Sashe 91
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*****
"Abu, Jamila." Ya shigo yana ƙwala musu kira tun daga soron ƙofar gida har ya shigo tsakar gidan bai daina ƙwala musu kira ba. Kowaccen su ta fito daga ɗaki, Abu tace "haba Mallam wannan wane irin kira ne haka tun daga ƙofar gida mutane na ji, ai ko miye ma sai ka bari har ka shigo gida." Wata uwar harara ya jefa mata kafin yace "anƙi a bari a shigo gidan, wallahi Abu ki kiyayeni kada fa kiga ina sakar miki fuska kice zaki kawo mini raini sai naci mutuncin ki wallahi. Ina ƴaƴan naku suke? Wallahi yau sai an fitar mini da ɓarawon da yake zuwa yana yi mini sata a shago don ba yarda zan yi ba, haka kurum kuna nema ku karyani bayan baku san da yadda nayi na samu kuɗi na kafa jarina ba sai yanzu da kuka haifi lalatattun ƴaƴa zaku dinga turasu kasuwa suna yi mini ɗauki ɗai ɗaya tun ana yi da kaɗan-kaɗan ina shiru gashi yanzu har an fara ɗibar masu yawa." Gyara tsayuwarta Jamila tayi tace "sai kaje can ka nemi masu yi maka sata amma dai ba ƴaƴana ba tunda kai kanka kasan karatu suke yi basu da lokacin kansu bare har suje kasuwa suna yi maka sata, ahto. Sata kam ai sai zauna gari banza marasa aikin yi waɗanda basu ajiye komai ba sai yawo daga wannan inuwar zuwa waccan inuwar amma ba ƴan makaranta ba masu abun yi."
Abu da bata saka baki tayi tsalan jin abinda Jamila tace don tasan Kamalu take yiwa gugar zana tace "to wa kike nufin yana yi mishi satar? Ba dai Kamalu kike so kice ba ko? Don wallahi ɗana yafi ƙarfin yayi sata sai dai kaje can ku nemi ɓarawon kayanka amma ba a ɗakina ba. Sannan ai ba mu kaɗai bane masu ƴaƴa ita Fatima me yasa baka kirata ba sai mu kaɗai saboda mu ka rainawa wayo." Gaba ɗaya sai suka kalli ƙofar ɗakin Umma da duk abinda suke yi tana jin su bata saka musu baki ba ganin ba'a saka da ita ba, ko yansu ma da Abu ta ambaci sunanta bata nuna taji su ba bare ta fito tace wani abu sai ma ta gyara kwanciyar ta tana cigaba da jan carbinta kamar bata ji meke faruwa a tsakar gidan ba.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA SHIDA*
{56}
Ana cikin haka sai ga Kamalu ya shigo ai kuwa Badaru na ganin shi ya damƙi hannunshi yaja shi har ɗakinsu yana cewa "Wallahi bazan yarda ba sai ka fito min da kayana da kake zuwa kana sacewa a kasuwa, nasan babu mai yi min wannan aikin sai kai tunda duk cikin ƴaƴana kai ne gagararre, haihuwa asara." Abu da tun lokacin da ya fara jan Kamalu ta biyo bayansu tayi caraf tace "A'a wallahi Mallam kada ka ƙara kiran ɗana da haihuwar asara haka kuma ban haifi ɗan iska ba, haba ace yanzu duk cikin yaran gidan nan Kamalu kaɗai zaka tsame kace shi yayi maka sata saboda shi an tsane shi ba'a son shi. Idan da gaskiya ai sai kayi bincike idan ka kamashi da laifi sannan ka iya cewa komai ba yanzu da kake lalube cikin duhu ba." Duk da hararar da yake jifanta dashi bai sa tayi shiru ba sai da ta dasa aya tukuna, shi kuwa Kamalu fito ma yake yi da baki yana kallon su ɗai-ɗaya kamar bai fahimci akan me suke hatsaniyar ba. A fusace Badaru yana nunata da yatsa ya fara faɗin "Duk wa ya lalatashi idan ba ke ba shine har zaki zo kina cewa an tsane shi za'a yi mishi ƙazafi, to ba lalataccen bane haihuwar asara wanda bai iya tsinananwa kanshi da komai ba sai dai ayi mishi. Wallahi tun muna shaida juna ka fito min da kayana idan ba haka ba kotu ce zata rabani da kai," ya ƙarashe maganar yana kallon Kamalu da sam hankalinshi baya wajenshi, kaya ne dai yaci kuma ba zai bayar ba sai dai ya ɗauki duk matakin da yake ganin ya dace, dolene ya saci kaya ya hada lefe ehe!
Kallon Badaru yayi a wani shagiɗe cikin magana irin tasu ta gagararrun ƴaƴa yace "Don baka so na ba shine zai sa ka ƙala mini sharri ba, haka kurum kowacce shara ka ɗebo sai ka watsa ta a kaina, to idan baka so na ka kai ni bolar ƴaƴa ka jefar mana."
Baki buɗe Badaru yaje kallonshi, da ƙyar ya iya cewa "Ni kake faɗawa maganar banza irin wannan Kamalu? To wallahi zaka fita ka bar min gida kaima tunda ba da uwarka muka haɗa kuɗi muka yi ginin ba ah to, na kori Baqeer ma babu abinda ya dameni bare kai gayyar tsiya haihuwar asara."
"Kafa daina aibata mini ɗa Mallam bana so, kaje can ka nemi ɓarawon kayanka amma ba Kamalu ba. Taho mu tafi kaji," ta cewa Kamalu, suka fice suka bar Badaru a ɗakin yana cigaba da bambamin masifa don fa ba yarda zai yi ba sai an fito mishi da kayanshi, haka kurum yana ji yana gani ba za'a yita saka shi asara ba.
*****
Tun daga waccan ranar Kabir ya ƙara janyewa daga Nabila tunda ya fahimci babu alkhairi a tattare da taraiyar su, gaba ɗaya ya ƙauracewa zaman gidan idan ya fita tun safe baya dawowa sai dare ya tsala sannan kuma ya daina barin ƙofar ɗakin shi a buɗe ko shiga kawai zai ya fita kuwa. Duk wata hanya da Nabila zata ganshi ta ƙara cusa kanta a wajenshi yayi ƙoƙari ya tosheta to itama ta ɗan ja baya dashi tunda wancan al'amarin ya ratsa tsakaninsu. Yanzu ba kasafai ta fiye nemanshi ba saɓanin da da ko bata ganshi ba ta dinga damunshi da waya kenan tana tambayar yaushe zai dawo gida yau tunda ta tashi bata sanya shi a idonta ba, irin waɗannan abubuwan dai da take amfani dasu tana manipulating ɗin shi don shi sam babu sonta a cikin zuciyarshi, to ta yaya ma hakan zai kasance bayan ga matsayinta a wurinshi, gashi yanzu duk yadda ya kai da kauce mata sai da ta janyo suka aikata abinda tun farko yayi ta guje musu afkuwarshi.