← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 168

Sashe 12

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****
Suna zaune a tsakar gida, Abu dake sana’ar maganin mata tanata dafa tsumin ta a gefe, tana zaune akan kujera irin ƴar tsugunno ɗin nan, ita kuma Jamila tana gefe tana tsince shinkafar da zata yi girkin rana dashi dan yau itace da girki, suna yi suna gulma da habaicin Fatima wacce ke zaune a cikin ɗakin ta tasa carbi a gaba tana addu’a, ita dai kawai addu’a take Allah ya sassauta musu, ta sani jarabawa ce daga Allah sai dai tana fatan Allah ya basu ikon cinye jarabawar.
Kamar daga sama taji muryar Abu tana tafa hannu tana salati, Jamila hankali a tashe ta riƙe haɓa tace “Yau me zan gani? Duwawo ya mutu ya bar zani? Baqeeru? Ya ka fita da ƴan ƙafafunka zaka dawo mana a kujerar guragu? Yau ni naga abinda zai kasheni? Wai abin nan dai da gaske ne ashe?”
Abu ce ta ɗaura da salati tana ajiye ludayin da take tuka tsumin dashi tana cewa “Baqeeru? Wannan wani ibtila’in ne ya samemu?”
Baba ne ya kauda kai yace “Ku shiga dashi ɗakin shi.” Salim dake tura keken ne ya cigaba da turawa suna shiga Fatima ta taho da gudu ta zubawa Baqeer ido wanda ke zaune akan kujera kai baka ce yana magana ba, kallon komai na wurin kawai yake yi, idanunshi ne suka sauka gun Umma dake jikin ƙofa tana ganin yadda aka dawo dashi gida bayan bai ko gama warkewa ba.
“To sannunku ku fita.” Baba yayi maganar yana kallon Salim, fita yayi jiki a sanyaye, Fatima tana ƙoƙarin shiga ɗakin Baba ya ɗaga mata hannu sannan ya maida ƙofar ɗakin ya rufe, cak ta tsaya a bakin ƙofar cikin tashin hankali dan ita kam tasan ba ƙalau ba.
Baba ne ya maida idanunshi kan Baqeer wanda ke zaune akan kujera, turashi Baba yayi zuwa gaban table ɗin da yake zane, da mamaki Baqeer ke kallonshi, Baba ya cire takardar kai yasa sabuwa, ya saitashi yadda ya kamata, pencil ɗin da yake amfani dasu ya ɗauko ya miƙa mishi yace “Bismillah!”
Daga waje kuwa Abu ce ta kalli Fatima tace “Me kike yi a tsaye a bakin ƙofar ki shiga mana?”
Fatima ta kalli ƙofar ba dai abinda take tunani bane yake faruwa a ciki? Nan da nan zuciyarta ta shiga bugawa, ya zata yi? Ga tsoron Malam take balle ta kwankwasa ƙofar ɗakin.
Jamila ce tace “Ba dai yaron da aka kawo daga asibiti bane za’a sashi aikin da aka saba?”
Abu ta sake tafa hanu tace “Ai shine ma, yo dama daga sun shiga ɗaki sun kulle ai kowa yasan kwanan zancen.”
Nan da nan Fatima ta ƙara jin hankalinta ya tashi, Baqeer ne yasa hannun hagu yana neman amsa, a fusace Baba yace “Dama zaka saka, ko ka taɓa yin zane da hannun hagu ne?”
Baqeer ya kai hannun damanshi sai dai yana kaiwa ya amshi pencil ɗin yaji yatsun hanunshi sun kasa riƙewa sai jin pencil ɗin kike a ƙasa, Baba rai a ɓace ya tsuguna ya ɗauko ya sa hannu a saman kafadarshi yace “Ka manta kai wanene a gareni Baqeer? Ka manta abubuwan dana sadaukar saboda kai? Ko kuwa ka manta duk wani burina a duniyar nan akanka yake? Naji ka rasa ƙafa zan iya hakura da hakan amma banda hannu, dole ka cikamin burin nan nawa, kai kaɗai ne wanda nake ganin abinda ban yishi ba zaka yi mini shi, kafi kowa sanin hakan, saboda kai har mantawa nake yi ina da wasu ƴaƴan, saboda kai mahaifiyarka ta samu girma da daraja a gurina, idan har ba so kake yi duk abubuwan nan su ruguje ba ka ɗaga hannu kayi abinda na saka ka, dan har yanzu mutane nayi mini kallon shashasha saboda na dage akan zanen da kake yi ina nuna musu shima sana’a ce ana ganin rashin sanin ciwo kai na da nuna ban san me ke faruwa ba, na dage har kazo ka kai wannan matsayin da zaka wakilci garin mu sannan muna sa ran ka wakilci ƙasa shine zaka ce wai karaya ta hanaka amfani da hannu? Kai har ka isa ma?
Baqeer hannunshi na rawa idanunshi sun cika taf da kwalla ya kai hannu cike da dauriya wanda bai taɓa sanin ma yanada ita ba, sai dai me? Yatsunshi ne suka sake yarda pencil ɗin.
A tsorace ya kalli Baba wanda yanayinshi kaɗai zai sa kasan yana cikin tsananin ɓacin rai.
Fatima dake waje tana jiyo kalamanshi sama-sama hawaye kawai take yi, ita kam tasan ko kowa zai amshi kaddarar abinda ya faru tasan banda Malam, yanzu ya zasu yi?

(To wannan lamari mu kanmu kallon juna muka yi dan tuni tausayin abinda ke faruwa ya gama mamaye mu, me kuke ganin zai faru?)

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

Umm Asghar Ce
Da
Ayusher Muhd

BAQEER
NA
UMM ASGHAR
DA
AYUSHER MUHD

RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAKWAS

{8}

Yanda ya da ka mishi tsawar itace ce ta ƙara gigita shi yace "Ɗauki mana, ka tsaya kana yin wani abu salalo-salalo kamar mara jini a jiki, kana ganin idan baka dage ba zamu kai ga cimma nasara ne? Maza ɗauki pencil ɗinnan ka fara tun raina bai gama ɓaci ba, kuma so nake yi ka ƙure basira wajen yin zane mai kyau mai ma'ana." Hannunshi yana rawa ya ƙara ɗaukar pencil ɗin ya riƙe da ɗan ƙarfi wai don ya samu ya zauna a hannun sai dai wata irin azaba da yaji ta ratsa shi har tsakar kanshi ya sakashi sakin pencil ɗin jiki na rawa, wasu hawaye ne masu ciwo suka sulmiyo daga idanunshi, ɗaga kai yayi ya kalli Baban daya kirne fuska ya sha kunu tamkar ba shine wannan Baban mai yawan so da tattalin shi ba, kwata-kwata yanzu babu tausayi a cikin ranshi sai fatan cikar burinshi kawai da yasa a gaba. Da ƙyar ya iya buɗe baki yace "Wallahi Baba ba zan iya ba, hannuna bai gama warkewa ba ko yaya nayi ƙwaƙƙwaran motsi dashi ba ƙaramar azaba nake sha ba." Babu zato yaji Baba ya sauke mishi wani irin gigitacen marin daya gigita shi har ya kusa faɗowa daga kan wheel chair ɗin cikin taimakon Allah yasa hannunshi mai lafiya ya riƙe hannun kujerar wanda ya taimakeshi bai kai ga faɗowa ba.

Cikin hargagi da masifar da Baqeer ya saba jin shi yana yiwa ƴan uwanshi da iyayensu mata sai dai bai taɓa katarin an sauke mishi shi ba ya nuna shi da yatsa yace "Wallahi ba zaka so ganin kalar ɓacin raina ba idan har baka ɗauki pencil ɗin nan kayi zanen nan ba, kana nufin duk uban kuɗin dana kashe da lokacina dana ɓata a kanka sun tashi a banza kenan? Baƙin ciki kake yi min ne Baqeer? Ganin ina daf da cika burina na shekara da shekaru, inace akwai ƴar baƙin ciki a tsakaninmu dama?" ya karashe maganar yana ji kamar ya saki kuka ko yaji sauƙin damuwar data cunkushe a zuciyarshi, ta yaya sai da yake daf da ganin cikar burinshi Baqeer zai nemi ya watsa mishi mafarki da burin da ya ɗauka gaba ɗayan rayuwarshi yana ginawa. Hawaye kawai Baqeer yake yi don yafi Baba jin baƙin cikin wannan ƙaddarar data sameshi sai dai baya da yadda zai yi don a yanzu dai a irin ciwon da yake ji a duk lokacin da ya motsa hannunshi yasan babu abinda zai iya ko yana son yin zanen bare ma baya cikin nutsuwar da zai iya yin wani zane a yanzu, ƙunci da damuwar dake danƙare a cikin zuciyarshi baza su bari ya iya yin komai ba.

A fusace ya fito daga ɗakin ya buga ƙofar da ƙarfin da sai da ya girgiza ginin ɗakin, wani irin wulaƙantaccen kallo ya watsawa Fatima data kasa matsawa daga ƙofar ɗakin tun bayan da Baba ya korosu waje ya rufe ƙofar ɗakin da Baqeer a ciki, yana wucewa tayi wuf ta faɗa ɗakin sai dai halin da taga ɗan nata a ciki ya ƙara sanyayar mata da gwiwa, kuka yake yi irin mai cin zuciyar nan wanda baka jin sautinshi sai dai kaga zubar hawayen kawai, tunda take bata taɓa ganin Baqeer cikin wannan yanayin ba, itama bata san lokacin da kukan ya suɓuce mata ba sai dai tayi saurin saka hannu ta toshe bakinta tana ƙoƙarin hana kanta yin kukan sai dai tausayinshi da take ji ba zai bari ba don duk sadda ta kalleshi sai taji wani irin rauni ya lulluɓeta. A haka taja jiki ta ƙarasa gabanshi ta tsugunna, hannayenta tasa ta kamo hannunshi mai lafiyar ta riƙe a cikin nata duka biyun, wani irin rauni ne ya lulluɓeshi ganin da yayi wa mahaifiyarshi a tsugunne a gabanshi, tausayinsu gaba ɗaya ya kamashi har bai san lokacin da ya fashe da kuka ba "Umma" kawai yake ambata muryarshi na rawa. Sai da suka yi kukansu ya ishe su sannan ta haƙurƙurtar da zuciyarta tasa hannu tana share mishi hawayen tace "Kayi haƙuri Baqeer da duk abinda zaka gani a yanzu, dole sai ka koyawa zuciyarka haƙuri ka koyi ɗauke kai daga al'amuran mutane ka koyi haƙurin zama dasu a yadda suka zo maka don ba kowa ne yake baƙin ciki da ƙaddarar data sameka ba, wasu har cikin ransu murna suke yi da abinda ya sameka ba dai zasu fito su nuna bane kawai, Allah ya baka lafiya ya ƙara maka haƙuri da danganar karɓar sabuwar ƙaddarar data shigo rayuwarka a yanzu."
Chapter 12 · 0% Book details