Sashe 86
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
Da
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA HAMSIN DA UKU*
{53}
Yau ta fito zasuje wani guri ita da Nabila taga layinsu cike da mutane, baki ta taɓe tace "Bai wuce aure ake." Nabila ce ta kalli gun tace "Kamar fa yarinyar nan ƴar iyayin nan ake aure dan naga pictures ɗinta a IG da farko ma ban gane ta ba sai da naga kanwarta na gane itace ta layin nan." Dayake Zeey batasan sunan Asiya ba sai cewa tai "Ban santa ba, kinsan ni ba rike mutane gareni ba." Nabila ta hau kan titi tana cewa "Ni ma ba magana muke ba, sanda bakya nan dai ina ganinta, itace kamar akace saurayin ta yaci gasar zane kamar ko?" Kamewa a zaune Zeey tai da jin Nabila nan da nan hankalinta ya tafi kan budurwar Baqeer da aka yaura, badai ita bace? In itace ya Baqeer ke cike? Nan danan taji gaba ɗaya ranta ya ɓaci ta dau wayarta tana cewa "Meye handle ɗinta?" Ba tare da dogon nazari ba tace "Cutie_Siya" da sauri ta duba ganin fuskar Asiya duk da ba wani dogon sani ta mata ba yasa bankalinta kara tashi, sam hankalinta ya tafi har Nabila ta gaji da magana tace "Wai menene?" Kallanta Zeey tai tace "Aunty Nabs bana jin yawon nan, plz saukeni kije ke kaɗai." Mamaki ne ya kamata tace "Zeey inje ni kaɗai kamar ya? Bayan mungama planning dake akan tare zamu?" Saman goshinta ta shafa tace "Banajin zuwa plz samu guri kiyi parking na fita." Takaici ne ya kama Nabila, tai parking ga mamakinta mai makon ma Zeey ta maida hankali kan ɓacin ranta gani tai ta fita kawai ta tari adaidaita sahu ta shiga hankalinta a kwance babu alamun ma ta damu. Hannayenta biyu tasa ta shafi fuskarta tana mamakin hali irin na Zeey da sam in tunanin ta yai wani gun bata bi ta kan komai, itama maimokon ta cigaba da tafiyar kawai gida ta koma, tana parkıng motar ta shiga ciki ranta duk ba da ɗi, tana ƙoƙarin yin hanyar dakinta ta hangoshi ya fito sanye da jeans da light brown ɗin riga da alama fita zaiyi dan yana rike da key a hannunsa yana kadawa, idanunsu na haduwa ya fara neman juyawa tai saurin cewa "Kabir in baka zo ba Allah zan ƙira sunanka da ƙarfi Mumy ta fito." Waigowa yai ya kalleta sannan ya tamke fuska sosai ya cigaba da tafiyarsa, har yazo kusa da ita bata matsa ba, yana yin taku biyu gaba da ita yaji ta sa hannu ta zagayo dashi gefen cikinsa, gabanshi ne yai wani irin faduwa hakan yasashi kasa ko motsawa, ya fara sauke numfashi cikin wani yanayi, kanta ta kwantar a bayanshi ta rikeshi sosai tace "My love dan Allah ka barni naji duminka ko na minti talatin ne." Kasa motsi yai saboda wani abu da yake ratsa mai gangar jiki, yawun bakinsa ya hadiya yace "Nabila abinda muke aikatawa ba daidai bane ke fa kanwar Mumy ce wannan wani kwamacala ne?"
"Na sani Kabir shiyasa nake ƙoƙarin jure abinda ke raina, ba zina na nemi mu aikata ba, ban kuma ce sai ka soni dole ba dan Allah nidai ka dinga barina ina rungumarka, duminka na ragemin radadin zuciyata, numfashinka ya ragemin kewa da kaunar ka, a haka inaji a jikina san da nake ma zai ragu." Waigowa yai ya kalleta yace "Taya sona zai ragu a zuciyarki ta haka?" Idanunta ne ya ciciko da kwalla tace "Allah zaiyi dan Allah karka hanani tabaka," ta ƙarasa maganar wani kwalla na gangarowa saman kuncinta, janue jikinshi yai ya fita nan ta bishi da kallo tana share kwallarta, wannan wani irin bala'i ne? Tana san abu amma ace wai bazai yiwu ba? Ita alaka ta dameta ne? Indai za'a barta da Kabir koma menene a faɗa ba damunta zaiyi ba. Waigowar nan da zatai taga Mumy ta nufota, da sauri ta fara share kwalla tana neman daidaita kanta, Mumy kuwa tana ƙara sowa ta sharara mata mari ba tare da ta ce mata komai ba, nan da nan gabanta ya faɗi badai taji abinda tace ba? Da hannu Mumy ta nunata tace "Wallahi ki fita ido na, uban me kike cemai da kika tsare shi kina kwalla? Wai nikam Nabila anya bakida aljanu?" Fuska ta tamke sosai ita ma rai a ɓace tace "Bishiyar kuka ne a kaina, ni ban isa nai abu ba sai kin takuramin? Gaisawa ma kenan bazanyi dashi ba sai a hau zargina?" Baki Mumy ta saki, cike da mamaki da tsoron kalamanta, tana nan a tsaye har ta shiga ɗaki lalai dole tasan abinyi akan Nabila tab!