← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 168

Sashe 136

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zee sam ta kasa zama sai zarya take yi zuciyarta ta kasa nutsuwa, Mummy ce ta riƙe hannayenta tace "Kar ki damu auta komai zai tafi daidai." A hankali ta jinjina kai alamar eh sannan tace "Matsalar nakasa da nace miki yana dashi ne bana so Daddy ya wulakantashi saboda wannan, nasan halinshi," ta ƙarasa maganar tana neman shiga falon, da sauri Mummy ta sake riƙota tace "Kar ki shiga shi kanshi Baqeer ɗin ba daɗi zai ji ba in ya ganki." Da mamaki ta kalli Mummy, ya aka yi tasan sunanshi? Don a iya saninta bata taɓa sanar da ita wanene wanda take so ba, baki ta buɗe zata yi magana suka jiyo muryar Dady daga falo yana cewa "Gurgu? Kai wannan wasa ne bana son shirmen banza da wofi, ni? Kamar ni gurgu mara ƙafa zai zo yace yana son ƴata? Uban waye ya tsaya maka da har ka rainani zaka tako kazo cikin gidana?"
Baqeer kalaman Daddy sun kai shi maƙura sai dai wahalar da Zainab tayi dashi ne yake tunowa, hakan yasa ya daure don kalaman Alhaji Sulaiman ba ƙaramin ɓata mishi rai suka yi ba, gurgu ba mutum bane kenan ko me?
Daddy yana hura hanci yace "Kai kaga mun yi maka kama da inda zaka zo da kekenka? Dalla fita ka bar min gida kafin nasa securities su fitar min da kai."
Zee ce ta shigo ciki da sauri, daidai nan Baqeer ya saki wani murmushi yace "Ashe girma bai sa ka canza halayenka ba." Waigowa yayi ya zabgawa Baqeer wani mugun kallo yace "Me kace?" Kai kawai ya girgiza yana ɗagowa suka haɗa ido da Zainab, murmushin takaici da tausayawa kansu yayi, lallai daya sani da ya riƙe son da yake yi mata a zuciyarshi tabbas da yasan ƴarshi ce da ya gwammace ya nuna baya sonta a ƙalla zata auri wanda yake sonta wanda zai kula da ita kamar Junaid. Shi da budurwarshi ta gujeshi ma da wannan larurar ta sameshi ina ga Alhaji Sulaiman?
"Me kace nace? Kai dalla ja keken guragunka ka bar min gida kaje can bakin titi nan ne ya dace da kai, ni ko mai gadin gidana gurgu bai kai yayi ba bare auren tilon ƴata," Yana kumfar baki yake maganar bai jira komai ba ya cigaba "In dai har Zainab zata kawoka a matsayin wanda take so to tabbas asiri kayi mata, wawan banza wawan wofi kai dai kayi asara wallahi....." Zee ce tace "Ni nake sonshi Daddy," tayi maganar idanuwanta na kan Baqeer, a fusace ya zabga mata wani kallo, fuskar nan tashi duk ta sake canzawa yana ƙara kumburota yace "Me kika ce?" Ta maida kallonta kan Daddy tace "Ni nace ina sonshi, laifi ne?"
Baqeer ne ya katseta da cewa "Koma ciki." Kallonshi tayi kamar zata yi kuka, kai ya jinjina mata alamar babu komai, hannu tasa ta shafi fuskarta sannan ta juya, mamaki ya kama Daddy ganin duk gardama irinta Zee gashi tana abu babu musu, ai kamar an fusatashi yace "Waye ubanka? Sannan mema abokinka yace sunanka?" Baqeer ya haɗiyi wani yawu yace "Baqeer sunana."
Yanayin Daddy ne ya canza zuwa mamaki yace "Baqeer?" Nan da nan ya tuno zuwan Badaru gidanshi akan ɗan shi yasa yaronshi hatsari, abinda ba zai iya tunawa ba yace ƙafar shi ta saku matsala ko bai faɗa ba? Don shi a trayuwarshi ma bai taɓa jin sunan Baqeer ba sai da Badaru ya sawa ɗan shi, bai mantawa sanda aka sa sunan har sai da yace menene ma'anar Baqeer? Kai ya girgiza don tabbas yasan ba dai ɗan Badaru ba.
Cike da zargi Alhaji Sulaiman yace "Ba dai zaka ce min Alhaji Badaru ne mahaifinka ba?"
Yanda Baqeer ya kalleshi ne yasa yayi baya ya zauna akan kujera, sai kuma ya miƙe yana haɗe yatsunshi yace "Wai yaron Badaru ne Baqeeru? Ka gaggauta fitar min daga gida ko sai nasa an kulleka, kai dan gidanku ni sa'anka ne? Ko nayi maka kama da wanda zaka zo ma kace kana son ƴa ta? Ba ma gurguntaka kaɗai ba yaron Badaru? Yaron Badarun ma ɗan iskan yaron da ka ja mana tashin hankalin da aka yi mana tsakani?" Cikin ihu yake maganar wanda yasa Zainab dawowa. Baqeer ne ya kalli Alhaji Sulaiman dake kumfar baki yace "Zan ƙara sanar da kaina, nine Muhammad Baqeer Badaru wanda yake son ƴarka Zainab......." Cikin hanzari Alhaji Sulaiman yayi kanshi a fusace don ranshi ya ƙara ɓaci yana ji zuciyarshi har wani tafasa take yi, Zainab har tayo ciki don ta tare sai taji Baqeer yace "Daddy!" Cak Alhaji Sulaiman ya tsaya, eh lallai Baqeer ya gama raina mishi hankali, yama rasa ta inda zai fara ci mishi zarafi, ya zai yi ya tozarta Baqeer yanda ya gama ci mishi mutunci, komawa yayi ya zauna ya kalli Baqeer kawai kafin yace "Daddy?" ya saki wani murmushin takaici sannan ya ɗauki waya ya danna, wani yake kira yace "Naga kasuwarku ɗaya da Badaru ko zaka kirashi kace yazo ya ɗauki nakasasshen ɗanshi da yazo bara gidana?" Yana kashe wayar ya kalli Baqeer yace “Daga Badaru har uwarka wannan karon sai na tozartaku mutanen banza mutanen wofi.” Baqeer kallon Daddy yayi don kalamanshi sun kai shi bango, ƙasan leɓenshi ya ciza don duk yadda yaso ya daure da ɓacin ranshi ya kasa, abubuwan da suka faru baya ke sake dawo mishi tun kafin Alhaji Sulaiman ya tara musu jama'a gwara su bar gidan, kallon Salim yayi wanda gaba ɗaya kana kallonshi zaka san cikin takaicin abinda yake faruwa yake, kai ya ɗaga mishi alamar su tafi, shi kanshi Salim baya ji zai iya cewa Baqeer ya cigaba da zama, Zee wacce Mummy tayi saurin riƙeta ya kalla, ya kauda kai kawai ya fara tura kekenshi, hankali a tashe tace “Ya Baqeer!” Ta kira sunanshi tana tahowa inda yake bayan ta ƙwace hannunta daga cikin na Mummy, hawaye ne fal cikin idanuwanta tana zuwa inda yake suka zubo ta ƙara cewa “Ya Baqeer!” Wani murmushi yayi mata wanda kana ganinshi kasan na menene sannan ya cigaba da tura kekenshi, tana neman binshi taji Daddy yace “Wallahi kina fita sai dai ki nemi wani uban ba ni ba.” Waigowa tayi da mamakin halayen shi ta zuba mishi ido tana tunanin ma me ya kamata tayi. Baqeer bai ko ƙara waiwayensu ba ya ja kekenshi kawai Salim ya turashi don ma suyi saurin fita.
Zee hawaye tasa hannayenta ta share tana kallon Daddy da har yanzu bai gama masifar shi ba tace “Ka shirya ganina a cikin gidan nam har na mutu kuwa don Dady ka sanni ka kuma san kafiya ta, ban taɓa son wani ba sai Baqeer kuma shi kaɗai zan aura, in har kana son ganina nayi aure to ka taimaki kanka ka barni na aureshi.” Tana kaiwa nan ta ruga ciki da gudu don ba ƙaramin wulaƙanta ta Daddy yayi ba, ta sani shekarun baya tana yarinya aka yi abun kuma babban abinda ya janyo saɓanin laifin tane da tayi magana tasan da abun bai kai haka ba, in bata manta ba tun daga case ɗin ta fara canza halayenta, ko rai zai ɓaci to fa zata faɗi abinda ta sani abinda kuma ke ranta.
Daddy wani takaici ne ya ƙara kamashi ji yake yi ko sanda yaji Nabila ƴar Mummy ce ranshi bai ɓaci ba irin yau, kamar shi? Kuma a rasa ma wa zai ce yana sonta sai Baqeer? Lallai bai taɓa fuskantar ɓacin rai irin wannan ba, ga siyasar shi na kawo kai za’a tantance wanda zai hau takarar wato primary election, shafar suman kanshi yayi yana jin wani ɓacin rai, Mummy ce ta zauna kusa dashi tana shafa gaɓɓan bayanshi tana cewa “Calm down Senate, tsautsayi ne ya afka amma yanzu komai zai warware ai insha Allah, bansan ya aka yi wannan abun ya faru ba.” Kallonta yayi idanunshi kaɗai sun isa kasan ɓacin ran da yake ciki yace “Kina ina har hakan ta kasance? Baqeer? Ni Zainab zata gayyatowa matsiyata cikin gida? Taya ma har ta ganshi har suka fara magana?”
Kai Mummy ta girgiza alamun bata sani ba kafin tace “Ni kaina abun ya bani mamaki amma in ka duba laifin na yaron ne, taya zai so Auta? Ta yaya? Ai yasan haɗin ba ɗaya bane.”
Tsaki yayi yace “Zancen banza zancen wofi ni ko da ƙafar shi ai wallahi bai kai na bashi ƴata ba bare,” ya ƙarasa maganar cike da ɓacin rai wanda yake ji kamar zuciyarshi zata fito, miƙewa yayi yace “Duk laifinki ne don kece kike barinta take fita, inba haka ba taya ma ta haɗu da shashashan can?” Yaja tsaki ya wuce ciki da ƙarfi ya rufo kofa.
Mummy ta sauke ajiyar zuciya sannan ta miƙe tayi ɗakin Zee zuciyarta duk ba daɗi, kuka Zee take yi sosai don abinda Daddy yayi ba shakka tasan shikenan Baqeer ya haƙura da ita don dama tasan tunda yasan wacece ita take tantama amma gashi ya daure yazo an tozartashi. Hawaye ta sake sharewa tana kallon wayarta, kiranshi take son yi amma bata san taya zata fara ba.
Ƴar karamar ƙara ta saki daidai nan Mummy ta turo ƙofa.
Chapter 136 · 0% Book details