← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 168

Sashe 131

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Tunda yaji Zainab bata da lafiya hankalinshi ya tashi, lallai lokaci yayi daya kamata ya bayyanar mata da abinda ke zuciyarshi yana ganin batun ɓoye-ɓoye kuma ya ƙare lokaci yayi da zasu san matsayin juna idan yin yi idan barin bari amma ya gaji da raragefe zuciyarshi kullum bata da nutsuwa saboda bai san matsayinshi a wajenta ba. Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi yayi yaga lokaci ƙarfe bakwai saura kwata na yamma, in banda yanzu dare zai yi da babu abinda zai hanashi zuwa wajen Zainab a yanzu amma In Sha Allahu gobe ba zata wuce ba ba tare da yaje ya ga a halin da take ciki ba. Koda ya koma gida sai ya samu kanshi da sanarwa da Dada batun rashin lafiyar Zainab ɗin ya kuma faɗa mata gobe zai je ya dubata. Cikin alhinin rashin lafiyar Zainab ɗin tace "Da kuwa ka kyauta don Zainabu yarinya ce mai mutunci da bata ɗauki rayuwa da girma ba, hausawa ma suka ce gaida me gaishe yadda ta ɗauki al'amuranmu da girma ya dace aje a gaisheta da jiki, wannan zuwa dubiyar ma kamata yayi ace harda ni za'a je." Girgiza kanshi yayi yace "Zan dai faɗa mata kina gaisheta amma kiyi zamanki, kinga bamu taɓa zuwa gidansu ba bamu san irin karɓar da za'a yi mana ba bare da ganin Zainab kasan ba daga ƙaramin gida ta fito ba." Tace "haka ne, to ka gaisheta kace ina dubata da jiki." Ɗakinshi ya wuce zuciyarshi fal tunani sam baya da nutsuwa sai dai yana jin ɗoki da farin cikin kasancewar gobe zai bayyanawa Zainab abinda yake ji a kanta a cikin zuciyarshi. Wayarshi ya ɗauka ya kirata yana so ya ƙara jin yanayin jikinta.
A lokacin da ƙiran ya shigo ta idar da sallah kenan don tun dawowarta tana kwance bata motsa ba, shigowar Mummy ɗakin uku tana tarar da ita a kwance duk a tunaninta bacci take yi bata san tana jinta ba bata son yin magana da ita ne kawai. A kasalance tace "Ya Baqeeer," muryarta na rawa.
Sai da yaji wani abu ya ratsa tun daga tsakar kanshi har zuwa tafin ƙafarshi saboda yadda taja sunanshi. "Ya jikin naki? Hope yayi sauƙi yanzu," Ya tambayeta cike da kulawa. "Da sauƙi Alhamdulillah, ya Dada? Nayi kewarta yau naso na ganta sai kuma nayi rashin sa'a ban sameku a gida ba."
Ɗan murmushi yayi, duk da bata da lafiya amma tana tambayar Dada. Waɗannan halayen nata na daga cikin abinda yasa ta shige zuciyarshi tayi kane-kane ba tare daya shiryawa hakan ba. "Tana nan lafiya tace na gaisheki da jiki."
"Wai faɗa mata kayi?" Ta tambayeshi da mamakin hakan ƙunshe a muryarta.
"Ina dawowa gida na faɗa mata baki da lafiya gobe zanje na dubaki sai tace itama zata je, da ƙyar dai na lallaɓata ta haƙura amma tace lallai nace tana gaisheki da jiki," ya ƙarashe maganar yana dariya.
Cike da jin daɗi take murmushi saboda kulawar da yake bata ya tabbatar mata tanada matsayi a gunsa, ajiyar zuciya yai yace "Magani fa? Kinsha?"
Ta ɗan sauke ajiyar zuciya tace "Nasha paracetamol." Kai ya jinjina yace "Zanzo naga ya jikin naki....." gabanta ne yai wani irin faduwa bata san sanda tace "A'a karka damu Ya Baqeer nasan gobe in na tashi zanji na ware." Mamaki yak da jin kalamanta sai dai ya alakanta hakan da kulawa ne tunda tasan halin da yake ciki, baisan batada lafiya ya ɗaga mata hankali kawai sai yace shikenan.
Suna gama waya ya ƙira Salim yace dan Allah gobe yazo, Salim cike da zargi yace "Inzo? Badai maganar gidan su Zainab din bane?" Baqeer yace "Kai dai kazo ina jiranka." Kafin Salim yai magana ga kashe wayar.
*****
Wannan karon shine karo na biyar daya ƙara kallon jikinshi, ɗinkin dake jikinshi kaɗai abin kallo ne, yayi kyau sosai da sosai. Wani sanyayyen murmushi yayi wanda ya ƙara sawa cikar zati da annurin fuskarshi ta bayyana "Ya Baqeer menene matsayina a wurinka?" Kalaman ta ne suka sake dawo mishi kamar a lokacin take faɗa mishi "Kasan rashin lafiyar me nake yi? Ko kuwa har yanzu zaka ce baka san komai ba?" Nan ma wasu bangare na cikin kalamanta suka sake zuwa mishi. "Yau zan sanar dake matsayin da kika taka a cikin zuciyata," yayi maganar yana sakin wani sanyayyen murmushi kamar ita ce a gabanshi. Salim ne ya saki baki ganin Baqeer yayi kyau caz kai kace wani ango ne yace "Wai ina zamu haka duk kabi ka dameni?" Kallonshi yayi yace "Gidansu Zeey zaka kai ni, bata jin daɗi ni kuma hankalina yaƙi kwanciya gashi akwai amsoshin da nake ganin baki da baki ya kamata na furta mata." Nan da nan tashin hankali ya bayyana a fuskar Salim hankali a tashe yace "Baqeer kayi mata waya mana tazo sai kuyi maganar, gani nake yi ba sai kaje ba." Wani kallo Baqeer ya yiwa Salim, me yasa a duk sanda yake son zuwa gidan su Zainab yake hanashi? Me yake ɓoye mishi ne da baya so yaje ya gani? Nan da nan ya tamke fuska sosai yace "Ko ka kaini ko na nemi wani ya kaini duk ɗaya amma dai yau nayi niyyar zuwa wajenta babu kuma abinda zai saka na fasa." Haka nan ba don Salim yaso ba suka shirya suka fita zuwa gidansu Zainab, adaidaita suka tara ga mamakin Baqeer sai yaji Salim ya ambaci sunan unguwarsu, wai dama Zeey ƴar unguwarsu ce amma shine bai taɓa saninta ba, gaskiya abun da mamaki duk da dai ba cika shiga sabgar mutane yayi ba watakila shine yasa bai santa ba tun da sai yanzu. Koda suka shiga unguwar kallonta kawai yake yi sai yake ganin duk ta canja mishi kamar wanda yayi shekaru bai shigo ba, kasa kallon layin gidansu yayi saboda wani ƙunci da yaji yana neman lulluɓeshi sai dai baya son yayi ruining musu wannan ranar shi da Zainab don haka yayi sauri ya kori duk wani tunani daga zuciyarshi sai na yadda gamuwarsu da Zainab zai kasance.
Babu yadda Salim ya iya haka suka ƙarasa layin gidan, wani tunani yayi ganin ya kawoshi layin gidansu Asiya budurwar data yaudareshi bayan rasa ƙafafunshi, wacce ta juya mishi baya ita da amininshi, nan da nan kuma ya sake kallon layin yana tuno kalamanta data yi mishi farko-farkon haɗuwarsu a wannan layin. Ƙofar gidan da Salim yayi parking ya kalla, gabanshi ne ya fara dukan uku-uku yana jin wani tsoro da fargaba na yawo cikin ranshi, bakinshi ne ya fara rawa yace "Salim ba dai nan ne gidansu Zainab ba?" Ido Salim ya runtse don abinda yake ta gudu kenan tun farko shi yasa yaƙi kawoshi gidan, riƙoshi yaje yi da sauri ya ɗaga mishi hannu alamar kada ya taɓashi sannan yace "Please wheel chair!" Haka ya fito ya buɗe mishi ya hau kan kekenshi na guragu ya tura zuwa ƙofar gidan, duk wani turi ɗaya da zai yi sunan Zainab ne ke dawo mishi cikin ranshi, ba dai? Ba dai Zainab Sulaiman Karaye bace wacce ya sani? Ba dai itace Zeey ɗin da tayi kane-kane a cikin zuciyarshi ba? No No Zeey? Zainab? It can't be. A daidai jikin gate ya tsaya sakamakon kanshi da yaji yana wani irin juyawa, wani irin dum yake ji wanda yasa baya gani sosai, wayarshi ya ɗauka ya tura mata text akan yana waje, sannan ya kalli Mai Gadi yace "Don Allah ba nan ne gidan Sulaiman Karaye ba kuwa?" Hankali a kwance yace mishi "eh nan ne," tura kekenshi baya yayi jikinshi nayi mishi wani irin sanyi, zuciyarshi na bugawa akai-akai kamar zata fasa ƙirjinshi ta fito. "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un, how? Ta yaya? Ta yaya Zainab ɗinshi take fitowa daga cikin wannan gidan? Kallonta yayi nan da nan kamanninta na yarinta suka fara dawo mishi tar a cikin kai, sai data bari sonta yayi tsamari yake jin duk wani bugun numfashin shi da ita yake yi sannan ya ganta a matsayin wacce ko a hanya baya fatan gamuwa da ita? Abubuwan da suka faru a baya a ta dalilin ta ne suka fara dawo mishi, kai kawai yake girgizawa yana tura kekenshi iya saurinshi. Ita kam tun sanda taga saƙonshi akan yana waje tasan shikenan komai ya ƙare, ita kam tasan rayuwarta ta ƙare. Baqeer shine jigon rayuwarta in dai har ya rabu da ita to tabbas rayuwarta tazo karshe.
"Ya Baqeer!" Ta ƙira sunanshi cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa, da sauri ta sha gabanshi ta tsugunna suka yi kai ɗaya tana hawaye tana cewa "Why? Please ka tsaya."
Idanunshi sun kaɗa sun yi jaa sosai, kenan ita tasan shi wanene amma ta raina mishi wayau? Ba dai fansa ta ɗauka akanshi ta hanyar sace zuciyarshi ba? Gagarumin case ɗin da aka yi shekarun baya ne wanda har yasa suka bar unguwar yake dawo mishi kamar a lokacin abun ke faruwa wanda a dalilinshi komai sai da ya kusa tarwatsewa, how? Taya zata yi mishi haka?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
       *Da*
*Umm Asghar*

*BAQEER*
*NA*

*AYUSHER MUHD*
        *DA
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA ƊAYA*

{81}
Chapter 131 · 0% Book details