← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 168

Sashe 5

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Motsi yaji yatsun nashi sun ƙara yi sai kuma idanunshi dake fafarniya alamun son ya buɗe su sai dai ya kasa saboda nauyi da yaji kanshi yayi mishi. Acan nesa yake jin ƙiran da mahaifin nashi yake yi mishi sai dai ya kasa tantance muryar waye yake ji, ƙoƙarin motsa ƙafafun shi yayi sai yaji ya kasa gashi dukkanin jikinshi yayi mishi nauyi tamkar wanda aka saka igiya aka ɗaɗɗaure shi kyakkyawan ɗauri irin wanda ake yiwa huhun goro.
"Baqeer kana jina kuwa? Daure ka buɗe idanunka ka kalleni nine nan mahaifinka ko na samu nutsuwa nasan cewa wani mummunan abu bai sameka ba" Baban yayi magana muryarshi na rawa don hankalin shi sam ba'a kwance yake ba, fatanshi a yanzu kawai yaga Baqeer ɗin ya miƙe ya samu tabbacin cewa babu wani abu da ya samu ɗan nashi da ya ɗauki dukkanin wani burinshi na rayuwa ya ɗora a kanshi.

Kamar mai koyon yadda ake buɗe idon haka ya buɗesu a hankali yana jin kanshi yana sara mishi da matsanancin ciwo, hannunshi na dama ya ɗaga da niyyar dafe kan ko ya samu raɗaɗin da yake yi mishi ya ragu sai dai yaji shi a ɗaɗɗaure ko motsa shi ya kasa yi, a hankali ya juyar da kanshi ya kalli hannun sai ya ganshi a naɗe a cikin cast alamun anyi mishi aiki a hannun shi yasa ya kasa motsa shi abinda yasa shi wurga idanu yana ƙarewa ɗakin da yake kallo yana tabbatar da akan gadon asibiti yake, juyawa yayi ɗaya ɓangaren ya kalli hannunshi na hagu yaga babu abinda ya sameshi sai ya ɗaga hannun ya dafe kan nashi daya matsanta mishi da azabar ciwo.
"Sannu Baqeer" Baba dake tsaye a kanshi yana kallon duk abinda yake yi ya faɗa. A hankali ya ɗaga mishi kai alamun amsawa don baya jin zai iya buɗe baki yayi magana.
"Ciwo kan yake yi maka?" Baban ya tambayeshi ganin tunda ya farfaɗo yake riƙe da kan abinda ke alamta matsanancin ciwon da yake yi mishi.

Ƙara ɗaga mishi kan yayi don ko ƙwaƙƙwaran motsi baya son yayi idan ba ya zame mishi dole ba. "Bayan kan sai ina kuma yake yi maka ciwo?" Ya ƙara tambayarshi ba tare daya lura da yanayinshi ba da sam baya son yawan magana, shi dai burinshi ya tabbatar babu wani mummunan ciwo a jikin Baqeer ɗin ko ya samu a sallamesu da wuri ya koma gida ya fara shirin tafiya gasar da zai je. Da ido yayi mishi nuni da hannunshi mai karayar da shima ya matsanta mishi da ciwo.

"Sannu, Allah ya baka lafiya" yace tare da komawa kan kujerar dake gaban gadon ya zauna. Ji yayi gaba ɗaya ya takura da kwanciyar don sam bata yi mishi daɗi, ƙoƙari yayi ya gyara kafafuwan shi ko yaji daɗin kwanciyar sai yaji ya kasa motsa su, yayi-yayi ya motsa kafar yaji ya kasa, a hankali ya ɗaga kanshi ya kalli ƙafafun nashi sai yaga ƙafar shi ta hagu a ɗaure take alamun akwai ciwo a jikinta itama sai dai kuma sam baya jin tana yi mishi ciwo kamar yadda hannunshi ya matsanta mishi da ciwo. Cikin dauriya ya sake ƙoƙarin motsa ƙafar sai yaji ai kwata-kwata ma baya jinta tamkar ba'a jikinshi suke ba don sam baya jin wani feeling a ƙafafuwan nashi.

Gabanshi ne ya faɗi saboda yadda ya kasa motsa ƙafafun alhali gasu nan a jikin shi yana kallon su. Cikin rawar muryar data shaƙe saboda daɗewar da yayi bai yi magana ba yace "Baba wani abu ya samu ƙafafuna ne? Gaba ɗaya bana jin su na kasa motsa koda ɗan yatsana ne sai nake ji tamkar ba a jikina suke ba".
Tasowa Baban yayi a ruɗe yace "kamar yaya baka jin su tamkar ba'a jikinka suke ba? Kada dai kace mini wani iftila'in ne yake neman faɗo mata bayan na karayar daka samu a hannunka hannun ma na dama wanda dashi kake amfani kana yin zane dasu". A gigice ya fice daga ɗakin ba tare daya ƙara kallon Baqeer ba dake kwance cikin tashin hankali don sosai ya tsorata da yadda Baban yayi magana. "Likita, likita" ya hau ƙwala kiran likita tamkar dai ya manta cewa a cikin asibiti yake kuma marasa lafiya ne a kwance a wajen da basa buƙatar wata hayaniya bare tashin hankali, har ya ƙarasa nurses station bai bar ƙwala kiran likita ba.

"Babu likita ne a kusa, don Allah kuzo ku duba mini yarona ya kasa motsa ƙafafun shi," yayi maganar a ruɗe abinda yasa nurse ɗin da tayi niyyar balbaleshi da masifa saboda hayaniyar da yake yi musu ta fasa don ta lura kamar ma ba'a cikin hayyacin shi yake ba. "Muje na gani" tace tana yin gaba ya bita a baya har suka ƙarasa ɗakin da Baqeer ɗin yake kwance. Har gaban gadon ta ƙarasa kafin tace "sannu ko, ina ne yake yi maka ciwo yanzun?"

Da hannu ya nuna mata kan shi sai kuma hannunshi mai karayar. "Ƙafar fa ko ita bata yi maka ciwon?" Ta ƙara tambayar shi. A hankali yace mata "Na kasa motsa kafafun nawa duka biyun kuma bana jin feeling ko kaɗan tamkar ba a jikina suke ba har mai ciwon, hatta ƴan yatsun kafata na kasa motsasu." Hannu tasa ta dafa shi tace "Yanzu fa? Ka ji saukar hannuna akan kafar taka?" Girgiza kai yayi alamun a'a. Da ɗan karfi ta matsa kafar ta ƙara tambayarshi "Yanzu fa?" nan ma yace mata bai ji komai ba.

"Ina fata dai ba wata matsalar bace ko nurse?" Baban yace gabaki ɗaya hankalinshi ya kai ƙololuwa wajen tashi don bai san ta yadda zai ƙarbi wannan ƙaddarar dake tunkaro rayuwarsu ta ƙarfin tsiya ba. Ɗan girgiza kanta tayi tace "A gaskiya dai bana ce ba amma bari naje na sanar da Dr duk abinda kenan zai sanar da kai, sannu Allah ya baka lafiya, ta cewa Baqeer sannan ta juya ta fita daga ɗakin cikin tausayawa yanayin da Baqeer ɗin ya tsinci kanshi a ciki. Bata jima da fita ba likitan ya shigo shima, a zabure Baba ya miƙe yace "Yauwa likita don Allah zo ka duba mini yaron nan yace baya jin ƙafafun shi tamkar ba'a jikinshi suke ba kuma ya kasa motsa su,"?yayi maganar cikin raunanniyar murya tamkar ya fashe da kuka.

Ƙarasawa yayi gaban gadon yace mishi sannu sannan ya hau taɓa ƙafarshi mai lafiyar yana jujjuyata tare da tambayar Baqeer ko yana jin feelings ɗin a yanzu yana girgiza kai alamun a'a. Ya jima yanavmatsa ƙafar yana jujjuyata waje-waje amma Baqeer yace shi baya jin komai. Juyawa yayi ya kalli Baba yace "Dole sai anyi mishi CT scan da MRI kafin mu faɗi wani abu akan rashin iya motsa ƙafafuwan nashi dama rashin jin alamun ƙafafun a jikin shi gaba ɗaya, In Sha Allah ba wani abun damuwa bane sai dai idan an yin zamu tabbatar daga inda matsalar take."

"To likita nagode" Baba yace wata irin zufar tashin hankali tana yanko mishi don a yanzu tunaninshi yafi karkata ga yawan kuɗaɗen da za'a kashe don ya tabbata wannan ƙaddarar data afko musu sai ta lashe maƙudan kuɗi kafin a samu akai gaci gashi kwanakin tafiyar su Baqeer ɗin sai matsowa suke yi shi yana kwance a gadon asibiti babu alamun zai warke bare har ya iya taɓuka wani abun arziƙi.

#Baqeer
#Shalele
#Asiya
# RayuwadaKaddara
#Hawayena
#UMMASGHAR
#AYUSHERMUHD

Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻

0020428430 Ishaq Fatima A GTBank
Ki tura shaida ta +234 809 845 6130

KATIN MTN Ta👇
07043079282

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

BAQEER
     NA

UMM ASGHAR
DA

AYUSHER MUHD

RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HUƊU

KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O?
INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?"
KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI  - MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS - MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA - GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO - MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB - MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA - MATSI
MAGANIN NI'IMA - MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU.....Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

08142800199
07068558096

4
Chapter 5 · 0% Book details