Sashe 16
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cak ta tsaya sannan ta waigo tare da sake takowa inda yake, wani wulaƙantaccen kallo ta watsa mishi tayi tsaki "Kai nan a tunaninka zan iya cigaba da yin soyayya da kai, a hakan? Kalle ka fa ka kalleni kai ma kasan ajina yafi gaban na zama matar gurgu, never wallahi har abada" Ta ƙarasa maganar tare da tofar da yawu kamar taga wani abun ƙyama. Juyawa tayi ta fara tafiya sai kuma ta juyo ta kalleshi irin kallon tsaf ɗinnan kafin tace "Ina fata zaka cireni daga cikin ranka ka manta ka taɓa sanin wata mace mai suna Asiya, ka ɗauka duk soyayyar da muka yi a cikin mafarki ta gudana ba gaske bane don ni tuni na cireka daga cikin zuciyata daga lokacin da nasan ka zama nakasashe gurgu nasa a raina ban taɓa saninka ba don haka nake haɗa ka da Allah kada ka ƙara nemana ko a waya ko kace zaka zo gidanmu don idan kazo ma bazan fito ba." Daga haka ta juya tayi tafiyarta ta barshi yana ƙwala ƙiran sunanta yana cewa "Please Asiya kada kiyi mini haka, kada ki juya mini baya don kinga larura da ta sameni, idan kika barni a cikin wannan halin dana tsinci rayuwata ban san inda zan waiwaya ba naji daɗi kuma."
Ko waiwayowa bata yi ba har ta ƙurewa ganinshi kuwa, haka ya sunkuyar da kai yana zubar da hawaye mai ciwo yana jin wai yau shi Baqeer, Asiya take faɗawa waɗannan maganganun saboda taga yadda Allah yayi dashi, har Salim ya dawo kanshi yana ƙasa ya kasa ɗagowa, sai da ya dafa kafaɗarshi sannan yasan ya dawo don dama matsawa yayi ya basu wuri. Salim gani yayi fuskar Baqeer tayi jawur gashi tayi caɓa-caɓa da hawaye.
"Lafiya kuwa Baqeer? Wani abu Asiyan tace maka naga duk ka firgice ka fita daga hayyacinka?"
Girgiza kai kawai yayi don bai ji zai iya buɗe baki yayi magana a daidai wannan lokacin ba, maganganun da Asiya ta yaɓa mishi sosai suka dakeshi duka bana wasa ba don ko kusa bai taɓa tsammanin tana daga cikin butaulallun mutane ba masu saurin manta alheri, bai ɗauka a cikin ɗan taƙaitaccen lokaci Asiya zata juyawa soyayyarshi baya ba sai kuma gashi ta ƙaryata tunaninahi ta nuna mishi rashin amana irin na mutanen wannan lokacin.
*****
A kwance Habi ta shigo ta tarar da ita akan katifarsu tana danne-danne a cikin waya. Kallon tsaf tayi mata taga babu abinda ya dameta da abunda tayi sai ma wani ɗan murmushi da take saki idanunta manne da allon wayar. Ninke hijabin ɗin data fita dashi tayi ta ajiye akan jakar kayanta kafin ta zauna daga bakin katifar wajen ƙafafun Asiya zuciyarta duk babu daɗi. "Ke kuwa Asiya me yasa zaki yi haka saboda Allah, ko ba kya son Baqeer bai kamata kiyi mishi irin wannan cin fuskar ba babu tausayin halin daya samu kanshi a ciki a haka ya taso don ya ganki yana ganin ko da ya rasa komai a rayuwa kasancewarshi tare dake zai sauƙaƙa mishi abubuwa ashe ke ɗin mayaudariya ce mai saka alkhairi da sharri, me manta girman soyayya da sanin darajar masoyi."
A harzuƙe ta tashi zaune tayi wurgi da wayar can gefe ta hau nuna Habi da yatsa tana cewa "Kinga Habi ki kiyaye ni ki fita daga idona na rufe, akan gurgun kike cewa na manta alkhairi, gurgun? To idan na aureshi bara zai yi ya ciyar dani ko kuwa ni zan turashi a keken guragun mu tafi yawon barar, wallahi nafi karfin auren nakasashe Allah ya tsareni da auren wahala, to me na sama yaci bare ya bawa na ƙasa? Idan ban rabu dashi tun yanzu ba sai yaushe? Ko kin fiso nayi ta bashi false hope ina yaudararshi alhalin ba aurenshi zan yi ba? To ni ba haka nake ba tun farko da nasan gurguncewa zai yi ma bazan fara kula shi ba bare har ki samu bakin faɗa mini baƙar magana, aikin banza kawai bayan ko kece babu yadda za ayi ki yarda ki aureshi shine ni zaki cikani da baƙin munafurci da iyayi har da wani wai abinda nayi ban kyauta ba, mtsew" Ta ɗauki wayarta ta koma ta kwanta tana cigaba da chatting ɗin da take yi kafin shigowar Habi tayi mata ruining mood ɗin ta.
Murmushin takaici Habi tayi tace "Gaskiya ce ba kya so ni kuma bazan daina faɗa miki ba idan kin so ki ɗauka kiyi aiki da ita idan kin so kiyi watsi da ita kamar yadda kike yi da duk wata gaskiya da zan faɗa miki, kada dai ki manta ramin ƙarya ƙurarre ne kuma ƙarya fure take yi bata ƴaƴa kuma duk wanda ya hau motar kwaɗayi zata sauke shi a tashar dana sani, ni sai yanzu ma na fahimci tun asali dama ba son Baqeer ɗin kike yi ba hidimar da yake yi miki kike kwaɗayi yanzu daya rasa duk wata dama tashi shine kike nema ki guje shi."
"An guje shi ɗin, idan kin ji haushi ke ki aureshi mana, ha'an kin fa isheni Habi wallahi ki fita idona in rufe, tom," tayi wata irin ƙwafa alamun dai ranta ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, daga baya ma tashi tayi ta fice ta bar mata ɗakin.
Bin bayanta Habi tayi da kallo tana jin takaicin halin ƴar uwarta tana jiye mata aikin dana sani don tasan komai daren daɗewa sai tayi dana sanin yaudarar da ta yiwa Baqeer ta gujeshi kawai don Allah ya jarabce shi da larura. Asiya ta gyara kwanciyarta dan dole ta yakice komai a ranta, duk da a can kasan ranta tana tausayinsa sannan tasan bata kyautamai ba, sai dak hakan shine daidai dan tabbas a yanda tasan Baqeer na santa in har tamai lagwa-lagwa to fa bazai taɓa rabuwa da ita ba, ita kuma a yanzu tasan wutsiyar rakumi tayi nesa da ƙasa shiyasa bama tasan abinda zai ja rabuwarsu ta ɗau lokaci gwara yaji zafin kalamanta ya kyaleta.
*****
Suna tafe shiru babu mai iya cewa ɗan uwanshi komai, shi dai Salim tausayin Baqeer ne fal a ranshi don lokacin da yaga budurwar nan tana magana ya taho ya ɗauka wani abin ne, ganin sun ja mota sun tafi yasa yai kamar zai koma cikin shagon, sai yaji kalaman Baqeer wanda ya sashi tsayawa gefe hakan yasa yaji duk abinda Asiya take cewa, sosai ya cika da tsoron Allah yana mamakin halin mutanen yau. A yadda yasan soyayyar Baqeer da Asiya bai taɓa zaton zata guje shi cikin lokaci ƙanƙani ba don kawai Allah ya jarabce shi da wata larurar da bashi ya ɗorawa kanshi ba. Suna tafe yana tura Baqeer a keken guragun shi sai dai ya kasa ce mishi komai don yana jin yadda yake sauke ajiyar zuciya akai-akai, fatanshi Allah yasa kada ya ɗauki damuwar Asiya ya ɗora a ranshi alhalin dama ba wai ya warware daga damuwar ƙaddarar da ta sameshi bane.
Har suka ƙarasa gidansu Baqeer babu mai magana, dama dai tunda abun nan ya faru Baqeer bai cika yawan magana ba idan ba ya zame mishi dole ba, Salim ɗin ne mai yawan maganar ko ba zai amsa ba yasan yana jin shi to shima yau damuwar abinda Asiya ta yiwa abokin nashi ta hanashi sukuni. A ƙofar gida suka tarar da Baba dake ta faman kaiwa yana kawowa tunda ya dawo gida ya tambayi ina Baqeer Umma tace mishi baya nan sun fita da Salim sai dai bai faɗa mata inda zasu je ba hankalin shi ya tashi, sam baya so mutanen unguwa su san halin da Baqeer ɗin ya samu kanshi a ciki don a ganinshi kamar zai zama abin zunɗe da dariya ganin yadda ya ɗaukake shi a cikin dukkanin ƴaƴan shi ya fifitashi ya fifita uwarshi akan baiwar zanen da kowa yake ganin ɓata lokacin shi yake yi akai don basu ɗauke shi wani sana'ar kirki ba kamar yadda shi ya ɗauka, har nasiha an sha zuwa har gida ayi mishi akan bai kamata yake fifita Baqeer ɗin da ƴan uwan shi ba sai yace ai dole ya fifita Baqeer don kuwa shi ɗin ɗa ɗaya ne tamkar da ɗa goma, shine zai share mishi hawaye ya cika mishi daɗaɗɗen burinshi na rayuwa suma idan suna so ya gatantasu kamar Baqeer suje su koyi yadda ake zane zasu ga yadda zai ji dasu ya ɗaukaka su a cikin ƴaƴa. A duk sanda ya faɗi haka kallan mara tunani mutane ke mai, zane fa? Ya rasa abinda zaiyi alfahari dashi sai zane? Dan mu kasarmu sam bamu ɗau ki zane da sunan sana'a ko abin alfahari da mutum zaiyi dashi ba.
Wani wulaƙantaccen kallo ya watsawa Salim daya durƙusa yana gaishe shi, bai amsa ba sai masifa daya balbaleshi da ita akan don me yazo ya fita da Baqeer yawo, wato gurgunta shin da yayi bai isa ba shine yake zuwa har gida yana fita dashi salan wani abun ya ƙara samun shi. Shi dai haƙuri kawai yake bashi don idan da sabo yaci ace ya saba da halin Baban abokin nashi, shi Baqeer ɗin ne yake bashi tausayi shi yasa baya kula duk wani baƙin hali na Baban yake zuwa yana taimakawa Baqeer ɗin da wasu abubuwan amma in banda haka ai da tuni yayi zuciya ya fita daga rayuwar ɗan shi tunda dai dashi ne baya son ganin shi.
Shi ya tura wheelchair ɗin zuwa cikin gida yana ƙwalawa Umma ƙira tun daga soro. Tuni su Abu da Jamila suka fito daga ɗakunansu tun ma kafin Umman ta fito don son jin gulma sun san tunda ya shigo da hayaniyar nan tabbas tijara zai yi mata. A nutse ta fito daga ɗakin duk kuwa da yadda gabanta yake faɗuwa tunda taji mahaukacin kiran da yake ƙwala mata. Daga bakin ƙofar ɗakinta ta tsaya tace "Gani Mallam, barka da shigowa."