Sashe 105
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Zeey tana tada mota taga text ɗin Baqeer a hankali ta saki wani murmushi, a yanzu shi kaɗai take son gani, maimakon tayi mishi reply sai ta ajiye wayar ta nufi gidan Dada.
Dada ta dawo daga maƙotansu kenan inda aka yi haihuwa kwanaki yau mai jego tayi arba’in zata koma gidan mijinta shine tazo gidan suka sha hira, tana ganin motar Zeey ta fara murna tana cewa “Lale da Zainabuwa ta.”
Fitowa Zeey tayi tana murmushi tace “Dada ta daga ina haka?”
“Naje makota ne mai jego tayi arba’in baki ga yaron ba yayi ɓulɓul abinshi.”
Murmushi tayi tace “Dada kina son yara.”
“Saura naki ɗan, Allah yasa nayi wa ɗanki wanka ke da Baqeer.”
Ido ta zaro da sauri tace “Dada wani Baqeer ɗin?”
“A’a Zainabuwa kwantar da hankalinki nufina da yaran ki da yaranshi ai ko tsugunawa yayi bazan bashi ke ba yadda kike ɗin nan sai namijin da yafi kowa mutunci zan bawa.”
Dariya Zeey tasa tace “Dada tawa Allah dai ya bar mini ke.”
Ciki suka shiga tana cewa “Mutumin baya nan ma sun fita shi da Salim….” Ganin takalminshi yasa tace “Ashe ma ya dawo, Baqeeru kana ciki ne?”
Shafa addu’ar da yake yayi ya koma kan wheel chair yana cewa “Dada kin dawo?” Yayi maganar yana buɗe ƙofa, idanuwanshi ne suka sauka akan Zee, tana jingine da jikin bangon kusa da ɗakin, wani nutsuwa da farin ciki ne ya sauko mishi ya zuba mata ido yana cewa “Dada ban san kin shigo ba ai.”
Itama murmushin tayi tace “Dada kin kulle ɗaki ne hala?”
Daga ciki tace “Zainabu bari ina zuwa abu zan ɗauko.”
Kallonta yayi yace “Ɗaki yafi dadi ai,” Yayi maganar idanunshi na kanta.
Tana kallonshi itama tace “Bani.”
Ido ya ɗan canza yace “Me?”
“Mark ɗina," hannunshi yasa a aljihu ya ciro biro yazo daf da inda ta miƙo hannun ya fara mata zane, kallonshi kawai take yi tana murmushi, zanen ƙwarangwal yayi mata sama-sama, baki ta buɗe bayan ta kalla a shagwaɓe tace “Wato nice ma ƙwarangwal?”
Biron yasa a gefen kuncinsa yace “Mark kika ce kuma baki ci komai ba.”
Ta turo baki tace “Allah a faɗa mini, please menene.”
Kiyi browsing ki gani, wayarta ta dauka ta rubuta ganin bata gane ba still yasa tace “Wani yare ne?”
“Hmm arabic?”
Nan ta sake rubutawa kurawa wayar ido tayi kawai sannan ta dago tana yi mishi wani kasalalken kallo wanda ya dinga ji komai na jikinshi na sagewa, tace “Wai da duk sorry ne aka dinga wahalar dani? Allah sai na rama an yi 1-0.”
Shima murmushin yayi yace “Anya ba 5-0 aka yi ba?”
Jakar gift ɗin daya saya mata ya kalla yana son ɗaukowa yaji muryar Dada tana cewa “Zainabu share wannan kizo in nuna miki wani abu,”
Kallonshi tayi shima kallonta yayi sannan suka kalli Dada. Me zai gani? Album ne a hanunta da sauri yace “Dada wallahi a’a.”
Dariya tayi tace “Dalla kai dai ka koma ɗakin ka ni hotona zan nuna mata ba wani abun ba.”
Da sauri ya turo kekenshi, itama Zee ta nufo wurin tana dariya tana cewa “To Ya Baqeer ai dai hoton Dada aka ce ba naka ba.”
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Umm Asghar ce*
*Da Ayusher Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA HUƊU*
{64}
Zaman dirshan tayi ta baza hotunan a gabanta tana kallo tana dariya, yawanci hotunan Dada ne tana budurwa sai waɗanda suka ɗauka da mahaifin su Umma lokacin tana amarya. Haka Zeey ta sakata a gaba tana dariyar kwalliyarta harda ƙwalla. Tana cikin kallon hotunan ne taga hoton wani yaro an ɗaukeshi da kwanon fura a gabanshi fuskar nan tayi dagace-dagace da furar kamar wanda ya wanke fuska da furar. Ɗagowa tayi ta kalli Baqeer sai ta ƙara kallon hoton, can dai tace "Dada waye wannan?" Ta ɗaga hoton tana nuna mata. Dariya Dada ta saka kafin tace "Waye kuwa idan ba dunkum ba, kin san fa ci ne dashi yana ƙarami." Kallonshi Zeey tayi sai ta kwashe da dariya har da riƙe ciki tace "Wai Ya Baqeer ka ganka kuwa," hannu ya kai zai ƙwace hoton tayi sauri ta janye hoton tana cigaba da dariya. A gefe ta ajiye hoton ta cigaba da kallon hotunan sai dai duk da haka lokaci bayan lokaci sai ta juya ta kalleshi ta sake kwashewa da dariya. Har suka gama kallon hotunan bata daina dariyar wancan hoton na Baqeer ba, sai da ta tattare wa Dada hotunanta ta ɗaga wancan hoton tace "Dada ina son wannan, kin bani?"
"Baki da dama Zainabu, duk hotunan nan ki rasa wanda zaki ɗauka sai wannan?" A shagwaɓe tace "Ni dai Dada shi nake so ki bani, kin ji?" Dariya tayi tace "Idan ma duka kike so ai zan baki bare wannan ƙwaya ɗaya." Juyawa tayi ta kalli Baqeer tayi mishi gwalo sai kuma tace "Ya Baqeer," shiru yayi ya rabu da ita. Tashi tayi ta koma kusa dashi tace "Ya Baqeer mana, please ka juyo ka kalleni magana zamu yi." Har cikin ɓargonshi sai da Baqeer yaji ƙiran nan da tayi mishi don tayi ƙasa sosai da muryarta sai tayi maganar cikin yanayinta na shagwaɓa abinda yasa yaji wani abu ya tsirga mishi tun daga tsakar kanshi har zuwa tafin ƙafarshi. Kallonta yayi sai yaga itama shi take kallo, hoton dake hannunta ta ɗaga mishi tana dariya ƙasa-ƙasa tace "Ka tuna?" Gira ya ɗaga mata da sigar tambaya sai kuma yace "Me?"
"Wannan hoton ka tuna lokacin da aka ɗauka?" Girgiza kai yayi alamar a'a don anyi hoton lokacin bai fi shekara biyu ba, ba zai iya tuna sanda aka ɗauka ba.
Hannu ya miƙa mata don ta bashi hoton har ta miƙa mishi sai ta tuna ba lallai ne ya dawo mata dashi ba don haka tayi saurin janye hannunta tana dariya tace "Naƙi wayon nasan idan na baka ya tafi kenan ba dawo mini dashi zaka yi ba." Shima dariyar yayi "Da gaske zan baki gani kawai zan yi." Maƙe kafaɗa tayi tace "Ni dai a'a gaskiya."
Ɗan ɓata rai yayi kamar yayi fushi yaƙi magana, kallonshi tayi tace "Wai fushi kayi don nace bazan baka ba? To gashi," yi tayi kamar ta miƙo mishi sai da ya waiwayo yaga wayarta take miƙo mishi. Da mamaki ya kalleta yace " Me zan yi da ita?"
"Oho," tace tana ɗaga kafaɗa, naga kamar kayi fushi ne shine na baka wayata a madadin hoton. Mayar mata da wayar yayi sai kuma yace "Ki ajiye wannan zan baki wani kinga wannan tsohon hoto ne."
"Ni dai shi nake so sai dai idan zaka yarda na ɗauke ka wani a wayata sai na baka wannan." Girgiza kai yayi alamun a'a, cewa tayi "Shikenan ka huta sai ka bar min abuna tunda dama ba kai ka bani ba bare kace sai na dawo maka dashi." Cikin ranta kuwa cewa take yi 'me kike yi haka ne wai Zainab? Kada fa kiyi abinda zai fallasa asirin da kike ɓoyewa cikin zuciyarki'. Shiru suka yi na wasu ƴan mintuna, tashi tayi ta leƙa Dada a ɗaki tace "Zan tafi Dada sai an kwana biyu kuma," tashi tayi ta biyota tana cewa "Bari na taka miki." Koda suka fito daga ɗakin baya tsakar gidan, ƙofar ɗakinsni Zeey ta kalla tana tunanin daga tashinta shine har ya shige ɗaki, kamar zata yi magana sai kuma tayi shiru, daga nan tsakar gidan suka yi sallama da Dada ta fita. Tsayawa tayi turus ganin shi a jikin motarta da gift bag a hannunshi, ƙarasawa tayi wurin tace "Kana nan ashe?"
"Da ina kike tunanin zani?" Shima ya mayar mata da tambayar. Ɗaga kafaɗa tayi irin nima ban sani ba ɗinnan sai kuma tace "Ban sani ba ko ka shiga ɗaki ne." Miƙa mata gift bag ɗin yayi, bata karɓa ba sai cewa tayi "Me zan yi dashi?"
"Karɓa mana, naki ne," hannu tasa ta karɓa sannan ta buɗe gift bag ɗin ta leƙa ciki sai taga kwalin turaren da yake yawan saya mata ne sai kuma fabric ɗin da bata san ko miye ba sai taje gida sannan ta duba ta gani. "Thank you," tace tana ɗan murmushi cikin jin daɗi, matsawa yayi daga jikin motar ya bata wuri ta shige. Har ta tayar da motar zata tafi sai kuma ta leƙo da kanta waje tace "Me yasa kake yawan yi min kyauta Ya Baqeer? Wacece ni a wurinka?" Bata tsaya ta saurari amsar da zai bata ba ta figi motar a guje ta bar wurin don gabanta faɗuwa kawai yake yi saboda kamar wacce aka matsi bakinta ta samu kanta da yi mishi wannan tambayar ba tare data shirya ba shi yasa tayi saurin barin wurin don bata son jin amsar da zata fito daga bakinshi ta zama akasin abinda take fata.