← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 168

Sashe 122

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

^****
Tunda ta shiga Dambatta gabanta ke faɗuwa, yaushe rabonta ma da ƴan uwan mamanta? Duk laifin da suke yiwa Mummy ya kamata ace sun yi musu magana ne ba wai su janye jikinsu ba, wayar babban yaron ƙanin mamanta ta kira don numbershi kaɗai take dashi shima don ya kirata ne kwanaki akan za ayi family meeting in da hali suzo, shine lokacin data tambayi Daddy akan zata zo ya hanata daga nan tayi saving ta kira tace baza su samu zuwa ba, har kiran ya katse bai ɗauka ba, hakan yasa ta sake kira, yanzun ma kamar zai katse sai kuma taji ance “Hello?”
Ajiyar zuciya tayi tace “Ya Adam kana ina? Gani a Dambatta.” Duk da yayi mamakin zuwanta bai hanashi cewa “Dambatta? Ke ɗin? Sannan in kinzo menene nawa a ciki?” Hankali a kwance tace “Kaga don Allah kar mu tsaya shiririta kana ina? Sam na kasa gane garin gani dai kusa da wani shago, gefen tasha kazo sai muje gidan Hajiya Goggo daga nan ina so in ɗan yi ziyara.” Ga mamakinshi kafin ma yace mata zai zo sai ji yayi tace “Kayi sauri ina jiranka,” tana kaiwa nan ta kashe wayar tana kallon mutane nata hada-hada, murmushi tayi tana tunanin yanzu fa kowa da tashi rayuwar, kowa da matsalolinshi. Atm ta hango daga gefe ta gangara ta ciro kudi 100k tasa a jakarta, sannan ta sake dawowa, tana kokarin duba agoggo taji anyi knocking glass ɗinta, zugewa tayi ta kalleshi da yake shi ta sanshi har sanda tazo sallama zata tafi ƙasar waje shi yasa bata yi wani kokonto akanshi ba hakan yasa tace “Ya Adam shiga.” Shiga yayi ya tamke fuska shi a dole yana son ta bashi haƙuri, Zeey ta hau hanya tana cewa “Ina zamu yi?” Samun kanshi yayi da nuna mata sai dai fuskar nan har yanzu babu wargi, har suka isa gidan Hajiya Goggo, parking tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya tace “Muje?” Gaba yayi yana tafe yana muzurai, ita kam ko a jikinta. Daga waje yace “Hajiya Goggo ga Zainabu.” Tana daga ciki tace “Zainabun Malam Lawi?”
Zeey tayi saurin cewa “Hajiya Goggo taku dai.” Mamaki ne ya kamata ta ɗan yaye labule don ganin wacece, Zeey ta sakar mata murmushi tace “Hajiya Goggo ina wuni?” Tamke fuska sosai Hajiya Goggo tayi wanda babu alamun wargi a tattare da ita, ta maida labulen tana cewa “Hala aurenki yazo ne kina tsoro kar azo biki aga babu dangin mahaifiyarki ko ɗaya.” Zeey ta sani sarai basu kyautaba ta taho jikin ƙofar ta tsaya tana cewa “Hajiya Goggo kishiruwa tunda  na taho bansha ruwa ba, sannan bikina bai zo ba da saura sosai.”
Hajiya Goggo bata tanka mata ba sai kuma can ta leko kamar an tunzuro ta tace “Kun gama tozartamu shine yanzu zaku dawo neman mu? Ace duniya da gaskiya? Kwanaki Kawu yana kan gadon mutuwarshi amma burinshi ya sakaku ke da Kabir a idanunshi, nan na wanki ƙafa ni da Altine muka je har gidan ku amma aka hanamu shiga aka koro mu wai mahaifinku ya hana mutanen Ɗambatta shiga mishi gida, haka muka tura a sanar da matar gidanku dalilin zuwan mu amma fir aka hanamu shiga, muka gaji da zama a waje muka dawo.”
Kalaman Hajiya Goggo ne taji sun ɗaure mata kai, mene? Ita dai a iya saninta sune suka je suka ciwa Mumy mutunci akan ta mallakesu, me suke nufi kuma yanzu? Adamu ne yayi saurin cewa “Allah in na tuna abun nan ji nake yi kamar naje har gidan dukanku nayi muku rashin mutunci don haka ki zo ki tattara ki bar mana gari.” Zee gaba ɗaya kanta taji ya kulle, bakinta na rawa tace “Anya ba ciki kuka shiga ba?” Tsaki Dada tayi tace “Yaushe rabon da ko harabar gidan ku a barmu mu shiga? Ni ban masan kun koma gidanku na da ba sai da muka je wancan aka ce kuna nan to Allah ya taimakemu mahaifiyarku akwai wata ƙawarta a unguwar ita tayi mana kwatance muka je.”
Idanuwan Zee ne suka fara canza launi tsoro da fargabar abubuwan da take ji su zama gaskiya take, taya zata fuskanci abubuwan nan in har Mumy ƙarya tayi musu a karo na biyu? Hajiya Goggo ce ta katseta da cewa “Kuje can mu mun sallama ku ai ba ku kaɗai muke dasu a dangi ba.”
Bakinta na rawa tace “Gidan Ummy a taimaka a kaini," ta ƙarasa maganar muryarta na wani irin rawa tana jin har cikin jikinta na rawa, yanayinta da suka gani ne yasa suma ta basu tausayi, ta juya da sauri tana kallan Adamu tace “Don Allah…..”

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*

*BAQEER*
*NA*

*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA HUƊU*

{74}
Chapter 122 · 0% Book details