← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 168

Sashe 67

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe goma sha ɗaya na safe Zeey ta gama shirinta tsaf ta fito cikin sabon ɗinkinta don haka nan taji kayan da take so ta saka kenan, tana so taga ya Baqeer zai yi idan yaga kayan a jikinta, ta dade a jikin madubi tana bin jikinta da ɗin kin da kallo, murmushi ta saki mai sanyi dan ta tabbatar wannan ɗin kin dan ita akai jiyake kamar ta samu guri mai mahimmanci a gun Baqeer.
A ɗakin Mummy ta sameta tana shirya kayanta da aka kawo daga wajen wanki a cikin wardrobe. Kallonta Mummy tayi ta mata alama da tayi kyau sosai, murmushi tai tana ɗan juya mata ɗin kin, nan da ban Mumy kuma ta canza ganin alamar shirin fita tayi tace "Yau kuma sai ina? Kin dai koyi yawo Zeey, kusan kullum yanzu sai kin fita, wai shin ina kike yawan zuwa ne?" A ɗan shagwaɓe ta hau turo baki tana bin bango tace "Yawo kuma Mummy? Please ki bari kada wancan ɗan sa idon ya jiki yanzun nan sai yaje ya haɗani da Daddy ina zaman -zamana yasa a hanani fitar ma gaba ɗaya." Dariya Mummy tayi tace "To nayi shiru amma dai don Allah kada ki daɗe sannan kuma a rage yawan fitar nan haka nan please." Rungume Mummyn tayi tace "To Mummy ba zan daɗe ba ai I promise, sai na dawo."
Tana fita shagon ɗinkin ta wuce don ko yau da safe sai da tailorn ya turo mata da saƙon text yana yi mata tuni wai kada ta manta yau ne zata kai shi wajen me zane. Koda ta isa bata fita ba sai ta tsaya a mota ta danna mishi horn kawai, shima da yake dama ita yake jira tun ɗazu yana ganin lokacin da tayi parking ɗin motar ya taso da hamzari ya fito. "Ranki ya daɗe sannu da zuwa" yace fuskarshi a sake cike da nishadi bayan daya ƙaraso wurin. Buɗe mishi gaban motar tayi sai dai ya mayar da murfin ya rufe yace mata "Ai ina ganin bari kawai na ɗauko babur ɗina sai na biyoki a baya ko?"Ɗaga mishi kai tayi alamun amsawa kawai dan dama kawai dan abun ya shafi Baqeer ne amna batasa mutane a motarta.
Haka suka tafi tana gaba yana biye da ita a baya har suka ƙarasa gidan Dada. Fitowa tayi daga motar bayan ta rufe ne ta juyo ta kalleshi tace "Bari na fara shiga na sanar musu zan kiraka sai ka shigo."
"To" kawai yace mata yana mai ɗokantuwa da son ganin mai zanen da kuma wasu style zanen da yayi don ko waɗanda Zeey ta nuna mishi jiya sosai suka tafi dashi. A tsakar taga Baqeer shida Dada, ita tana gefe tana sauraran radio shi kuma hana zaune yana zane suna hira sama-sama, sallamarta kawai waji yaji komai ya tsayamai dakewa yai bai dago ba sai dai bai iya cigaba da zanen ba.
Dada ta fara lale lale, cike da fara'a dan tana kaunar Zainab sosai, kallan Baqeer tai tana kusa da Dada jnda take gaisheta tace "Sai a ganka ai kamar ba'a ganka ba."
Dagowa yai suka haɗa ido, tace "Nida tailor ɗin ne."
Dada tai caraf tace "In akai kamar ba'a ganki ba ai ni na ganki ko? Kinga share wannan dukum-dunkum ɗin, yi maza kice ya shigo." Kalmar da Dada ta haɗa Baqeer dashi ne yasa yai saurin kallanta, bata ko bi ta kanshi ba Zeey ta mike tana kunshe dariyar da ke neman kwace mata suna haɗa ido da Baqeer ta kira Sani a waya tace ya shigo.
Da sallama a bakin shi ya shiga gidan sai ya tarar dasu zaune a tsakar gida sai Baqeer dake zaune akan wheel chair ɗin shi don ko da Zainab tazo ma anan ta iskesu da wasu sketches ɗin ajiye a gefenshi ga wani akan cinyarshi yana zanawa ita kuwa Dada tana ƴan kaye-kayenta a tsakar gidan.

Sosai Sani tela ya kalleshi yana mamakin wai dama gurgu ne mai yin zanen? Gashi dai tabbas yaga zahiri tunda gashi nan ma wani zanen ne akan cinyarshi yana yi, Allah mai iko. Hannu ya miƙe mishi suka yi musabaha kafin yaja kujerar daya gani a gefe ya zauna yana gaishe da Dada. Kallon Baqeer Zeey tayi tace "Ya Baqeer ga tailorn da ya ɗinka mini kayan daka zana, tunda ya gani yace na haɗa shi da kai kamar dai yadda na faɗa maka na kuma faɗa mishi dama bazan yi maganar kuɗin aikinka daga ni sai shi ba sai dai yazo na kawo shi wurinka kuyi magana." Gyara zama Sani yayi yace "Yallaɓai ina faɗa maka tunda na ɗora kayan Hajjaju akan IG bayan an ɗinka mutane ke damuna gashi kuma tace bata son kayanta su zama uniform" ya ɗan yi dariya sai kuma ya cigaba da cewa "Na tabbata idan nayi amfani da designs ɗin wurinka kamar dai yadda Hajjaju ta nuna min wasu jiya ba ƙaramin alheri za'a samu ba shi yasa ma nake so mu haɗa hannu waje ɗaya ka dinga yi mini zanen tunda Allah yayi maka baiwa ta nan ɓangaren ni kuma ina ɗinkawa sai mu tsara yadda zan dinga biyanka." Sai sannan yayi shiru yana kallon Baqeer yana jiran yaji me zai ce.
Bai ce mishi komai ba har sai da ya gama zana takardar dake gabanshi sannan ya haɗata da sauran waɗanda ya zana ya miƙa mishi. Karɓa yayi yana kallon styles na garari irin waɗanda bai taɓa mafarkin gani ba, tuni fuskarshi ta washe da fara'a yana jin tamkar yayi fice a harkar ɗinki ya gama idan har zai na ɗinka irin waɗannan styles ɗin. Kallonsu yake yi yana ƙarawa ya kasa daina kallon sketches ɗin , ita kuwa Zeey kallon shi kawai take yi tana murmushi sai kuma tace "Ai na faɗa maka idan kaga designs ɗin shi sai ka ruɗe."

"Ai kuwa dai gashi nan na ruɗe don na rasa ma wanda zan fitar nace yafi saura kyau," yayi maganar yana ƙara ɗaɗɗaga takardun. Da ƙyar dai ya iya ajiye papers ɗin sannan ya kalli Baqeer yace "Yo yallaɓai akan nawa zaka bani?"
Kallon inda Zeey take yayi sai yaga ita ma shi take kallo, gira ya ɗage mata irin ya dai sai ta taɓe baki ta kawar da kai tana jin haushin yadda take ɓarar da ajinta idan har tana zaune a gaban Baqeer bata iya kawar da kai bata kalleshi ba. Mayar da kallonshi yayi ga telan yace "Duk da ban taɓa sayar da zane na style ɗin kaya ba bana sayar da paintings ɗina at nothing less than 100k so nawa kake ganin zaka iya biya?"
Baki Sani ya saki jin manyan kuɗin daya ambata, kallonshi yayi ya marairaice fuska yace "Haba Yallaɓai har dubu ɗari bai yi yawa ba, ina ma laifin dubu ashirin haka zuwa dubu talatin?" Wani miskilallen murmushi ya saki kafin yace "Anya kuwa ka shirya yin kasuwanci dani? Daga dubu ɗari ka dawo dubu ashirin, kaso ɗaya a cikin biyar na abinda nace fa kenan?" ya miƙa mishi hannu da nufin ya bashi sketches ɗin. Ƙara damƙe su Sani tela yayi yace "Haba Yallaɓai ai ba za'a yi haka ba, yanzu dai kayi mini ragi a yadda zan iya biya amma dubu ɗari tayi yawa akan kowanne zane tunda ba guda ɗaya zan karɓa ba." Kallon Zeey yayi yana so tasa baki Baqeer yayi mishi ragi sai dai yaga ita ko a jikinta kawar da kai gefe ma tana yin game a wayarta don a ganinta wannan ba maganarta bace tunda bata da wani sani akan harkar zane da yadda ake sayar dasu shi yasa bata saka musu baki ba ta ƙyalesu suyi cinikin a tsakaninsu. Ƙara marairaice fuska yayi yace "To nawa zan biya yallaɓai?" Jin da yayi Baqeer bai ce komai ba. Shima kallon Zeey yayi sai yaga hankalinta ma baya wajensu don haka ya cewa Sani "To ka kawo 50k each take it or leave it daga haka ba zan ƙara yi maka ragi ba" ya haɗe fuskarnan kamar wanda bai taɓa dariya ba don shi sam baya so a nemi raina mishi wayo akan sana'arshi. Ko da ba irin waɗannan zanen yayi ba a baya ai yasan nawa yake sayar dasu don haka yanzu ma babu dalilin da zai sa ya sayar da zanen shi a kuɗi ƙalilan, sannan mutane sau da dama sun iya tayin wulakaanci da nuna bakasan darajar abu ba, kowa kanshi ya sani ada farkon fara zanenshi haka mutane sukai ta maidashi wawa sai dai bayan yasan darajarsa ya canza.

"To Yallaɓai nagode, yanzu bari na zaɓi kaɗan idan yaso daga baya sai na ƙara. Hajjaju ko zaki taya ni zaɓe ne don ni nama rasa wanda zan ɗauka kowanne ba baya ba wajen tsaruwa,”ya ƙarashe maganar yana kallon Zeey. Karɓa tayi tana dubawa sai kuma tace mishi guda nawa kake so?"
"A yanzu dai guda huɗu nake so idan yaso daga baya sai na ƙara zuwa na karɓi wasu tunda ma naga wuri."Guda huɗu da suka fi yi mata kyau ta ware ta miƙa mishi, hannu biyu yasa ya karɓa yana ƙara kallon waɗanda ta zaɓa din. Tabbas waɗannan styles ɗin idan yayi su zasu janyo mishi customers sosai yasan kuma In Sha Allah zai samu alkhairi a ciki. Godiya yayi wa Baqeer ɗin kafin yace "Yanzu dubu ɗari ce a jikina cash da zan kai banki ko zaka karɓa in yaso idan na koma shago sai na ciro maka sauran?"
Chapter 67 · 0% Book details