← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 168

Sashe 68

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Hakan yayi" Zeey tace "Amma me zai hana ka saka mishi sauran ta account ai kamar zai fi ko?" Ta kalli Baqeer don son jin me zai ce. Ɗaga mata kai yayi alamun amsawa don haka Sani ya fito da kuɗi cash dubu ɗari daga aljihun shi ya miƙa mishi. Karɓa yayi ya ƙirga yaga sun cika cif, account number ya bashi a take a wurin ya tura mishi sauran kuɗin sai gashi da dubu ɗari biyu cif nashi na kanshi. Wani irin daɗi Baqeer yaji ya mamaye zuciyarshi, a tunaninshi tunda larurar nan ta sameshi ya tashi a aiki kenan ashe dai yana da sauran amfanin da zai yi da rayuwarshi. Sallamar su Sani tela yayi ya tashi ya tafi. Yana fita Baqeer ya miƙawa Zeey kuɗaɗen gaba ɗaya. Tsayawa kawai tayi tana kallonshi, "Amsa" yace mata shima idanunshi a cikin nata.
"Me zan yi dasu ni da zaka bani, ba kuɗinka bane?" tace tana turo baki gaba abinda ya kula kamar ya zame mata jiki tsabar shagwaɓa. Ganin ba zata karɓa ba ya ƙirga dubu ashirin ya miƙa mata. Noƙe kafaɗa tayi taƙi karɓa sai ma tashi da tayi ta shige falo gun Dada ta bar shi anan wurin. Da kallo ya bita kafin kuma ya tattare sauran sketches ɗin shi ya gara keken nashi ya bita cikin falan. Tana kishingide akan kujerar ƙarfen Dada ita kuma Dada tana zaune akan tabarma suna hira. Gefen kujerar ya ƙarasa ya miƙa mata kuɗin, sai ma kawar da kai tayi kamar bata ganshi ba.

Kallon Dada yayi yace mata "Dada yi magana."?Baki Dada tasa tace "Ke kuwa Zainabu ki karɓa mana, ai ba'a mayar da hannun kyauta baya." Tashi tayi zaune tace "Allah Dada ba zan karɓa ba, ya daga fara abu kawai zai ɗauki kuɗi ya bani ya bari a gaba na karɓa amma dai ba yanzu ba." Bai ƙara jan maganar ba sai ma ya miƙawa Dada kuɗin hannunshi. Karɓa tayi tace "Na miye wannan ɗin?"
Sai da ya kawar da fuska sannan yace "Naki ne."
"To daga farawa kai kuma Baqeeru sai ka cire iyayen kuɗi kamar wannan ka bani, da dai ka rage." Ƙin amsa yayi sai ma ya cire dubu goma a sauran kuɗin ya saka aljihun shi ya miƙawa Zainab sauran dubu saba'in ɗin yace "Please ki kaiwa Umma kice ta ɗauki 30k sauran ta bawa Hadiza da Maryam" karɓa tayi tasa a jakarta tana godiya kamar ita aka bawa. Dada ce tace "to kai kuma haka ake yi duk kabi ka rabar da kuɗaɗen naka?"
"Saboda ku nake neman ai Dada" abinda yace kenan kawai yace ya gungura kekenshi zuwa ɗakin shi.

*****

Bello da Asiya kuwa saboda tafiyar shi data matso kusa yasa aka dawo da bikinsu baya don a samu ayi bikin kafin lokacin tafiyar tashi yayi, shi zai fara tafiya daga baya sai Asiya ta bishi don aƙalla zai yi shekara uku zuwa huɗu acan ƙasar da aka turashi. Tsare-tsaren biki kawai suke yi Asiya ana ta iyayi da gwalli ita a dole ta zama big babe tunda zata fita ta bar ƙasar ƙawayenta na ƙara zugata suna fasa mata kai. Gida ma da Bello zai kama haya cewa tayi bata son mai tsakar gida sai dai ya nema mata gida me gate gashi duk inda suka je neman irin gidan da take so sai suji yayi tsada don kuɗinsu daga dubu ɗari takwas zuwa miliyan ɗaya ne har da inda aka ce musu miliyan ɗaya da rabi. Da ƙyar suka samu wani three bedroom flat a tarauni, gidan sama da ƙasa ne na saman suka samu. Sai da Bello ya jinjina yawan kuɗin gidan amma da ya tuna ba wani daɗewa zasu yi a ciki ba su tattara su bar ƙasar sai yaji ba wani abun damuwa bane don haka ya kama yana murna burinshi ya kusa cika. Events kala-kala ta tsara da zasu yi shi kuma yana biye mata idan Habi tayi magana tace ya kamata ta rage ƙaryar data ɗaukarwa ranta ta tuna ita ba ƴar kowa bace iyayenta basu ajiye ba basu bawa wani ajiya ba sai ta hayayyaƙo mata da masifa tace tana yi mata baƙin ciki don taga Allah ya ɗaga darajarta ya kusa rabata da ƙangin talauci.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*

*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
DA
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA BIYU*

{42}

  Dada ce ta fita jin sallama daga waje, Zeey a hankali ta kalleshi sai kuma ta canza yanayin fuskarta ganin kallan da yake mata, takardun ta kwasa sannan ta miƙe ta koma jikin ƙofa tana sake kallansu, yana daga zaune yake binta da kallo, gyaran murya yai yana ɗan kauda kai. Ta kalleshi tace "Ya Baqeer karma ka fara."
"Me?" Ya tambaya yana kallanta, tace "Wai karma ka canza magana kaga dai magana ɗaya kake yi."
Bai san sanda ya ɗan murmusa kaɗan ba, kanta ta kwantar jikin bango tana kallanshi, ba shakka itadai yanzu kam ta tabbatar san Baqeer nada mahimmanci arayuwarta wanda murmushinshi kaɗai nutsuwa take saka mata. Yanda ta kalleshi ne yasa yace "Kallan na menene?"
Kai ta girgiza alamar a'a tace "Hakuri na nake jira ka bani?"
"Name kenan?"
Ajiyar zuciya tai idanunta na kanshi tace "1?"
"Zero ɗin fa ina aka kaishi?"
Tasan halinshi sarai kwanan nan, yanzu har kalamansa sun daina bata haushi, kallan zanen ɗinkuna dake hannunta take tabbas Baqeer Allah ya bashi basirar zane taya mutumin da bai taɓa ɗin ki ba zai zane ɗin kuna haka?
Kallansa tai shima daidai nan ya ɗago yana kallanta, ya zaiyi da abinda ke ransa? Wai yau shine ya wuni yana zanen kayan da Zeey zata ɗin ka tasa, haka kawai in ya ajiye sai yaji kwakwalwarshi na auno mai ita cikin wata shigar wasu kayan, idea na sake saukar mai wanda hakan zaisa ya zauna ya sake yin zanen, sannan abinda ke ɗaure mai kai yanda zanen kayanta ke sashi farinciki da nutsuwa a cikin ranshi. Yasa a ranshi ko keken electric ɗin bai fara amfani dashi ba zai fara yanka dan yanzu ji yake yana san ɗin ka mata abinda zata sa.
"Zaka min sketch na maza?"
Kallanta yai da mamaki sai kuma ya tuno Junaid badai so take tace ya zana mata saurayinta ba? Nan danan fuskarsa ta canza, ya kauda kai tace "Hmmm a tsayi bai fika ba, sannan a jiki ma haka, ashekaru ma ina ga bai fika ba."
Fuskarshi ce ta murtuke sosai dan yanzu kam ya tabbatar da Junaid take duk da basu gwada tsayi ba amma yana tunanin kansu ɗaya sannan jiki ma da kadan Junaid ya fishi kenan ko kaya ne zasu iya sawa, mamaki ne ua kama Zee ganin yanda ya canza fuska lokaci ɗaya. Tace "Me kuma nai? Ko bazaka dinka ba?"
"Eh!" Kalmar dayaji ta fito daga bakinshi kenan shi kanshi bai sani ba "Meyasa?"
Nan ya fara tambayar kansa dan shi kanshi baisan amsar da zai bata ba, yana ƙoƙarin yin magana Dada ta dawo tana cewa "Baqeeru almajirincan ne Tanimu wai gaisheka yazo yi."
Ja mishi ƙofa sukai suka bashi guri dan ya hau keken guragun, haka ya hau ya turo keken zuwa jikin ƙofa yana buɗe wa suka ƙara kallan juna, wani yanayi ne ke ratsa zuciyar ta da ita kanta batasan sanda ta canza yanayin kallan da take mai ba, wani abu ne ya tsayamai wanda yai saurin kauda kai yana cewa "Tanimu?"
Da sauri yaran ya taso da bai wuce shekara 16 ba yana gaida Baqeer, tana daga ciki tana kallan yanda suke magana fuskar Baqeer a sake, hakan yasa ta kasa ɗauke idanunta daga kanshi. Mikewa tai ta ɗau dinkin ta sannan tawa Dada sallama.
Yana kallan sanda ta fita ganin taki mai magana yasa ya rasa ta yanda zai mata magana harta kai bakin ƙofa idanshi na kanta, takardun hannunta ta ɗaga mai sama kaɗan, kai ya ɗaga mata alamar to tana murmushi tace “Zan kawoshi.” Nan ma kai ya ɗaga mata, ta kalli Taminu sannan tace “Bazan ƙira waya ba.”
Yanzun ma kai ya ɗaga mata, fuska ta canza sannan ta fita waje, mota ga shiga tasa hannu saitin kirjinta tana fitar da wani irin numfashi sama-sama nutsuwa ce take saukar mata ta sake kallan sketch ɗin tana cewa “Duk ni zan fara ɗin kunan nan.”
Baqeer kuwa samun kanshi yai kamar wanda bashi da damuwar komai, yana mamakin yanda ta shigo rayuwarshi har ta cire duk wani duhu dake baibaye dashi. Tanimu ya daɗe a gidan dan har gyaran ɗakin Baqeer, Dada tace ya jira yaci abinci yace a’a zaije kasuwa ne yin dako sannan ya tafi.
Chapter 68 · 0% Book details