Sashe 160
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
DA
AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA TAKWAS*
{98}
Sababbin designs ɗin da yake aiki akai ya zauna ya fitar, sai da ya gama har yayi uploading ɗin su cikin computer da suke aiki da ita sannan ya kira Salim ya faɗa mishi zasu fita in anjima bayan sallar magrib, bai faɗa mishi inda zasu je ba yace idan sun je ya gani duk da ma dai Salim ɗin yasan ba zai wuce gidansu Zee zasu ba. Ana yin sallar la'asar ya tashi daga aiki, daga masallaci basu koma shagon ba yace da Tanimu su tafi gidan Maryam, so yake yi suje su gama da wuri don baya so ya ɓata lokacin shi na zuwa gidansu Zainab. Suna isa bakin gate ya ɗauki waya ya kira Maryam yace mata gashi a wajen gate tazo ta shigo dashi.
Tashi tayi cikin farin cikin yau Ya Baqeer ne a gidanta don ba zata iya tuna rana ta ƙarshe daya tako ƙafarshi zuwa gidanta ba tasan dai tun kafin ya samu accident ne. Fitowa tayi daga ɗaki ta faɗawa Baban Aareef dake zaune a parlourn Ya Baqeer ne yazo ya fita ya shigo dashi ciki. Shima yayi mamakin da jin Baqeer ɗin yazo gidan saboda daɗewar da yayi bai zo ba sai kuma lokacin yaji yana kunyar haɗuwa da Baqeer ɗin don duk tsawon lokacin nan bai taɓa zuwa yaje ya duba shi ba har Allah yasa ya samu lafiya ya cigaba da harkokinshi. Haka nan dai ya tashi ya fita jikinshi a sanyaye don ba zai yiwu ya barshi yana jira ba, surukuta ce sosai a tsakanin shi da Baqeer ɗin, yana girmama shi yana ganin mutunci saboda yadda yake tsaye akan al'amuran ƙannen shi ya ɗauki girman da Allah ya bashi.
Yana fita ya ganshi akan wheelchair ɗin shi don tuni ya fito daga cikin motar yana jiran Maryam tazo ta shiga dashi cikin gidan, tunda uban mijinta ya dawo gidan da zama ya daina shiga kanshi tsaye saboda kaucewa gutsuri tsomar ƙananun maganganu bare daya fahimci halin mahaifin Auwal ɗin.
Yana wani sussunkuyar da kai ya miƙa mishi hannu suka gaisa shi kuwa Baqeer sai bai nuna ma yasan abinda yake yi ba. Zuwa yayi zai tura wheelchair ɗin Baqeer ya ɗaga mishi hannu ya nuna mishi remote control ɗinta yace "kada ka damu ba sai ka turani ba zata tura kanta." Ɗan murmushi yayi ya koma gefe, gaba yayi Baqeer na biye dashi a baya har suka shiga cikin gidan babu wanda yayi magana. Suna shiga Maryam ta tashi da fara'arta ta tareshi tana yi mishi sannu da zuwa, Aareef na zaune akan kujera yana kallon cartoon. Yana jin muryar Baqeer ya taso yana yi mishi oyoyo ganin shi zaune a wheelchair sai yasa yaron yayi turus yana kallon shi. Hannu ya miƙa mishi yace "zo mana Aareef, zo mu gaisa na daɗe ban ganka ba."
Kasa zuwan yayi sai juyawa da yayi yana kallon Maryam, sai data ɗaga mishi kai sannan ya ƙarasa wurin Baqeer yana mamakin yadda ya ganshi haka har dai ya kasa yin shiru sai da ya tambayeshi.
"Uncle Baqeer me ya sameka na ganka akan wheelchair?"
Murmushi yayi yana shafa kan yaron yace "Accident nayi Aareef Mommynka bata faɗa maka ba?"
Da kai ya amsa mishi yana kallon kujerar wheelchair ɗin with curiosity. "Zaka sauka ka bani na ɗana?" Dariya Baqeer yasa jin abinda yaron yace sai ya ɗaga mishi kai alamun amsawa, su kuwa iyayen sai girgiza kai suke yi Maryam ji tayi kamar ta makeshi don haushi. Korashi ciki tayi don tasan idan har yana wurin ba zai bari su gaisa da ɗan uwanta cikin nutsuwa ba wanda alamu suka nuna akwai abinda ya kawo shi, tafi bayarwa dai ko Umma ta faɗa mishi matsalarta ne shi yasa yazo.
Kitchen ta shiga ta haɗo mishi ruwa da drinks ta ɗora akan tray haɗw da cups ta kawo, sai da tsiyaya mishi ruwa da kemon duka a kufuna ta ajiye a gabanshi sannan ta samu wuri ta zauna ta soma gaishe shi. Bayan nan suka cigaba da hira jefi-jefi shi da Baban Aareef, anan ne ma yake bashi haƙurin rashin zuwa dubashi da bai je yayi ba ya kawo uzurin abubuwa ne suka sha kanshi shi yasa bai samu yaje ba. "Ai babu komai," Baqeer yace don bai ga amfanin ɗago wannan maganar ba.
Gyara zamanshi yayi akan wheelchair ɗin sannan ya kalli Auwal sosai yace "wurinka nazo akan maganar Maryam." Kallonshi yayi sosai, shi dama tunda ya ganshi yasna dole akwai abinda ya kawo shi don tun da can baya zuwa musu gida haka nan sai idan sun samu saɓani shi da Maryam ko shi ya kira shi ko ita idan ta kirashi amma yawanci ma shine yake kai ƙararta. Gyara zamanshi yayi yace "wani abu Maryam ɗin tace anyi?" Kallonta Baqeer yayi yace "maimaita abinda kika ce yayi miki." A nutse ta buɗe baki ta fara magana, duk wata matsala da take da ita a zamanta da Baban Aareef da mahaifin shi yau sai data faɗawa Baqeer harda shigo mata da yake yi ɓangarenta kanshi tsaye akan hakan yasa yanzu ta daina zaman parlour kwata-kwata, a ƙarshe tace "to yanzu aiki ne ya sama min tun kwanaki don ya daɗe da yin alƙawarin zai barni nayi aiki saboda na faɗa mishi ina da sha'awar yin aikin, har nan ya kawo mini offer ina ta murna sai da ya fita sallah ya dawo yace wai wannan maganar a barta saboda sun yi magana da Baffa, nace ya faɗa min wacce magana ce suka yi da zai sa a hanani aiki bayan ansa min rai yace wai maganarsu ce shi da mahaifinshi nace to ai nima ta shafeni tunda akai na aka yi. Haka nan dai na haƙura da aikin ba don naso ba, nace mishi to tunda ba zai barni nayi aikin ba ina so zan koma makaranta nayi masters nan ma yace a'a ni kuma zaman haka ya isheni idan suka fita daga gidan nan haka zan yini ni kaɗai har sai sun dawo don haka nace mishi ina so zan fara snacks na sayarwa tunda abu ne ina daga cikin gida zan yi yace babu damuwa hakan shawara ce mai kyau kawai yana fita sai dawowa yayi yace wai batun sana'ar nan a haƙura kawai don shi baya son mutane suyi ta shigo mishi gida suna fita yanzu kuwa ina fara sana'a za ayi ta sintirin shigo mishi ana gane mishi sirrin cikin gida ni kuwa nace ita ma sana'ar da zan yi Baffan ya hana to kuwa in dai ba za'a barni nayi sana'a ba sai a ƙyaleni na fita nayi aiki don ba zai yiwu komai nace ina so ba sai an kushe shine yace wai ina yiwa mahaifinshi rashin kunya ni kuma Ya Baqeer gani nayi ba Baffa nake aure ba don me yasa zai dinga shiga rayuwata sai mun gama tsara magana da mijina sai ya rushe kuma ace bazan yi magana ba alhalin ni ake cuta," ta ƙarashe maganar muryarta na karkarwa alamun kuka take ƙoƙarin dannewa.
Tunda ta fara maganar duk suka yi shiru suna saurarenta har sai da tayi shiru sannan Baqeer ya kalli Auwal yace "haka aka yi?"
Gyara zamanshi yayi yace "Eh Ya Baqeer sai dai kada ka manta Baffa mahaifina ne dole nayi mishi biyayya akan duk abinda yace ita kuma Maryam sai tace ba haka ba to tana nufin sai abinda take so zan bi na take ra'ayin mahaifina."
Shiru Baqeer yayi yana auna maganganun da dukkansu suka yi, kallon Auwal yayi yace "Da farko dai wacce magana take yi akan mahaifinka yana shigo mata har nan da gaske ne?" Don duk cikin maganganun da Maryam tayi wannan ya fi ɓata mishi rai. Shiru yayi ya kasa amsawa. Sai ya cigaba da cewa "da gaske ne kenan tunda kayi shiru, to maganar gaskiya dole ka dakatar da mahaifinka daga shigo mata cikin gida tunda shi ɗin ba muharraminta bane kai ko muharraminta ne bai dace ya shigo mata ba tunda bai san a wane irin yananyi zai risketa ba bayan haka ita ɗin yanzu baliga ce babu dalilin da zai sa don tana aurenka mahaifinka ya dinga shigo mata ɗaki, idan kuma baza ka iya hanashi shigo mata cikin gida ba sai ka canja mata muhalli don aure take yi ba bauta ba, idan bata sake a cikin gidanta ba a ina ake son taje ta sake. Sannan kuma maganar sana'a da tayi ina ganin kayi haƙuri ka ƙyaleta tayi tunda dai baka son aikin kuma ta haƙura idan yaso sai ka gindaya mata sharuɗɗa akan yadda kake son ta tafiyar da kasuwancin nata."