← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 168

Sashe 140

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka nan ya haƙura ba don ranshi yaso ba sai don babu yadda zai yi, sai dai duk da hakan bai rabu da yin zane ba yana yi yana ajiyewa a cikin kayanshi ba don zasu yi mishi wani amfani ba sai don zanen yana sanya shi nishaɗi shine abu guda ɗaya da yake ƙaunar yi a rayuwa.
A farko farkon rayuwarsu Badaru da Suleiman Ƙaraye abokai ne saboda gidajen iyayensu dake maƙwabtaka da juna sai daga baya abotar tasu ta fara ja baya saboda shi Suleiman yana ganin Badaru bai yi karatu ba don haka bai kai yayi abota dashi, ba to shima Badaru da yake ya kasance mutum ne mai tsananin zuciya yasa ya janye jikin shi daga Suleiman don ba zai ɗauki ƙasƙanci da cin fuskar da yake yi mishi ba duk suka haɗu a hanya ko wani wuri dai haka. Haka dai suka sake abokai kowa yana yi da daidai shi ba kowane lokaci suke gaisawa ba sai ta ƙure. Ana cikin haka ne Badaru ya haɗu da wata yarinya daya mato a soyayyarta, son Uwani yake yi bil haqqi da gaskiya. Kullum sai yaje zance wurinta saboda baya iya yin kwana ya yini bai sanyata a idanunshi ba. Kusan kowa dake unguwar yasan da soyayyar Badaru da Uwani saboda ita ma anyi dace bata kula kowa sai shi, duk wanda zai je wurinta yace yana sonta a take zata sallamesu tace akwai wanda take so, tace dole ta taya Badaru kishin kanta saboda bai rageta da komai ba, komai ya samu nata ne, kafin ya yiwa kanshi hidima sau ɗaya yayi mata sau goma don haka take tattalin farin cikin shi take gudun abinda zai ɓata mishi rai.

Ana haka har iyaye suka shiga maganar aka yi musu baiko. Tuni Badaru ya tayar da ginin gidanshi, yana ta shirin aurenshi da Uwani da aka saka rana har shekara biyu zuwa lokacin ya gama ginin da yake yi. Wata rana Suleiman na zaune a majalisar da suke zama shi da abokanshi Uwani tazo wucewa. Yana ganinta yaji ta kwanta mishi don haka ya nemi sanin gidansu a wajen abokanshi anan suke faɗa mishi ai budurwar Badaru ce don anyi musu baiko ma ranar auren kawai ake jira a ɗaura. "Ai dai baca riga an ɗaura ba ko?" Yace yana kallon abokinshi da yayi maganar. Da kai ya amsa mishi. "Ku zuba ido kuyi kallo ni na faɗa muku ba dai yarinyar can ta auri Badaru ba idan har ban sameta ba sai dai duk mu taru mu rasa gaba ɗaya.”
Wannan alwashin da yaci ne yasa yana tashi daga wurin bai dire ko ina ba sai a ƙofar gidansu Uwani yasa aka yi mishi sallama da ita. Da farko ta ɗauka Badaru ne yazo duk kuwa daba lokacin zuwan shi bane sai data fito taga wani mutum da bata taɓa gani ba. Haka dai Suleiman yayi amfani da wayewarshi irin ta ƴan boko ya tsara Uwani, tun tana ƙin kulashi har tazo bata san lokacin da ta fara son shi ba. Haka tayi ta yiwa Badaru halaye har dai daga ƙarshe ta fito ta nuna mishi ita fa ba zata aureshi ba don ta samu miji ɗan boko daya ƙware a iya gayu da ƙwalisa.
Hankali a tashe Badaru ya baza neman saurayin da ya hurewa Uwani kunne har take neman guje mishi, anan yake jin ai Suleiman ne saurayin da take cewa tayi ɗan boko, baƙin ciki kamar ya kashe Badaru don a rayuwa idan akwai wata da yake so to Uwani ce, shine Suleiman zai je ya hure mata kunne ya rabashi da ita. Itace ya ɗauka ya nufi majalisar dasu Suleiman ke zama, yana zuwa wurin ya ɗaga itace zai kwaɗa mishi aka tattare aka hanashi. Badaru ya ƙara harzuka yana masifa yaa cewa Wallahi yau ko shi ko Sulaiman dan sai sunyi kunar bakin wake. Hankalin Sulaiman ya tashi ganin da gaske Badaru yakeyi zai halaka su, nan fa aka fara bashi baki. Haka yayi ta ɗurawa Suleiman zagi yana cewa sai yaga bayanshi tunda ya rabashi da masoyiyarshi tace bata son shi bayan daf ake da ɗaura musu aure. Wannan abun da Suleiman yayi wa Badaru ne yasa suka ƙara ƙullatar juna ƴar gaisuwar da suke yi ma tuni suka daina.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce*
*Da Ayusher Muhd*

*BAQEER*
*NA*

*AYUSHER MUHD*
*DA
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA SHIDA*

{86}

Wani abun Allah shi kanshi Suleiman ɗin da yayi ƙwacen budurwa sai kuma yazo bai auri Uwanin ba duk da tsananin son daya samu kanshi yana yi mata don da farko da niyyar yaudara yaje mata bare da yaji ance ita ce wacce Badaru zai aura sai yaga ai kawai bari yaje ya tarwatsa abun amma tun tafiyar bata yi nisa ba ya afkawa sonta mai ƙarfi. Sai kuma Mahaifin shi yace ba zai aureta ba saboda ta fito daga ƙaramin gida ma'ana iyayenta masu ƙaramin ƙarfi ne shi kuma yana ganin ai ɗanshi yafi ƙarfin yayi aure a irin wannan gidan. A haka Uwani tayi ba wan ba ƙanin karatun ɗan kama. Ita bata auri Badaru ba da yaso ta da dukkan gaskiyarshi saboda ta samu Suleiman ɗan gayu ɗan boko da take ganin yafi Badaru komai yace yana sonta, a ganinta irin wannan damar sau ɗaya take zuwa a rayuwa idan tayi sake ta rasashi ba ƙaramar asara zata tafka ba. Sannan ita bata auri Suleiman ɗin ba don iyayenshi suna ganin yafi ƙarfinta. Sai kuma daga baya ta dawo wajen Badaru shi kuma yace taje ya barwa Suleiman.

A Ɗambatta makarantar da aka turashi bautar ƙasa ya haɗu da Hafsatu a lokacin tana aji biyar na secondary shi kuma yana ɗaukarsu darasin English. Suleiman yana ganinta yaji ta kwnta mishi a rai, tun bayan rabuwarshi da Uwani bai sake gain macen data shiga ranshi farat ɗaya ba irin Hafsatu. Bai ɓata lokaci ba ya gabatar mata da kanshi ya miƙa mata ƙoƙon barar soyayyarta. Sai aka yi dace itama ya kwanta mata don haka bai sha wata wahala ba wajen yaɗa manufarshi. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fara soyayya, babu daɗewa iyayen Suleiman suka nema mishi auren Hafsatu don koda suke a ƙauye ta fito daga babban gida irin wanda mahaifin Suleiman ke so don haka aka saka rana bayan ta gama makaranta da sati biyu. Anan unguwarsu mahaifin shi yayi mishi gini mai kyau a jikin gidan shi, kasancewar Suleiman tilon ɗanshi yasa yake gatata shi fiye da ƙima.
A wannan lokacin matan Badaru uku, Jamila ce uwargida sai Abu sannan ya auri Fatima daga baya saboda daga Jamila har Abu ƴaƴa mata suke ta haifa mishi shi kuma namiji yake so shi yasa ya kasa haƙuri yana ganin kamar su ɗin basu da cikin haihuwar ƴaƴa maza. Fatima na zuwa ta samu cikin Baqeer wanda tsiransu da Kamalu wata uku ne itama Abu ta haifi ɗa namiji. Tunda Fatima ta haihu Badaru ya ɗauki son duniya ya ɗorawa Baqeer komai ya samu Baqeer, tun bai fara cin abinci ba ake sayo mishi kayan ƙwalama ya hana asauran ƴaƴanshi idan Fatima tayi magana yace ba haka ba wani sa’in har burin Allah ya isa yake mata in dai tabawa wani abu. Wannan bambancin da yake nunawa ne yasa sauran matan suka tsani Fatima da ƴaƴanta don Badaru ya fifita su akan su da nasu ƴaƴan don ko da Abu ta haifi Kamalu bai nuna wani farin ciki ba sai ma cewa da yayi sai yanzu zata haifa mishi namijin bayan ya riga ya samu, ranar suna baiji kunyar yankawa Baqeer katan rago ba shi kuma Kamalu aka yanka dan akuya karama.
Tunda Badaru ya ƙyalla ido yaga Baqeer yayi gadon baiwarshi wajen iya zane yayi ta murna yana alfahari dashi yana jin shine zai cika mishi burinshi da nashi mahaifin ya daƙile mishi tun bai yi nisa ba, hakan yasa ya hana Baqeer sakat yana koya mishi dabarun yin zane, ko wasa Baqeer bai isa ya fita ba sai Badaru yace bayan ya bashi aiki bai yi ba shine zai ce ya biyewa yaran banza suna shashanci. A komai sai ya nuna bambanci don komai na Baqeer daban yake a wajen Badaru. Makarantun daya saka su daban su suna zuwa ta yaku bayi shi kuwa mai tsada mai kyau, haka ko wajen sutura ba iri ɗaya yake ɗinka musu ba, komai na Baqeer yafi kyau da tsada. Wannan bambancin da yake nunawa ne yasa ƴan uwanshi suka tsaneshi idan ka cire Hadiza da Maryam babu mai san shi a cikin ƴan uwanshi kowa haushin shi yake ji.
Chapter 140 · 0% Book details