Sashe 144
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A sukwane ya fice daga ɗakin, yana shiga ɗakinshi ya faɗa toilet ya fara kelaya amai, tuni ɗan abincin da yaci ya fice sai kakarin kawai da yake yi. Daya tuna warin bakin Asiya sai yani wani aman ya yunƙuro mishi gashi cikin shi babu komai. Da ƙyar ya samu aman ha tsaya ya fito yana sauke numfashi, haba wannan masifa har ina? Shi yanzu da wanne zai ji fisabilillahi? Ga rashin aikin yi ga mata ƙazama Allah ya bashi, duk inda ya juya baya jin daɗi ya rasa inda zai saka ranshi yaji daɗi. Ƴar buƙatar data shigar dashi ɗakin Asiya ma tuni ta kama gabanta tayi nata wuri don a yanzu sai yaji ko ɗan yatsanta ba zai iya riƙewa bare har ya haɗa jiki da ita.
Allah ya taimaki Baqeer da yanzu shi ake yiwa wannan ƙazantar shi da baya son ƙazanta ko misƙala zarrati. Koda yake hakki ne shima yake bibiyar shi hakkin abinda ya yiwa Baqeer gashinan yana ɗanɗana kuɗarshi a hannu. Dana sani iya dana sani Bello yayi ta akan abinda ya yiwa Baqeer gashi nan tun ba'a je ko ina ba yaga sakamakon abinda ya aikata.
*****
Tunda ta hau titi take sharara gudu fatanta kawai ta ganta a gaban Ummi ta kwanta a kafaɗunta tayi kukan baƙin cikin da yake damunta, tayi kukan rabata da masoyinta da ake nema ayi, tayi kukan yaudararta da soyayyar bogi da Mummy tayi, tayi kukan tausayin abinda ɗan uwanta na jini ya jawa Baqeer, tayi kukan abubuwa da yawa data rasa a rayuwarta saboda riƙon taɓararru da Mummy tayi mata. Hannu tasa ta ɗauke hawayen daya zuba daga idanunta, duk ta tuna yadda Mummy ta dinga raina musu wayo tana ƙara nesanta su da mahaifiyarsu suna jin haushinta sai taji zuciyarta ta ƙuntata, ta rasa laifin me suka yi mata data yi musu irin wannan zaluncin ta shiga tsakaninsu da mahaifiyarsu tasa mahaifinsu ya hana su zuwa inda take ya kuma hana ƴan uwanta zuwa su gan su. Ribar me Mummy taci da duk tayi hakan bayan basu aikata mata laifin komai ba.
Hukuncin Allah ne kawai ya kai Zainab Ɗambatta lafiya don bata da wata nutsuwa haka nan tayi tuƙin har Allah ya kaita garin lafiya. A wani wajen sayar da layin waya ta tsaya ta sayi sabon layin mtn aka yi mata register ta biya ta bar wurin. Dole ta canja layi idan har tana so ta nesanta kanta daga Baqeer, tana jin nauyinshi tana jin nauyin ƙara haɗa ido dashi sabida abinda Kabir yayi mishi, gashi Daddy yayi rantsuwa ba zai aura mata shi ba, ita kuwa baza ta iya aurenshi ba har sai Daddyn ya amince da batun auren da kanshi, a yanzu kuwa tasan abu ne mai wahala yayi hakan, bata so ta cigaba da jin muryarshi ko ta ganshi don tasan rabuwarsu zata yi musu matuƙar wahala.
Tana yin parking motarta a ƙofar gidan Ummi, Inaya na dawowa daga makarantar islamiyya. Tana ganin motar Zeey ta tsaya a ƙofar gidansu ta rugo a guje tana murna. Sauri tayi ta goge hawayen fuskarta ta fito daga motar tana dariya, buɗe hannayenta tayi Inaya ta shige jikinta ta rungumeta. "Aunty Zeey ashe zaki dawo da wuri?" Ta tambayeta tana ɗaga ido ta kalli fuskarta, ɗan ɓata fuska tayi ganin yadda fuskar Zainab tayi jajawur da kumbura saboda kukan da tayi. Cike da kulawa tace "Aunty Zeey me aka yi miki? Kuka kika yi ko?" Girgiza kanta tayi tace "A’a abu ne ya faɗa min a ido shine yayi tayi min zafi amma yanzu ya fita." Ɗaga kai Inaya tayi alamun ta fahimta, suna riƙe da hannun juna suka shiga cikin gidan. Tun daga harabar gidan Inaya ke ƙwalawa Ummi kira tana ceqa "Ummi fito ki gani Aunty Zeey ta dawo," har suka ƙarasa cikin parlourn. A tsaye a bakin ƙofar kitchen suka tarar Ummi ta zubawa ƙofar parlourn ido tana so taga shin da gaske ne abinda taji Inaya na faɗa ko kuwa. Zeey na shigowa taga Ummi kawai sai ta ruga a guje ta rungumeta tana sakin wani irin kuka mai ciwo, hannu Ummi tasa tana bubbuga bayanta a hankali dan tabbas tasan wani abu ya sake faruwa.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce*
Da
*Ayusher Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA TARA*
{89}
Ummi bayan ta kawai take shafawa har sai da ta gaji da kanta ta tsagaita da kukan, Inaya kam tana gefe tayi tsuru duk zuciyarta ba daɗi ganin Zee na kuka, ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta kamo hannunta tana cewa "Inaya ki je ki cire kayan islamiya ki watsa ruwa kizo kici abinci." Ba musu tayi ciki su kuma suka shiga ɗaki, da yake Zee ta saba shigewa jikin Mummy sai take jin yau ɗumin jikin tata mahaifiyar take so, kanta ta kwantar akan cinyar Ummi tana maida kukan dake neman ƙara tasowa, Ummi ce ta daure tace "Ki kwanta in kin ware anjima sai muyi magana," tayi maganar tana zare jikinta don ta kula Zee na buƙatar kaɗaicewa, da sauri Zee ta riƙota tana girgiza kai tana cewa "Ummy karki tafi don Allah, gaba ɗaya duniyar nan bata mini daɗi wurinki kaɗai nake sa ran samun sauƙin abinda ke damuna." Kallonta Ummi tayi ta dawo kusa da ita ta zauna ta kamo hannayenta tare da juyo da ita saitinta tace "In ɗan adam ya shiga damuwa me yake cewa?" Wasu hawaye ne suka zubo tace "Nayi addu'o'i Ummi kawai zuciyata ce nake ji kamar zata buga."
Kallon da Ummi ke yi mata ne yasa tace "Allahumma inni a'udhu bika minal-hammi wal-Ḥuzni, wal-ajazi wal-kasli wal-bukhli wal-jubni wa ḍala'id-dayni wa ghalabatir-rijal." Lumshe ido tayi, Ummi ta saki murmushi kaɗan kafin tace "Ke da Halima ne?" Kai ta girgiza sai kuma hawaye ya sake zubowa tace "Ni da kowa ne ma Ummi wanda nake so an hanani aurenshi, Daddy ya takura sai dai na auri Junaid kuma ni bana sonshi," ta kalli Ummi tana jin wani zafi a ranta tace "Ummi don yana gurgu shikenan sai ya zama abun ƙyama?" Mamaki ne ya bayyana a idon Ummi tace "Gurgu ne?" Zee ta jinjina kai tana goge fuska tace "Kema nasan ba yadda zaki yi ba sai dai wanda ya ja mishi abun...." Sai kuma tayi shiru don bata son ta ɓata Kabir a wajen Ummi tun kafin ma su haɗu, ita dai Ummi baza tayi ƙarya ba amma tabbas ba zata yiwa yar ta fatan auren gurgu ba, Zee ta kalleta sai kuma tayi shiru kawai don bata son ta ɗagawa Ummi hankali daga zuwa, kai kawai ta girgiza alamun babu komai tana ciza ƙasan leɓenta.
Ummi ta shafi saman kanta tace "Ki tashi kiyi sallah kici abinci naga babbar jaka kika zo da ita a hankali sai mu tattauna." Kai ta ɗaga alamar to, hakan yasa Ummi fita, tana maida ƙofar ta rufe ta bi ɗakin da kallo cike da tausayin Zee tabbas abubuwa da yawa sun faru sai dai da alama na saurayin yafi damunta, a hankali zata kula da yarta za kuma ta gina shaƙuwar da suka rasa, kuskuren da tayi a baya na barin Halima ta gaje mata yara ba zata sake makamancinshi ba yanzu.
Zee kuwa a ɗakin alwala tayi bayan tayi sallah ta kwanta akan sallayar ta zubawa wayarta ido, number Baqeer take nema bayan ta goge komai dake cikin wayar ɗazu, wayar ta ɗaura akan kirjinta tana jin wani raɗaɗi na rashinshi na damunta, kalaman Badaru ne ke sake dawo mata, ashe yayanta ne duk ya janyo mishi wannan bala'in? Ta runtse idanuwanta wanda suka ƙanƙance saboda kukan da tasha.