← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 168

Sashe 137

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Baqeer kuwa yana fitowa suka yi kiciɓis da Kabiru gabanshi ne yayi wani mugun faduwa, tunani yake ba dai shine wanda ya buge a mota ba? Don in bai manta ba ya bincika kuma ance mishi ƙafarshi ta samu matsala, kar dai shine ya zo kawo ƙara? Shi kuwa Baqeer kallonshi kawai yake yana tunanin Kabiru ne? Salim ne yace “Baqeer are you okay?” Kai ya ɗaga mishi alamar eh, wanda hakan yasa Kabir yaji sunan Baqeer gashi dama yasan yaron Badaru ya bige, innalillahi, yanda yaga Baqeer na mishi wani kallo ne yasa ya tabbatar abinda ya kawosu kenan? Bakinshi na rawa yace “Ba dai Dady kuka zo kawo wa ƙara ba?” Kallonshi Baqeer yayi cike da mamakin kalamanshi sai kuma yayi tunani kila ko yasan yana son Zainab ne hakan yasa yace “Eh, laifi ne?”
Kabiru ya matso daf da Baqeer yace “Ka dai sani Daddy ba zai taɓa bani laifi ba sannan kai tsautsayi ne baka sani ba? Nasan nayi laifi amma kaima sanda kake tafiya me yasa baka duba inda kake takawa? Da sai ka fara samuna na baka hakuri in kuma kuɗi kazo nema na baka amma ba wai ka kawo karata ba,” yanda yake magana kaɗai zaka san a ruɗe yake, kalaman da yake yi ba sai Baqeer yayi tantama ba don abinda yake son cewa a bayyane yake, murmushi Baqeer yayi wanda yafi kuka ciwo sannan ya sake kallon motarshi, tabbas motar can ce ya gani sanda ya bugu, idanun Baqeer ne suka canza yanayi ya ciji leɓenshi na ƙasa yace “Sanda ka kaɗeni me yasa baka tsaya kaga halin da nake ciki ba?” Kabir ya haɗiyi yawun bakinshi yace “Ban san mutum bane sai daga baya, amma…” hannu kawai Baqeer ya ɗaga mishi ya kalli Salim yace “Mu tafi,” yayi maganar cike da raunin murya. Tafiya suke kawai zuciyar Baqeer na sake tafasa, sam ji yake kamar kanshi zai faɗo saboda tashin hankalin daya shiga, Salim kanshi ya kasa magana saboda mamakin abubuwan dake faruwa, lallai wannan soyayyar ta Zee da Baqeer kyanta shine kowa bai san kowa ba ayi a rabu a haka amma ina zasu kai wannan ɓacin ran da suka shiga da tashin hankali?

******
Zee kuwa Mummy ce ta rungume ta kawai kuka take yi tana cewa “Mummy yanzu Daddy yayi mini adalci? Yayi wa Baqeer adalci?” Shafa bayanta tayi tace “Kiyi hakuri Zee ni kaina bansan meke damun senate ba, sai dai ya kamata muyi mishi uzuri kin dai san yadda yake ji dake.” Kallon Mummy tayi Mummyn tace “Yadda yake ji dake ne yasa yake haka, kiyi haƙuri zan sake yi mishi magana sannan nasan zai fahimceki in kika nuna son da kike yi mishi.”
Kallon Mummy tayi tace “Mummy kiyi mishi magana don Allah bazan auri kowa ba sai shi, in kuma ba haka ba Allah ya shirya zama dani har tsufana.” Kai ta jinjina tana riƙe da ita tace “Na sani, anjima kije ki ƙara sanar dashi ra’ayinki ni ina tare dake ba kuma zan yarda ayi miki auren dole ba, menene a ciki don bashi da ƙafa? Sannan shi faɗan da shikenan bazai wuce ba ko me?”
Cike da gamsuwa da maganar Mummy tace “Mummy nagode da kika fahimceni.” Hannu tasa ta share mata hawayenta tace “In ban fahimceki ba wa zai fahimceki?”

******
Badaru cike da ɓacin rai ya sauke wayar da aka yi mishi wai yazo ya ɗauki nakasashen ɗan shi. Me ya kai Baqeer gidan Alhaji Sulaiman? Abu ɗaya ne yazo mishi tabbas Kabir ne ya buge Baqeer kila shine yaje ya nemi hakkinshi, ai kuwa in haka ne dole yaje yaci zarafin Alhaji Salaiman tunda dai saboda shi komai na rayuwarshi ya ruguje sannan yana neman inda zai sauke ɓacin ran da yake ƙunsa kwanan nan. Da wannan tunani ya baza rigarshi ya fito daga ɗakin Jamila.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce*
*Da Ayusher Muhd*

*BAQEER*
*NA*

*AYUSHER MUHD*
*DA
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA HUƊU*

{84}
Yana tafe fakam-fakam yana saƙar wasiƙar jaki yana ayyana abinda zai yi da kuɗaɗen da zai karɓa a wurin Suleiman Ƙaraye na fansar abinda ɗanshi yayi wa Baqeer. Har ya gama tsara yadda zai kasafta kuɗinshi don wallahi sai an biyashi asarar da aka janyo mishi tunda dai ya tabbata ɗan nashi ne ya kaɗe Baqeer da mota kaɗewar da itace sanadin halin daya tsinci kanshi a ciki yanzu. Yana zuwa gaban gate ɗin gidan ya hau bubbugawa da ƙarfi kamar zai ɓalla ƙofar gate ɗin. A fusace maigadi ya taso yana cewa "Kai da Allah ana zuwa, haba mutane sam babu hankali kazo gidan mutane kana buga ƙofa kamar qanda yazo yaƙi." Yana buɗe ƙaramar ƙofar suka haɗa ido da Badaru dake tsaye sai faman hura hanci yake yi. Yana ganin shine ya tare ƙofar ya hanashi wucewa. A wulaƙance ya kalleshi yace "lafiya?" Don yasan zuwan nan na Badaru ba alheri ne ya kawo shi ba tunda kuwa kowa yasan ƴar tsamar dake tsakaninsu da maigidan. Harararshi Badaru yayi yace "Kauce ka bani wuri na wuce, ni ba da kai zan yi ba da ubangidan ka zanyi don shine tsaran yina ba kai ba." Ƙin matsawa yayi ya bashi wurin kamar yadda ya buƙata sai ma cewa yayi "Tsaya dai anan naje na faɗa mishi kazo amma bazan baru ka shiga ciki ba alhalin wancan zuwan da kayi ka tayar da tarzoma ƙiris baka yi mini sanadin aikina ba."

Jayayya ce ta ɓarke a tsakaninsu Badaru ya dage sai dai a barshi ya shiga shi kuma maigadi yace ba zai shiga ba sai dai ya jira yaje ya sanar da zuwanshi idan ance ya shigo sannan zai buɗe mishi ƙofa ya shiga. Hayaniyarsu ce ta fito da Alhaji Suleiman daga cikin gida, tun kafin ya ƙaraso wurin ya shaida muryar Badaru. Yana zuwa yace "lafiya? Me kazo yi a gidana? Idan kuma nakasashen ɗanka kazo ɗauka tuni ya tafi". Wannan kalami na Suleiman Ƙaraye sai ya ƙara tunzura Badaru, a masife yace "Waya nakasa min ɗan nawa idan ba ɗanka ba? Kuma ni zuwa nayi a biyani fansar nakasa ɗana da kuka yi tunda dai ya tabbata ɗanka ne ya kaɗeshi don nasan babu abinda zai kawo Baqeer gidanka sai don a biyashi diyyar ƙafarshi da ɗanka ya nakasta mishi. Waya sani ma ko da gayya kuka nakasta shi don kunga ya taso da basirar iya zane yana daf da tafiya gasar da zata ɗaukaka sunanshi a duniya kowa ya san shi."
A sakarce Suleiman Ƙaraye ya kalleshi yace "Har wani ɗa gareka da za'a yiwa baƙin ciki, tun wuri gara kaje ka nemi wanda ya nakasta ɗanka amma ba Kabir ba. Kada kaga kwanaki kazo har gida kayi mini hauka na rabu da kai wallahi idan na sake ganinka a ƙofar gidana sai na ɗaure haka har igiya tayi rara kuma ka faɗawa gurgun ɗanka babu shi babu ƴata ko yana da lafiya shi bai isa na bashi auren ƴata ba bare yana gurgu nakasashe." Mallam Bala rufe mini gate ɗin gidana sannan daga yau idan ka kuma bari mahaukacin nan yazo mini gida a bakin aikinka." Ya shige cikin gida yana bambamin faɗa kamar shi in banda raini ta yaya za ace wai ɗan Badaru ne ke son ƴarshi. Yana shiga Mummy ta taso tace "Senate me ya faru? Tun daga waje nake jiyo faɗanka." Zama yayi akan kujera, tsaki yayi yace"Wancan wawan mutumin mana wai yazo karɓar diyyar nakasta ɗanshi da Kabir yayi."
Zama tayi a kusa dasi tace "Badaru wai? Har yanzu bai bar batun Kabir ne ya kaɗe ɗanshi ba duk da an faɗa mishi a ranar da abun ya faru ma Kabir bai fita ba? Wai shin meke damun shi ne?"
Tsaki yayi yace"Waya san mishi mana, koda yake duk laifin Zainab ne data rasa wanda zata ce tana so sai ɗan shi in banda haka shi ya isa yazo ƙofar gidana yace zai  kawo mini zancen banza." Dafa kafaɗarshi tayi tana shafawa a hankali zuwa bayanshi tace "Ka daina ganin laifin auta ni na tabbata yaron nan yaudararta yayi in ba haka ba ina shi ina Zainab ka kuma fa san mutane ba wani tsoron Allah suka cika yi ba yanzu haka ba haka nan ya barta ba shi yasa gaba ɗaya ta susuce akan shi don in dai ba aikin asiri ba ban ga ta yadda za'a yi auta ta so gurgu ba gurgun ma ɗan gidan Badaru."

"Ni dai na faɗa ko mutuwa zata yi bazan aura mata ɗan Badaru ba, ah ti gara ma ki faɗa nata idan zata haƙura su daidata da Junaid tun wuri daya fiye mata." Tashi yayi ya bar parlourn ranshi yana ƙara ɓaci wai kamar shi ace gurgu ne masoyin ƴarshi gurgun ma ɗan Badaru, Badaru dai da tun asali babu wata jituwa a tsakaninsu.
Chapter 137 · 0% Book details