← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 168

Sashe 59

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙyaleta tayi tasha kukanta ya isheta sai da tayi shiru don kanta sannan Umma tace "Sarai kin san halin mahaifinku Hadiza amma ba zaki yi haƙuri kamar yadda kowace mace take yi ki zauna a ɗakin ki ba, kun dai fi so kullum sai kun janyo mini ɓacin rai?” Wani hawayen Hadiza ta share cikin rawar murya alamun kowane lokaci zata iya cigaba da kukan tace "Umma ya zan yi? Wallahi duk haƙurina mutumin nan baya gani sannan kuma saboda Allah Umma a ina ake yin aure babu abinci, kullum fa haka yake ficewa ya bar mu da yunwa daga mu har yaran sai dai kowacce tasan yadda zata yi ta ciyar da ƴaƴanta ni kuma kin sani ba wani abu gareni ba, jiya na tashi ko ƙwaya bani da ita a ɗakina kuɗin da nazo kika bani ya ƙare a awon abincin da zamu ci da ƴan sauran buƙatu, jiya haka su Hassan suka tafi makaranta basu ci komai ba ni kuma ganin har lokacin tashin su ya kusa na rasa yadda zan yi yasa na ɗauki wata tsohuwar akwatin shi ta garwa na kaiwa ƴan gwangwan suka saya sannan na samu nayi mana abincin da muka samu muka ci, to wai akan ya dawo na sanar mishi da yadda aka yi na ɗauki akwatin da ba ma amfani yake yi da ita ba shikenan ya dinga surfa ruwan bala'i yana yi mini zagin tsame nama har yana cewa wallahi ba zai yarda ba sai na biyashi akwatin shi ko na bashi kuɗin da aka sayar ni kuma nace bazan bayar ba tunda ai hakkin shi ne ya ciyar damu amma ya fice ya bar mu babu abinda zamu ci don nayi ƴar dabara shine akan haka zai ci mutunci na, wallahi Umma har marina yayi da ace na tsaya ma nasan har dukana sai yayi ni kuma shi yasa na taho gida don wallahi na gaji da auren nan da babu abinda nake tsinta a cikinshi sai tarin damuwa da baƙin ciki," ta ƙarashe maganar tana sakin wani marayan kuka.

Ita kanta Umma kasa riƙe hawayenta tayi tana jin tausayin irin rayuwar da suka tsinci kansu a ciki ita da ƴaƴanta kowanne akwai tarin ƙalubalen dake dabibaye da rayuwarsu sai dai kuma hakan ba shine zai sa ta goyawa Hadiza baya ta kaso aurenta ba alhalin zaman gidansu ma ba daɗi gare shi ba don haka cikin tausasawa tace "ai kuwa dai haka nan zaki koma ki cigaba da haƙuri, sanin kanki ne zaman gidan nan a yanzu yafi ƙarfinki tunda dai kina jin abinda mahaifinki yace ba zaki zauna mishi a gida ba ba tare ma da ya bari yaji abinda kika zo dashi ba, dole kije ki cigaba da haƙuri ko don ƴaƴanki ki kuma nemi abun yi da zai riƙe ku ke da ƴaƴanki tunda dai kin san halin mijinki ba mai ɗaukar nauyin gidan shi bane sai dai ku kuyi mishi.”

Cigaba tayi da kuka jin Umma tace sai dai ta koma alhalin zaman gidan gaba ɗaya ya fice mata akai, idan ace akwai abinci ma sauran buƙatu ne ba'a ɗauke musu da da sauƙi sai taje tayi ta haƙuri amma saboda Allah ta ina zaman aure zai yiwu babu abinci don haka tace "Yanzu Umma haka ma zaki ce na koma bayan idan na koman ma ba canjawa zai yi ba?"
"Haƙuri fa zaki yi Hadiza ki koma amma ba zai yiwu na barki ki zauna a gidan nan ba alhali mahaifinki yace sai dai mu haɗu mu bar mishi gidan gaba ɗaya, ni kuwa da girmana bazan je na zaune wa Dada ba bayan ga Baqeer can na kai mata tana riƙe dashi, sana'ar dai ita zaki nema dole don haka sai kiyi tunani anan unguwarku me kike ganin mutanen wajen sun fi buƙata ko kuma me nene ba kuda yawaitar masu shi kinga daga nan sai mu san wacce irin sana'a zaki yi tunda dai akwai kuɗin kujerun nan a wajena sai ayi amfani dasu ki kafa jarin.”

Ajiyar zuciya kawai Hadiza take saukewa tana share hawaye, ita dai a sonta Umma ta barta ta zauna a gida sai dai kuma bata ga alamar Umman zata ƙyaleta ba, gara ma taje ta nemi na kanta yadda zata fi ƙarfin wulaƙanci har a wurin mijin ma don yadda yake yi mata cin kashi baya yiwa kishiyarta haka saboda ita tana da abun hannunta bata neman komai a wurin shi sai ma shi da yake lallaɓawa tana bashi rancen kuɗi. Tashi tayi ta ɗauke Aydah da tayi bacci a ƙasa ta gyarawa su Hassan da tun shigowar su suka kwanta bacci kwanciya sannan ta nemi wuri kusa da ƴaƴanta ta kwanta, tasan dai dole tayi tunanin abinda zai fisheta kafin gobe ta tattara ta koma can gidan.

*****

Tunda ya shige ɗakin yake tunanin abinda ya kamata ya fara da zai taimake shi da mahaifiyar shi da ƴan uwanshi sai dai kuma duk sana'ar da tazo ranshi sai yaji anya kuwa zai iya irin wannan sana'ar alhalin shi ba ƙafa ce dashi ba a yanzu, matsalar da aka samu ita ce tun farko da zane ya buɗe ido kuma shine kaɗai abinda ya tsaya ya koya don yana tuna wani lokaci acan baya da yaso ya koyi sana'ar ɗinki Baba ya hanshi yace me zai yi da wani ɗinki shi da yake da sana'ar shi a hannu, yadda Allah ya bashi baiwar iya zane kuɗin da zai samu a harkar bai ninka abinda zai riƙa samu a ɗinki ba, yana ji yana gani ya haƙura da wannan burin nashi ya mayar da hankali akan zanen to yanzu gashi inda rayuwa ta kawo shi, bai iya komai ba sai wannan zanen da baya jin a yanzu zai iya ƙara riƙe pencil da sunan painting ko da za'a saka mishi bindiga a kanshi kuwa.

Wajen kayan zanen shi ya nufa ya ciro takarda da pencil ya saita su yadda zai ji daɗin yin zane, pencil ɗin ya ɗora akan takarda ya rufe ido yana so yayi picturing abinda zai zana kamar dai yadda yake yi a baya sai dai jin ƙwaƙwalwar shi yayi ta zama blank kwata-kwata sai yaji tamkar bai taɓa sanin yadda ake yin zanen ba, yayi-yayi ya jarraba yin zanen nan amma ya kasa. Ji yayi gaba ɗaya zuciyarshi ta ƙuntata, ta yaya abun da tun yana yaro ƙarami ya ƙware akai yanzu tashi ɗaya lokaci guda zai gudu ya bar shi tamkar bai taɓa sanin yadda ake yi ba, gaba ɗaya sai ya zama frustrated yayi jifa da takardar ya watsar da pensiran yana sakin huci. Kanshi ya kama ya rirriƙe yana jin kamar yayi ta sakin ihu ko yaji wani sanyi ko yaya ne a cikin ƙirjinshi da yayi mishi wani irin nauyi yana yi mishi zafi.

Ƙara janyo kayan da yayi watsi dasu yayi ya sake ɗaukar pencil wai ya ƙara gwada zana ko kaza ce amma duk yadda yayi tunanin ta yadda zai fara ya kasa, haka nan dai yayi ta ƙirƙirar abinda zai zana har ganye sai da yayi tunanin ya zana amma ya kasa, sai ya samu ƙwaƙwalwarshi kamar an shafe mishi sanin yadda ake yin zanen ne kawai, wata irin ƙara ya saki yana jin rashin amfanin kasancewar shi a raye tunda ba zai iya yiwa mahaifiyarshi da ƴan uwanshi maganin kukansu ba, shine babba kuma shine gatansu duk wata taƙamarsu dashi suke yi to yanzu gashi ba zai iya yi musu maganin komai ba shi yasa sam baya ganin amfanin rayuwar shi. Da hanzari Dada ta shigo ɗakin tana cewa "haba Baqeeru, ayi bawa shi dai ya kasa tawakkali kullum sai ka ɗaga mini hankali ka ɗagawa uwarka da bata da wani tunani sai naka, ai ko baka ɗauki dangana don kanka ba kayi don mahaifiyarka". Kallon tsakar ɗakin tayi taga yadda ya watsar da kayan zanenshi tace "Dole ne sai kayi zanen ne? Ba sai ka nemi wata sana'ar ba tunda dai Allah bai hana maka rai da lafiyar da zaka tashi ka nemi na kanka ba, haba. Banda dai ubanka ya kwaɗaita maka son zanen nan ni banga wani abu da mutum zai tsinta a cikin shi ba wai sai kaji an saka maƙudan kudaɗe an sayi takardar da wani ƙato ya taƙarƙare ya zana. Ai ina ga kwashe kayan zanen zan yi idan baka ganin su ai baka ce dole sai kayi ba alhalin duk ranar da ka gwada yin zanen bama zama lafiya, ƴar walwala da nutsuwar da ka samu duk sai subi su ruguje.” Tana sababi tana tattare kayan haka ta kwashe su ta mayar ɗakinta tayi musu kyakkyawan ɓoyo don bata jin zata ƙara barin Baqeer ya gansu ma bare yace zai ɗauka ya gwada yin zane bayan ta lura abinda ke ƙara dagula nutsuwa da kwanciyar hankalin shi kenan.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce*
      *Da*
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
     *NA*
*AYUSHER MUHD*
            *DA*
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA BAKWAI*

{37}
Chapter 59 · 0% Book details