Sashe 117
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*****
Mayar da kayan data fara zubawa cikin akwati tayi a wardrobe ta shirya, komawa tayi ta zauna akan tabarma tana jan carbi sai dai lokaci bayan lokaci tana tuna tijarara da Badaru yayi mata, kome yasa ya hanata tafiya kuma bayan shi da kanshi yace ta bar mishi gidanshi. Wayarta ta janyo ta kira Baqeer, lokacin da kiran ya shiga wayarshi yankan ɗinki yake yiwa Tanimu don shi har yanzu hannunshi bai gama faɗawa ba ya dai iya taka keke sosai ya haɗa kaya amma yanakwar na ɗan bashi wahala. Ajiye scissors ɗin hannunshi yayi akan kayan da yake yankawa ya ɗauki wayar, yana ganin sunan Umma ya saki wani murmushi. Da sallama ya amsa wayar sai bayan ta amsa sallamar da yayi mata sannan suka gaisa. Tambayarshi tayi yadda ake ciki da shagon da yake son ya buɗe ganin har ya kusa kammala makarantar koyon ɗinkin. Nutsuwa yayi yace "Ai na faɗa miki mun samu shagon har an biya rabin kuɗin hayar, In Sha Allah zuwa ƙarshen watan nan akwai waɗanda na yiwa sketches zasu biyani da kuɗaɗen da wasu dana ajiye a banki nake so na zuba kekunan, a yanzu dai ni da Tanimu ne zamu fara zama a wurin sai munga yadda kasuwar ke tafiya kafin mu nemi wasu ma'aikatan kuma."
Tana sauraren shi har ya gama yi mata bayani sai gyaɗa kai take yi cikin nuna gamsuwa da abinda yake faɗa duk kuwa da ba ganinta yake yi ba. "Allah ya taimakeka ya bada sa'a ya saka maka albarka a cikin kasuwancin da zaka fara. Allah ya kareka daga sharrin maƙiya da mahassada ya kawar da dukkanin wasu abun ƙi ya yalwata arziƙinka."
"Ameen Umma," kafin yake cewa yana jin wasu ƙwallar tausayinta sun cicciko mishi a ido. Ko ƴaƴa nawa ne irinshi da suka yi dacen samun uwa ta gari irin Umma mai mayar da damuwar ƴaƴanta damuwarta, mai sayar da farin cikinta don ƴaƴanta suyi dariya, mai yawan kyautayi da tausayin ƴaƴanta wacce cigaban ƴaƴanta shine nata, gaskiya basu da yawa don kafin a samu irin Umma a cikin al'umma sai an daɗe. Har suka yi sallama bata daina yi mishi addu'a ba abinda yake ƙara mishi ƙwarin gwiwa da karsashi akan son ya ƙara dagewa wajen ganin ya cimma burinshi ko don ya saka farin ciki a cikin zuciyar Umma.
Tun lokacin da ya faɗa mata ƙudirinshi akan sana'ar ɗinki da yake so ya fara ta duƙufa wajen yi mishi addu'a babu dare babu rana tana roƙa mishi alherin Allah akan abinda yasa a gaba, ita a yanzu bata da wani buri data sanya a gaba sai fatan ganin cigaban Baqeer, tana so taga ya zama wani abu a rayuwa shi yasa take jure duk wani wulaƙanci da take gani a cikin gidan har ranar da Allah zai iyakance musu wannan zama ta tafi ta barwa Badaru gidanshi din daga ranar daya kori Baqeer daga cikin gidan taji a ranta itama bata da muhalli a cikin shi...
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
Da
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA ƊAYA*
{71}
Mummy ce ta ja Nabila ɗaki ganin su kaɗai suka rage a cikin falon, suna shiga tasa key ta rufe ɗakin zuciyarta na wani irin zafi, ta kasa waigowa daga jikin ƙofar, Nabila kam zama tayi a ƙasan ɗakin tana share ƙwalla kafin tace “Mummy ni dai don Allah ko ma menene kiyi amma ki sa a aura mun Kabir…..”
Wani irin waigowa tayi ta bita da mugun kallo kafin tace “Kabir? Ke yanzu kina ganin ko numfashin mutuwa kike yi Senate zai aura miki shi? Sau nawa ina ce miki ki bari? Ko kina tunanin ni ban san me nake yi bane?”
Kai kawai ta sunkuyar ƙasa tana jin tsanar kowa na kamata, Mummy ce ta ɗan sauke ajiyar zuciya kafin tace “Ya aka yi kika san Inna ba ita ta haifeki ba?” A hankali ta ɗago ido kafin ta kauda kai gefe tana kallon wajen gado ba tare da tace komai ba, Mummy ta sake cewa “Ya aka yi kika sani? Don kaf garin nan babu wanda yasan sirrin nan, kuma saboda wannan sirrin tunda muka baro Nijer bamu sake komawa ba, ba neman ƴan uwan mu muka yi ba bare su san inda muka koma suzo, to ya aka yi kika ji?”
Yanzu kam kanta ta dawo dashi wurin Mummy, ɗan nazari Mummy tayi don da Nabila na bala’in jin maganarta, sannan babu ruwanta kwana a gidan ma da ƙyar Zee da Inna ke sakata zuwa kafin shekaru huɗu baya da ta fara canza halaye, a gaban mutane ita mai tarbiyya ce amma in su biyu ne sai ta fara mata maganar raini. Da sauri ta kalleta tace “Ba dai sanda Inna tayi mini faɗa akan karatunki ba? Sanda Zeey bata daɗe da fara karatu a ƙasar waje ba akan insa Senate ya biya miki kema ki tafi?”
Kanta ta sunkuyar. Mummy ji take yi kamar ta rufeta da duka, hakan yasa itama ta tsugunna a wurin da Nabilan take zauna ta sa hannu ta ɗago kafaɗarta ta riƙe da hannayenta biyu tana jijjigata tace “Yanzu hankalinki ya kwanta kin ɗauki fansar abinda kike so?” Wasu hawaye ne suka zubo mata, Mummy ta sake matsa kafaɗarta tace “Kin san baƙin cikin da kike sakani a ciki kuwa? Kin san halin da nake shiga a baya saboda ke? Amma na daure na nemar miki gata, ko kina tunanin da ban auri senate ba zaki yi school ɗin da kika yi? Zaki zauna gidan da kuke yanzu? Zaki samu mota da gatan da kike dashi yanzu?” Takaicin Nabila take ji wanda ji take yi baƙin cikinta duk ya gama nuƙurƙusarta.
Sakinta tayi kawai ta miƙe tsaye ta fara ciro kayan Nabila tana zubosu ƙasa daga cikin akwati, Nabila da sauri ta sa gwiwoyinta a ƙasa tace “Mummy na tuba, na tuba wallahi kawai kishi nake yi yadda naga kina son su Zainab amma sam ba so nayi a tozartaki ba, sannan wallahi bansan abinda ya faru zai koma haka ba, don Allah ki yafe min.” Wani irin ɓacin rai Mummy ke ji sai data watso kayan duka sannan ta ce “Tashi ki haɗa kayanki ki bar mini gida, kin ji na faɗa miki.” Tana kaiwa nan ta fito daga ɗakin idanunta sunyi jaaa saboda ɓacin rai, abinda ta gina shekara da shekaru yarinyar nan ta lalata mata shi lokaci ɗaya yanzu ya zata yi, ta rasa wani tunanin zata yi kawai idanunta suka hango Zeey da Kabir sun fito daga ɗakin shi, baya tayi kawai sai ji tayi ta faɗi, da gudu Zeey ta taho inda take ta ɗagota tana tambayarta menene? Mummy a hankali take kallonta tana fitar da numfashi sama sama tana cewa “Jiri kawai nake ji, Auta abubuwan da ke faruwa ƙwaƙwalwata da zuciyata sun kasa ɗaukansu.” Kama mata tayi ta kaita ɗaki har Mummy ta riko hannunta, zare hannunta tayi daga cikin na Mummy ba tare da ta amsa mata ba sannan ta fito daga ɗakin.
Kabir na tsaye inda suka barshi kai kawai ya girgiza ya koma ɗakin shi, Zeey ma ɗakinta tayi sai dai da yake ɗakinta kusa dana Nabila ne tana jiyo kukanta daga ciki, kuka take yi sosai wanda yasa Zeey take jin komai ba daɗi ita dai sam ba zata yafe mata ba sannan bata son ganinta a wannan lokacin, sai dai kukan na ƙara ɗaga mata hankali ga magriba ta kawo kai, hakan yasa ba zata iya fita ba, waya ta ɗauka ta kunna karatun Qur’ani kawai ta haɗe kanta da gwiwarta wuri ɗaya, ta rasa wani tunanin zata yi, sam yanzu tsoron mutane take.