← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 168

Sashe 90

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau tun safe ta tashi da aikin taliya da aka kawo mata daga nan maƙwabtansu za'a yi musu ta gara, da yake tun bayan data sayawa Hadiza injin markaɗe da kuɗin kujerunta data sayar sauran ƙudin daya rafe sai ta sake sayen injin taliya ta koma kan sana'arta tunda dama ana ta zuwa nema. Yanzu ta ɗauke hankalinta daga kan mutanen gidan data lura babu abinda suke so da gani irin kasawarta ita da ƴaƴanta. Tana kallon Jamila dake girkin ranar sai kaiwa da kawowa take yi kamar me neman wani abu ita dai ko ɗaga kai bata yi ta kalleta ba, da fai ta lura ba kulata Umma zata yi ba sai ta matso kusa da ita cikin murya ƙasa-ƙasa kamar wacce bata so aji me zata ce tace mata "kin san nan Mallam yazo yana faɗa akan ana yi mishi sata ko?" Bata jira Umma ta amsa ba ta cigaba da cewa "to ashe dai Kamalu ne yake zuwa yana kwashe mishi kayan shago yana kawowa uwar ta ɓoye wai kayan lefe yake tarawa aure zai yi, ko wane sakarkarun iyayen ne zasu ɗauki ƴa su bashi bayan sun san ba nutsuwa gareshi ba, ai dai zamu sha kallo duk ranar da Mallam yasan su suke ɗaukar mishi kaya." Kallonta kawai Umma tayi ta mayar da kai akan aikin taliyarta don ita dama ba shiga irin waɗannan gulmace-gulmacen nasu take yi ba shi yasa suke jin haushinta don duk yadda ka kai da iya tsegumi bata taɓa tofa nata a ciki sai dai ta bisu da Allah ya kyauta kawai.
Wucewa Jamila tayi tana cewa "Ai ke matsalarki kenan, babu dama a kawo miki ƴar magana ana so a ɗan tattauna dake sai kiyi wani girim kamar ba kya magana." Murmushi kawai tayi ta cigaba da aikinta, Jamila kenan. Ita yanzu har ta manta da yadda suke haɗe mata kai ita da Abu kowaccen su sai ta ɗauko gulmar ƴar uwarta ta rasa da wanda zata yi sannan suke sanin da zamanta, ko ance musu mahaukaciya ce ita da zata biye musu bayan tasan irin zaman da suke yi da ita.
Tana gama aikinta ta tattare wurin ta gyara sannan tayi shigewarta ɗaki ta bar Jamila a wurin ta bita da harara, tana jin takaicin yadda Fatima ke yi musu sam bata shiga sabgar su duk abinda zasu yi mata bata magana sai in sun ƙureta sannan take maida martani ɗaya-biyu tayi shigewarta ɗaki ta barsu ta ciwon zuciya.

*****
Tunda Bello ya tafi Germany ta saka ƴan kuɗaɗen daya bar mata a gaba tana sayi banza sayj wofi ko abincin da Habi take girka musu bata ci sai dai tayi order a kawo mata Habi ta fita ta karɓo, babu abinda take yi daga kwanciya sai kwanciya sai dai tayi wanka taci gayu ta naɗe akan kujera tana yawo akan social media, ita ce ig ita ce tiktok don whatsapp ma ba sosai take hawa ba sai idan zasu yi video call da Bello. Duk wani aikin gidan Habi ce ke yi dama can Asiya malalaciya ce bata son moruwa sam shi yasa ta sakarwa Habi aikin gidan nata gaba ɗaya duk da ba wani aikin kuzo mu gani bane tunda ba yaran da zasu ɓata wuri gareta ba. Idan Habi taga yadda take kashe kuɗi tayi magana sai ta rufeta da faɗa tace tana yi mata baƙin ciki don daga Allah ya ɗagata ta samu rayuwar hutu shine sai ta nuna ƙyashi da hassadarta to ta dai kusa tafiya ma ta bar mata ƙasar idan ta daina ganinta sai kuma taga da wanda zata yi, don haka Habi ta daina yi mata magana duk abinda tayi sai ta kawo idanu ta zuba mata.

*****
A yanzu Baqeer ya samu nutsuwa ya samu kwanciyar hankali, har wata ƴar ƙiba yayi sanoda kwanciyar hankalin daya samu. Baya da matsalar komai saboda dai Alhamdulillah yana samun kuɗi da contract ɗin da yayi signing gashi kuma kamar kada yayi signing contract ɗin sai mutane suke ta nemanshi da son yayi musu designing ɗinkuna, ga mahaifiyarshi da yake yiwa aiken kuɗi akai-akai haka ƴan uwanshi ya cigaba da taimakonsu kamar da tun ma ba Hadiza ba da dama shine yake ɗauke da nauyin gidanta. Anan ɗin ma ya wadata Dada da dukkanin abun buƙata don baya jira sai ƴaƴanta sun kawo mata duk abinda yasa zata buƙata yana ƙoƙarin ganin ya ajiye mata, tun daga kan kayan abinci, kayan masarufi, fruits ne da duk dai wasu abubuwa da ya kamata, gashi lokaci zuwa lokaci yake turawa Umma kuɗi tayi mata miya ta bawa Salim ya kawo mata duk don ya rage mata ɗawainiyar da take yi dasu. Sosai yake tausaya mata ganin girma ya kamata gashi kuma komai na hidimar gidanta ita take yi ba mataimaki gareta ba sai yaran maƙwabta idan sun shigo waɗanda baka raba gidanta dasu. Har ɗan ƙaramin gas ya saya mata duk don ya sauƙaƙa mata ya rabata da hura wuta da itace. Kullum kuwa ta buɗi baki albarka take saka mishi tana addu'ar Allah ya yalwata arziƙinshi yasa albarka a cikin nemanshi ganin yayi mata abinda ƴaƴan data haifa basu yi mata ba.
Yau yini yayi yana sketches daya gaji ne ya fito waje don yasha iska. Leƙawa yayi ɗakin Dada zai ce mata ya fita don kada tazo tana nemanshi bata ganshi ba sai ya ganta a zaune akan sallaya ta jingina da bango tana gyangyaɗi. "Dada" ya kira sunanta bata s bs da ya ɗan ɗaga murya ya ƙara kiranta sannan ta buɗe ido tace "na'am Baqeeru, wani abu kake so?" tana gyara zamanta. "Fita dama zan yi nace kada kizo kina nemana sai na tarar kina bacci, ai gara ki kwanta kada jikinki yayi ciwo kina bacci daga zaune". Girgiza kai tayi tace "ai yanzu na zan tashi na ɗora girki da yake ma ba wani aiki bane mai wahala tunda ka sayo wancan abun shi yasa ma har ka iskeni ina bacci, sai dai ka tsaya ka kunna mini murhun kafin ka fita kasan har yanzu ba sanin yadda zan kunna nayi ba".
Ƴar dariya yayi yace "Ke dai kawai kice tsoro kike ji kada ki ƙone shi yasa ba kya iya kunnawa da kanki bayan na nuna miki yadda ake yi ba wani wahala ne da kunnawar ba." Tashi tayi ta bishi a baya tana cewa "naji ɗin ni dai kada ka fita baka kunna mini ba." Sai da ya kunna mata gas ɗin ya nuna mata yadda zata yi ta kashe idan ta gama koda zai daɗe bai dawo ba kafin lokacin sannan yayi mata sallama ya fita. A ƙofar gida ya haɗu da Tanimu zai shiga gidan hannunshi riƙe da babbar leda. Yana ganinshi yace "kai kuma daga ina? Duk yau ban ganka ba saboda babu zuwa makaranta ko." Dariya Tanimun yayi yana sosa kai alamun jin kunya don duk yau bai leƙo Baqeer ɗin ba yace "Wallahi yau a shagon su Nuhu na yini ina tayasu aiki shine ma na karɓo wasu kaya nake so ka yanka mini sai naje na haɗa." Juya keken yayi suka koma cikin gidan yana cewa "ya kamata dai ka dage ka koyi yankan nan da kanka gashi kana son hawa keke amma ka kasa mayar da hankali ka tsaya ka koyi yanka sosai."
Dada na ganin shigowarshi tace "Har ka dawo ko fasa fitar kayi?" Tsayawa yayi ya mata bayanin abinda ya shigo dashi sannan suka shiga ɗakinshi. Karɓar kayan yayi Tanimu yayi mishi bayanin abinda yake so yayi, da taimakon shi Tanimu ya yanka kayan don yace ba zai yanka mishi ba sai dai ya nuna mishi yadda zai yi tunda dukkansu koyo suke yi idan bai tsaya ya iya tun yanzu ba sai yaushe zai iya. Yana kallon yadda Tanimu yake yankan yana tunanin ya kamata ya sayi kekuna ko guda biyu ne ɗaya manual ɗaya na wuta su gyara shagon ƙofar gida su zuba su fara aikin anan kafin ya samu ya buɗe babban shago yadda yake da buri, don wuri babba yake so ya buɗe inda zasu dinga ɗinki har da ready made ba wai sai mutum ya kawo kayanshi ba to amma yasan irin wannan wurin sai a hankali zai buɗu ba wai lokaci ɗaya zai cimma wannan manufar ba shi yasa yake so su fara da ƙaramin shagon a gefe guda kuma yana cigaba da sayar da sketches ɗin shi ga kuma contract ɗin da yayi signing ana biyanshi albashi duk wata banda kuɗin da suke biyanshi duk lokacin da yayi musu designing kaya, yasan a hankali da abinda yake samu cikin lokaci ƙanƙani zai buɗe babban shagon kamar yadda yake buri amma yafi so ya fara da ƙaramin wurin hannunshi ya goge a ɗinkin kafin ya buɗe wancan ɗin.
Chapter 90 · 0% Book details