman sakashi a ciki ba hankalinshi ba kwanciya zai yi ba.
Zainab na zuwa tace "Gani Daddy," bayan ta zauna akan kujera tana kallon yadda Daddyn ya kasa zama a wuri ɗaya sai fama zagaye yake yi a cikin parlourn kamar mai yin parade.
Kallonta yayi ya nunata da yatsa yace "Ina fata kun gama daidaitawa da Junaid don mun gama magana da mahaifin shi zasu zo mu tsayar da ranar aurenku nan ba da jimawa ba." Shiru tayi ma ta kasa magana jin yadda maganar tazo mata a bazata, ana cikin wancan case ɗin me ya kawo wannan? "Tashi kije," taji muryar Daddy kamar daga nesa yana bata umarni. Sai sannan ta dawo cikin hayyacinta tace "Wani irin aure kuma Daddy bayan na faɗa maka bana son shi, ni dai gaskiya bazan aureshi ba." A fusace yace "Na dai faɗa miki aurar dake zan yi kuma banga uban da ya isa ya hanani ba, ruwanki ne ki koyawa kanki son shi ruwanki ne ki ƙi aure ne dai ke da Junaid babu fashi." Ya fice daga gidan a fusace ranshi yana tafasa. Tashi tayi a guje ta shige ɗakinta tana kuka. Mummy da fitowarta kenan daga nata ɗakin taga wucewar Zainab ɗakinta tana kuka ta bita ɗakin hankali a tashe tana fatan ba wata matsalar bace ta sake kunnowa kuma. Tana shiga ta ganta ta kifa kai akan gado sai gurshaƙen kuka take yi, tambayarta tayi abinda aka yi mata take irin wannan kukan.
Ɗagowa tayi ta kalli Mummy fuskar nan tayi jawur idanunta sun yi kozai-kozai alamun taci kuka ya isheta tace "Wai Daddy ne yace sun gama magana da Baban Junaid zasu saka ranar aurenmu dashi bayan tun da farko na faɗa mishi ni bana son shi amma yaƙi yarda kuma ma Mummy ni ina da wanda nake so me yasa ba za'a barni na aureshi ba."
Zama Mummy tayi a bakin gadon tasa hannu tana shafawa Zainab baya kamar mai lallashin wata ƙaramar yarinya tace "To me yasa baki faɗa mishi ba?" Sai cewa tayi "Bayan bai bari nayi magana ba ya fice yana masifa ni kuma wallahi babu mai yi min auren dole haka kurum." Shiru tayi na wasu ƴan daƙiƙu kafin tace "Ai kin san ko kowa bai tsaya miki ba ni zan tsaya miki, ba Daddy ba koma waye babu mai yi miki auren dole idan har ina raye wanda kike so shi zaki aura, haba wane irin auren dole sai kace muna zamanin iyaye da kakanni."
Kanta ta kwantar akan cinyar Mummy tana jin wata irin nutsuwa na ratsata don tasan ko kowa bai goya mata baya ba Mummy na tare da ita. A shgwaɓe tace "Mummy bai fa ce yana so na ba." Tsaki Mummyn tayi tace "Ke ba sai ki faɗa mishi ba tunda dai ba haramun bane ba kuma ace dole sai namiji ne zai fara furtawa mace soyayya ba, babu batun wani ɓoye-ɓoye yadda zamanin nan ya canja don kin faɗa mishi kina son shi ba laifi bane." Haka Mummy tayi ta ƙarfafarta tana nuna mata ta kwantar da hankalinta don ba zata taɓa bari ayi mata aure da mijin da bata so ba abinda yasa ta samu ƴar nutsuwa ke ab don tasan tunda Mummy tace haka ita tasan yadda zata yi tasa Daddy ya haƙura da batun aura mata Junaid.
Tana kwance tana saƙa da warwara akan shawarar da Mummy ta bata na ta fara furtawa Baqeer cewa tana son shi sai dai kuma zuciyarta ta kasa nutsuwa da yin hakan tana ganin kamar bai dace ba a matsayinta na ɗiya mace da aka sani da kunya da kawaici ta fara bayyana mishi asirin zuciyarta, to sa ma ace tayi hakan idan shi baya jin irin abinda take ji akan shi ba fa kenan ta zubar da ƙimarta ta ɗiya mace ta fallasa mishi asirin zuciyarta yazo yace baya sonta bata san a wane hali zuciyarta zata kasance ba, tana jin watakila ma bugawa zata yi don bata ga ta inda zata iya rayuwar da babu Baqeer a cikinta ba. Mummy ce ta shigo ɗakinta tana faɗa mata Junaid na guest sitting room yana jiranta. A fusace ta tashi zaune tace "Mummy me yazo yi a wurina kuma? Please Mummy kice mishi ya tafi wallahi na tsane shi bana son ganinshi, shine bayan duk faɗa mishi da nayi tayi akan ni bazan aureshi ba a matsayin aboki kawai na ɗauke shi yaje ya turo Babanshi zasu sa ayi mini auren dole to wallahi bazan aureshi ba, idan shi maye ne sai dai ya cinye kanshi da kanshi amma ni nafi ƙarfin nacin shi wallahi."
Hannayenta Mummy ta riƙo tace "Duk wannan faɗan da kike yi ai shi ya kamata kije ki yiwa ba wai ki zauna anan kina yi ba alhalin bai ma san kin yi ba, zuwa zaki yi kija mishi kunne kice ya fita sabgarki don ba aurenshi zaki yi ba tunda dai kin tabbatar ba kya son shi to gara ya kama gabanshi tun wuri yasan nayi don nasan harda yawan ganinshi yana zuwa wurinki da Daddy ke yi yasa ya bijiro da maganar aurenki da shi kamar wacce muke neman kai dake, ni an faɗa mishi idan zaki tabbata babu aure zan damu ne, a yadda nake jin ƙaunarki a cikin zuciyata ban ƙi muyi ta zaman mu a cikin gidan nan ba don bana son tuna akwai wata rana da dole zamu rabu kiyi aure."
Tashi tayi tana jinjina kai, tabbas harda fuskar data sakarwa Junaid yasa kowa ke tunanin soyayya suke yi bayan tasha faɗa cewa ita ba zata aureahi ba saboda a aboki kawau take kallonshi ba wai masoyi ba. Haja ta fita fuska kozai-kozai ko ruwa bata sa ta wanketa ba Tana shiga sitting room ɗin babu wata gaisuwa babu komai kawai Zainab ta rufe shi da masifa tace "ai dai kasan ba sonka nake yi abotar ma kuma na fasa don haka tun wuri gara kaje ka samu su Daddy ka faɗa musu ba zaka aureni ba don wallahi idan ka yarda ka aureni ka aurar wa kanka tashin hankali, haba bana son naci wallahi. Ka dai san nasha faɗa maka ni bazan aureka ba amma ka nace akan magana ɗaya, to tun wuri kaje ka faɗa musu ka janye don ni dai bazan aure ka ba, to na auri sa'ana nace na auri wa ma?"

Idan ka kalli Junaid a wannan lokacin sai ya baka tausayi gaba ɗaya ɗokin da yazo dashi ya gama gabanshi, ashe bada yardar Zeey iyayensu suka yanke musu wannan hukuncin ba. Ɗan zamowa yayi daga kan kujerar da yake zauna yace "haba Zainab don Allah kada ki bari son da nake yi miki ya tafi a haka, kema kin san ina son ki tun kafin iyayenmu suyi tunanin haɗamu, please ki bani dama na nuna miki irin son da nake yi miki, bana buƙatar sai kin soni son da nake yi miki kaɗai ya ishemu ba sai kin so ni ba har ƙarshen rayuwarmu," tsaki tayi ta mishi wani irin wulaƙantaccen kallo tace "Ai ni zama da wanda bana so ne ma ba zan iya ba kwata-kwata, shawara kuma ta rage ga mai shiga rijiya don ni dai na gama magana," daga haka ta juya tayi shigewarta cikin gida ta barshi anan.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce*
Da
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
*NA*

*AYUSHER MUHD*
        *DA
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA BAKWAI*
Chapter 110 · 0% Book details