← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 168

Sashe 104

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Badaru ne ya shigo gidan riƙe da kwankwaso don har yanzu bai gama warkewa ba, daidai Fatima zata shiga ɗaki kamar dama jiranta yake yi sai jita yi yace “Ai ba tun yanzu ba nasan dama kin rainani, in banda iskanci kina ganina shine ba zaki gaida ni ba zaki wuce? Fatima na kula fa kin gama rainani a gidan nan wallahi zaki kwashi kayanki ki bar mini gida.” Kallonshi tayi maimakon ta bashi hakuri sai ji yayi tace “Sannu da zuwa,” daga haka ta shige ciki, ƙwafa yayi yace “Munafuka kawai ai an yanka ta tashi yanzu kaf dinku kallon kowa nake yi.”
Abu tana jin haka tayi sum-sum ta shige ɗakinta ta maida ƙofar ta rufe, ya nufi ɗakin Jamila yana cewa “Munafuka kema daga ke har ɗanki kun kusa ku bar mini gidana.” Jamila ta amshi ledar bread dake hannunshi tana sanabe tana cewa “Malam kai dai kada ka wahalar da kanka don Allah kaga dai ba dadi kake ji ba.” Ciki ya shiga yana cewa “Ai ko ba lafiya gareni ba daidai nake dasu dukansu."
Fatima kuwa tana shiga dakin ta saki murmushin jin daɗi tare da yiwa Allah godiya, account dinta da Baqeer ke turo kudi ta kalla, dubu dari ne a ciki don idan ya turo mata ba wani kashewa take yi ba gani take in mutanen gidan suka ga tana kashe kuɗi tabbas zargin ta zasu fara yi, ɗaki ta shiga ta kira Baqeer suka gaisa sannan tayi mishi godiya. Cike
da jin daɗin dake bayyane a fuskarshi yake bata labarin shagon da zai kama, Umma wasu zafafan ƙwalla ne suka zubo saman idanunta albarka kawai take saka mishi tace zata samu tayi miya sosai a aiko musu, nan shima yayi godiya suka yi sallama. Ƙwallar data tarun mata a ido tasa hannu ta share tare da yin hamdallah.
Baqeer ne ya kalli Salim wanda ya saki baki yana kallon jakar gift bag da ya siya yasa abayar nan da turaren nan a  ciki, ɗauke jakar yayi yana ƴan wurƙila ido yana cewa “Ahh lallai abu yayi karfi, ina ce dai ba a ɗinkin mata zamu ƙare ba?”
Wani mugun kallo yayi mishi yace “Ka gama neman maganar ka kayan maza ma nake tunanin maida hankali sosai akai akwai abinda nake son yi.”
Dariya Salim yasa yace “Faɗa mini gaskiya ba dai so kake yi ka dinga yin na maza ba saboda baka son yiwa wasu matan ɗinki inba Zee ba?”
Tsuke fuska yayi yace “A yaushe nace hakan? Sannan Zeey sai dai ka faɗawa saurayinta haka ai ba ni ba.”
Kai ya kau da yana shafar haɓa yana cewa “Adai gama waske-wasken za’a dawo dai inda aka barmu in ma mutum na neman sauƙi gwara ya fito ya faɗi abinda ke ranshi.”
Gyaran murya Baqeer y8ai yace “Yauwa muna magana akan sunan da za’a sa in nayi ɗinki.”
Matsowa Salim yayi yace “Ko zaka yi amfani da MBB ɗin ka don sunan nayi mini daɗi." Kai Baqeer ya girgiza alamar a’a sannan yace “Na gama amfani da sunan har abada, na farko na barwa wanda ya saci sunan shine last gift dana mishi a duniya, na biyu kuma bana son Baba ya gane nine da wannan sunan.”
Cike da fahimta Salim ya jinjina kai yace “Na Baba dai na fahimta amma banga dalilin barwa butulu irin Bello sunanka ba.”
Murmushi kawai Baqeer yayi don bai san me zai ce ba sai can yace “Ya kake ganin Muhammad B?”
Salim yace “Yayi shima amma sai dai mu maida sunan Mohd kaga zai yi tsayi.”
Shiru Baqeer yayi alamun nazari kafin yace “MOHBAQ fa?” Tafi Salim ya fara yace “Perfect yayi sosai dama MBB ma kai kasa da kanka sai naga wannan ma yafi dadi Mohbaq Muhammad Baqeer kenan.”
“To shugaban yan washi bar zuzutawa dai.”
“To ko mu tambayi Zee am sure……”
Jakar hannunshi ya kusa kwada mishi, dariya Salim yasa yana cewa “Ah to wai don ka tabbatar.”
“Kai dai nasan yanzu bakinka ba shiru zai yi ba kana matsawa zaka kira Habi.”
Yanayin fuskar Salim ne ya ɗan canza yace “Nifa kunsa mana ido babu abinda ke tsakanina da ita," kamar tasan abinda ke faruwa kawai sai ga kiran wayarta cikin wayarshi, kallon Baqeer yayi tare da saurin maida wayar aljihu wanda hakan yasa Baqeer cewa “Ya? Ta kira ne? Kuje kusha soyayyar ku ni babu ruwana.” Fita yayi daga shagon da sauri yana cewa “Ba ita bace customer ne.” Kallonshi yayi yana girgiza kai, kallon shagon yayi nan ya fara tura kekensa yana bin girman shagon da kallo don shaguna huɗu suka je gani sai wannan hankalinshi ya fi kwanciya dashi saboda girmanshi yana ganin in za ayi abu gwara ayi shi a wadace.
Aunawa ya dinga yi abubuwan da ya kamata su siya na furnishing ɗin shagon, nutsuwa da kwanciyar hankali ke sake ratsashi, wayarshi ya kalla sai kuma yayi murmushi haka kawai yaji yana son jin ya take, text ya mata yace “Zafa a baki fail a exam ɗin .”
Zeey lokacin tana zaune ɗakin Mummy sun yi shiru gaba ɗaya ta rasa me zata cewa Mummy, ita kam Mummy a kwance akan gado wani matsanancin ciwon kai take ji don gaba ɗaya jiya bata samu bacci ba, senate kuma da safe ya fita saboda wani taro da zai yi attending a Niger State, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kamo hannun Mummy ta riƙe gam cikin sanyin murya take cewa, “Mummy na bashi kwana biyu ya sanarwa Daddy da kanshi, sai dai yanzu an riga an shiga kwana ɗayan farko In Sha Allahu zamu samu mafita, sai dai an cuci Nabila ban san yadda zamu yi da baiwar Allahn nan ba.”
Kai Mummy ta girgiza itama ta ƙara rike hannun Zee tana cewa “Aikin gama ya riga ya gama, sannan in da lefin Kabir ita ma da nata laifin, tsorona Allah tsorona Senate ko Inna wani yaji abinda ke faruwa,” ta ƙarasa maganar cike da damuwa, kallonta ta sake yi tace “Ya aka yi kika sani?”
Wani abu ta haɗiya tace “Ta kirani jiya akan tana da ciki to da farko ban yarda ba amma da nazo na ganta sai na tabbatar, sannan ƙin faɗar wanene da kuma yadda nasan ba yawo take yi ba yasa na fara zargin Ya Kabir, naje wurinshi na bugi cikinshi sai kuma kalamanshi da actions ɗin shi suka tabbatar mini abinda nake zargi, Mummy taya Ya Kabir zai yi mana haka?” Wasu ƙwalla masu zafi ne suka taru a idonta.
Mummy ta rungumeta tace “Babu komai Zeey mubi komai a sannu In Sha Allahu Allah zai kawo mafita.”
Kallonta tayi tace “Allah zai kawo mafita amma bazan bari a cuceta ba kin dai sani, dole ne Daddy yasan abinda ake ciki sannan Inna ma ki sanar da ita ko ni na sanar da ita, babu yadda za ayi tace tana da ciki a bar abu har sai ya girma kafin asan abun yi.” Ajiyar zuciya Mummy tayi don tasan wacece Zeey akan faɗar gaskiya ko da mahaifinta ne sai tayi faɗa sannan in tana da ra’ayin abu babu mai canza mata shi akan wannan dalilin yasa sam bata da ƙawaye don bakinta baya shiru.
Ganin Mummy zata lallaɓata yasa ta fito daga ɗakin ta shiga nata, kallon ɗakin tayi yayi kaca-kaca saboda Nabila bata gyara mata ba, fitowa tayi tasa mai aiki tazo ta gyara mata sannan ta amso abincin Mummy ta kai mata ta koma ta ɗauko na Nabeela ta kai mata, rungume juna kawai suka yi Nabeela na kuka tana shafar bayanta, sun daɗe a haka kafin tace “Ya isa Aunty Nabs In Sha Allahu komai zai tafi daidai.”
Kai ta girgiza tana cewa “Ta yaya? Bayan babu wanda zai fahimceni? Nice da cikin kuma ni aka ƙwacewa virginity? Sannan ni za’a bari da zagi?”
“Kinyi PT ya nuna positive ne?”
Kai ta ɗaga alamar eh kafin tace sau hudu ina yi amma still positive," ido ta ɗan runtse, Nabila ta kalleta tana hawaye tace “Zeey don Allah ki taimakeni tsoro nake ji ke kinsan ni wacece babu yadda za ayi na kula wani inba ta ƙarfi aka nuna mun ba.”
Hannu tasa a saman leɓenta tace “Na sani, ke dai kici abinci ki kwantar da hankalinki.”
Tana kaiwa nan ta fito daga ɗakin, jita yi komai na gidan ma bata so hakan yasa kawai ta shirya ta ɗauki wayarta ta fito ta faɗa mota tayi gaba.

*****
Da mamaki Kamalu yake kallon yaron shagon Baba yace “Kai dan gidanku nida shagon mu zaka hanani shiga?”
Yaron ya sake danne ƙofar ta ciki yace “Don Allah Kamal kar ka janyo mini matsala ka ga Baba saura kaɗan ya koreni don Allah ka bari in yana shagon kazo.”
Buga ƙofar ya fara kamar zai ɓalla ta hakan yasa mutane suka fara kallonshi, ƙwafa yayi ya juya yana masifa "yaron nan wallahi sai na tareshi a lungu nayi mishi dukan tsiya, sai ya san ni ya wulaƙanta ɗan banza ɓarawo kawai, ai kaine kake sata tunda ni kayan ubana gadona nake ci."
Aljihunshi ya laluba yaga babu komai, ajiyar zuciya yayi ya hango wani mai babur wanda yake sak irin nashi, da gudu ya nufi mai babur ɗin dake cikin hold up, yana zuwa yace “Bawan Allah ɗan zo nan don Allah tambayarka zan yi.”
Me babur ya zabga mishi wani kallon banza yace “Sauri nake yi.” Ya fara tuƙin shi, gudu Kamalu yasa yana bin babur ɗin sai dai duk yanda yake zabga gudu bai cimma shi ba haka ya dinga haki yana sauke ajiyar zuciya, haka ya ƙarasa gida da ƙafa saboda babu kuɗi a hannunshi ya gaji ya galabaita sosai ga wata azababiyar yunwa dake ƙara kamashi.
Chapter 104 · 0% Book details