Sashe 151
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannun ƙofar ya saki tare da zubawa ƙofar ido, kalaman Nabila ne suka dawo dashi daga hayyacinshi “Koma menene Kabir nake so, in har da gaske kina so na kamar yadda kika ce to kisan yanda kika yi na aureshi, shi nake so kuma shi nake son aura.” Mummy ce ta katseta a fusace tana cewa “Sanda nake ta ce miki a’a ki bari kin ji magana ta? Ko har yanzu baki san shirmenki bane ya samu cikin situation ɗin da muke ciki yanzu? Da kin barni ni nasan yadda zan yi ki aureshi tunda ba aure ne ya haramta tsakanin ku ba amma shirmenki da gaggawa yasa kika lalata komai, banda dai ni nasan takan komai da yadda zan gyara abu da tuni kin kashe mini aure, to sa’a ta ɗaya Alhaji Sulaiman a tafin hannuna yake, sai yanda nayi dashi daga shi har yaranshi, ba boka ba Malam amma duk a tafin hanuna suke, ita kanta wacce ta nemi yi mini gardama na rabata da mahaifinta,” tayi tsaki sannan ta cigaba “Amma da yake ke sam baki da haƙuri gashi nan kin rasa Kabir ɗin, da kin bi maganata sanda nace a’a da yanzu sai yanda kika yi dashi, ko kina tunanin lokacin da kike munafircin kyawawan halaye duk ba training nake yi miki a fakaice ba?” Nabila kallon Mummy kawai take yi cike da mamaki kafin tace “Ke ba son su kike yi ba ni kuwa Kabir son gaskiya nake yi mishi, kuma Allah in kina so hankalina ya kwanta ki san yadda kika yi na mallakeshi.” Tsaki Mummyn tayi tace “A yanzu ko zai aureki bazan baki shi ba don kuwa babu dalilin da zai sa ki aureshi, primary election ɗin ma har sun faɗa ya faɗi, gashi yana asibiti yayi accident na kira driver ɗinshi naji meke faruwa saboda bani da time na yawon asibiti yake sanar dani ƙafarshi kamar ta samu matsala, to faɗa min me yake dashi da zan bashi ke? Bayan rabin dukiyarshi tawa ce.” Kabir duk yadda yaso ya daure akan abubuwan da kunnenshi ke jiyo mishi kasawa yayi ji yayi ƙafafunshi na neman kayar dashi ƙasa, da sauri ya dafa bango sannan ya fara jan ƙafafunshi yana tafiya kamar wanda bashi da laka, zuciyarshi bazata iya tsayawa ya gama jin abinda kunnenshi ke jiye mishi ba, waje kawai yayi ya shiga mota, ko tankawa mai gadi dake tambayarshi har ya fito bai yi ba, da ƙyar ya iya sawa motar key sannan ya bar layin. Kalaman Mummy ne ke sake mishi rito a zuciya wanda yake ji kamar ana sake dawo mishi dasu cikin kunnuwanshi, da ƙyar ya isa asibiti sai dai ya kasa fita daga motar kawai ya zauna yana tunanin wannan rayuwa, taya zata riƙesu shekara da shekaru ta dinga irin wannan furucin? Ya daɗe a haka kafin wayar Zainab ta shigo wayarshi, da sauri ya ɗauka yace “Kin iso?” Hankalinta a tsananin tashe tace “Ya Kabir kuna ina? Gamu yanzu mun shigo.” Kwatancen inda zata sameshi yayi mata sannan suka yi sallama, basu fi minti uku ba sai gasu sun iso lokacin yana waje yana jiransu. Da sauri-sauri gudu-gudu ta ƙaraso idanunta taf da ƙwalla tace “Ya Kabir ina Daddy?” Wani abu ya haɗiya tare da kallon Mubashir sannan yace “Muje.” Nan suka shiga ciki, duk ta rikice kawai Daddy take son gani, Kabir ne yace “Zainab akwai ragowar payments da bamu yi ba wanda ni kuma babu ragowar kuɗi a wurina.” Mamakin kalamanshi ne yasa ta kalleshi sai dai bata da lokacin wannan hakan yasa ta miƙa mishi card ɗinta ta sanar dashi pin sannan tace “A ina Daddyn yake?” Nan ya sanar da ita ɗakin ita dai hankali a tashe take tafiya, Mubashir ne yabi bayanta. Kabir sai daya biya ragowar kuɗaɗen sannan ya dawo inda Daddy yake. Tunda Zainab taga halin da Daddy yake ciki take kuka, kuka kawai take yi, a hankali ya ɗan motsa hannayenshi sannan ya buɗe ido kamar mai jin bacci ya saukesu a kanta, wani murmushi yayi mata na tausayi sannan ya maida idon ya rufe da alama dai maganin da drip ɗin da aka saka mishi akwai na sa bacci, kallon Kabir tayi tana hawaye ta kalli ƙafar da aka naɗeta da bandage tace “Ya Kabir ya zamu yi?” Kai ya girgiza alamar rashin sani kafin ya share ƙwallar shi yace “Ina ji duk alhakina ne ya sauka akan Daddy, Zainab na shiga uku….” Ya ƙarasa maganar yana dafa bango don shi kaɗai yasan me zuciyarshi take ji a wannan lokacin. Fitowa tayi daga ɗakin tace “Ya Kabir zo.” Bai musa ba yabi bayanta har sun kai bakin ƙofa ta kalli Mubashir tace “ƙanina ɗan zauna anan kaɗan yanzu zan dawo.” Cewa ƙanina da tayi yasa Kabir ƙara kallon yaron, wani abu ya haɗiya don yanzu kam ya tabbatar yaron nada haɗi da Ummi ko ba ɗanta bane yasan yaron dai wani nata ne. Fitowa suka yi suka zauna daga gefe, kallonshi tayi tace “Ina Mummy?” Kalmar Mummy da tace yasa ya kalleta ji yayi wani abu ya tsaya mishi yace “Zainab ashe matar nan ba tsakani da Allah take son mu ba.” Yanayinta ne ya canza tace “Ba dai wani abun tayi maka ba?” Kai ya girgiza zuciyarshi na zafi ya sanar da ita abinda ke faruwa.” Hawaye Zee ta goge tace “Ya Kabir me yasa kaga na bar gida ban ƙara waiwaye ba? Na gane halayenta ne kuma kai da Daddy kun kasa bani dama na sanar daku wannan dalili yasa naƙi dawowa.” Nan ita ma ta kwashe komai ta sanar mishi, mamaki duk ya hana Kabir magana, sai hawaye kawai da yake ta zubo mishi saboda tashin hankalin da yake fuskanta wurin matar da yafi yarda da ita a duniya fiye da kowa. “Zainab na faɗa miki alhaki ne, na yar da Ummi gashi nan abinda ya sameni, ya zan yi? Wannan daya kawoki wanene?” Murmushi tayi tace "ƙaninka ne wanda baka sani ba.” Kai ya kauda yana maida kwallar dake neman zubowa yace “Wacce muka yi waya fa?” Tace “Ita ma.” Ido ya runtse, tausayinshi ya kamata tace “Ya Kabir ka girma yanzu don Allah, yanzu dai kana ganin yadda rayuwa ta zo mana, matar nan haka ta dinga zuga Daddy yana kwaso kuɗin da ba nashi ba na gomnati yanzu kaga ko zuwa ta dubashi bata yi ba.” Kwafa yayi yace “Rayuwa ce tayi abinda ranta ke so.” Haka suka koma ɗaki suna ji suna gani aka shiga da Daddy aiki, takaicinta ɗaya da bata dage wajen sanar da Daddy da Kabir halin Mummy ba har sai sanda aka zo lokacin da abu ya riga ya ƙure. Mubashir ne ya siyo musu ruwa ya miƙawa Kabir ɗaya, kallonshi yayi idanunshi sun ciko hannu ya miƙa mishii alamar musabaha, Mubashir shima ya miƙa mishi, ji yayi zuciyarshi na ƙara karyewa kawai sai ya rungumeshi. ***** A hankali Baqeer ya kai hannu saman goshinshi da yake ji kanshi nayi mishi ciwo, Tanimu ne ya kalleshi yace “Ya Baqeer ka koma gida ka huta don Allah, ni zan kula da ayyukan da ake yi anan.” Kallonshi yayi sannan ya kalli kayan mutanen da yake taso a gama haɗa musu don yana da buƙatar wasu kuɗin ya haɗa da na hannunshi ya biya ragowar kuɗin gidan, in yaso a hankali ayi funitures ɗin da ya kamata, zai sake magana Tanimu yace “Don Allah kaje ka huta.” Murmushi yayi yace “Kai ma ka iya magiyar Salim ko?” Kai ya sadda ƙasa yana shafa bayan kanshi, tare suka fito suka shiga mota akan in ya kai shi zai dawo shagon shi. Kanshi ya maida jikin window yana kallon mutane, motar data gifta ta gefensu ya kalla da kuma sauri ya kalli number motar, sai dai bai iya duba number sosai ba ta wuce, kai ya girgiza tunowa da yayi ba ita kaɗai bace mai irin motar, sannan in da sabo ya saba ganin irin motar yana duba plate number yaga ba nata bane, ido ya ɗan lumshe sannan ya buɗe yana tunanin anya bai fi son Zainab akan yadda take sonshi ba kuwa? A wani shagon Rufaida yoghurt ya tsaya ya ɗan yi siyayya sannan suka wuce, ya bawa Tanimu nashi shi kuma ya shiga gida. Hadiza tayi wankin ragowar kayan Umma wanda aka zubar a waje suka ɗan ɓaci, gaisawa suka yi yace “Maimakon ki bari in za’a kai wanki a haɗa?” Tace “A’a ba komai, dama ɗazu muka zo ni da Maryam to ita ta koma saboda nemanta da mai gidan yake yi shine nace bari na ƙarasa kafin na tafi.” Kai ya jinjina yace “Yanzu dai ba matsala ko?” Dariya tayi tace “Inafa matsala ai Ya Baqeer yanda kasan ba Baban su Husaini ba haka yake min, nan nan yake dani tunda yaga ina samun kuɗi sosai, sannan kaga saida atamfofi da nake online ɗin nan shima ba ƙaramin taimaka min yake ba, ni dai kam ba abinda zance maka sai fatan Allah ya kara lafiya ya kawo mace ta gari.” Bai amsa a fili ba sai dai yace Ameen a ranshi. Mayafi ta ɗauko ta yiwa su Umma sallama sannan ta tafi. Dada ce suna gaisawa tace “Ni kam Baqeer auren mahaifiyarka kashe mata shi kayi ko me? Ita ta biyeka kai kuma banga kana da niyyar maidata ɗakinta ba.” Kai ya kauda yace “Da wannan auren da babu shi duk daya ne.” Baki Dada ta saki kafin tace “Koma dai menene ka maida ta ai dai ɗakinta shine darajarta.” Kallonta yayi sosai yace “Dada bafa zata koma ba, ni gidan dana siya ma na kusa gama biyanshi maidaku can zan yi.” Kallon mamaki suka yi mishi, ya shige ɗaki ba tare da ya ƙara cewa komai ba, Dada ce tace “Fatima nima ba son zamanki da Badaru nake yi ba amma aure da ƴaƴa kun riga kun zama ɗaya.” Murmushi ta yiwa Dada tace “Ke kika san mun zama ɗaya Dada amma ba Badaru ba, ni ba kashe aurena zan yi don ɗana Allah ya azurtashi ba kawai dai bazan koma bane har sai yayi nadama ya canza hali.” Jin haka yasa Dada kallonta, tabbas Badaru bashi da imani ita kanta tana bada shawarar ne a matsayinta na uwa wacce tasan hakan bai dace