← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 168

Sashe 71

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*******
Plate kowa yaja yasa abinci a falo da Dady, kallan Zeey yai yace “Ƙira Kabiru mana.”
Kallansa tai tace “Anya ma yana gidan kuwa bari dai na duba.”
Mumy ce tai saurin rikota tana cewa “Baya ɗan jin dadi shine nace ya kwanta.” Da mamaki tace “Yanzu fa na ganshi da zan….” Sai kuma tai shiru kar ya gane yanzu ta dawo ta wayance tace “Allah Mumy ba wani bacci kawai gulma ce.” Rikota Mumy tai tana cewa “Bari ni na duba.”
Bata musa ba ta koma ta zauna ta kalli Dady tace “Dady bari na ƙira Nabeela.”
Hannu ya mata alamar ta dakata sannan yace “Magana nakeso muyi shiyasa bance tazo ba, mahaifin Junaid yace kun haɗu ko?”
Nan danan yanayin fuskarta ya canza tace “Eh amma Dady kasan ba wani abu tsakanin mu.”
Kai ya jinjina yace “First step ne so babu matsala, Mumy fa? Da na tafi batajin dadi ne naga duk tayi sanyi.”
Kai tsaye ta buɗe baki tace “Mutanen Dambatta ne……”
Cikin hanzari Mumy wacce ta taho tace “Zee zo kiyi maza ki dubamin Nabeela.”
Kallan Mumy tai da mamaki sai dai ganin yanayinta yasa ta tashi da sauri, tana zuwa inda take ta ja ta sukai falan ciki tace “Zeey kin manta nace mu bar maganar nan?”
Baki ta turo tace “To gashi nan abin yana damunki har Dady ya gane.”-
“Please Zeey ya isa nima na ware banasan na zama sillar mai raba alakar da Allah ya haɗa .”
Jiki a sanyaye ta kalleta sannan tace “Shikenan na bari Mumy.”
Haka suka koma Mumy tace Kabir ma wanka, sukaci abinci ta koma ɗaki tai salla sannan ta faɗa gado.
Kwanciya tai zuciyarta na tuno mata yanayin Baqeer nan ta ɗau waya tamai text tace ‘Me kakeyi?’
Baqeer dake zaune yana addu’oi sai daya shafa sannan ya ɗau wayar maida mata yai da ‘?’
Baki ta taɓe tace “Oh ni!”
Zata ajiye wayar wani sakon ya shigo ‘Thank you’ kallan sakon tai zuciyarta na ji kamar tafi kowa farin ciki, rungume wayar tai a ƙirjinta taɗan yi juyi tana lumshe ido. Zata mai reply kenan Nabeela ta shigo da sauri ta rufe wayar tace “Aunty Nabs.”
Karasowa ciki tai ta zauna tana cewa “Ɗazu kinwa Kabir laifi ne?”
Ido taɗan juya kaɗan tace “Allah ni na ɗauka ma wani abin ne, kinga Allah ki kyale shi yai abinda yaga dama nifa a iya sanina ba abinda namai kawai kinsanshi sam baya rasa abin cewa.”
Jiki a sanyaye tace “Kinsan dai kaf duniya baki da kamar shi dan Allah Zee ki daina ɓata mai rai.”
“Wai ke kullum a bayanshi kike bakya taɓa ganin laifinshi?”
“Ke kuma kullum su Mumy da Dady a bayanki suke ai.”
Kallan Nabeela tai cike da zargi tace “Bayan gaskiya dai ke kanki dan dai kina san biye mai ne amma kema kinsan neman faɗa yakeji dani ko da yaushe.”
Kawar da maganar tai da cewa “Abinci fa? Kinci?”
“Umm!” Kawai tace dan tabbas tana jin ba da ɗi, mikewa tai da sauri Zee ta ɗago ta kalleta har tabar ɗakin.
Dakinta ta koma ta kwanta zauna tana tunani, ya zatai da abinda ke ranta? Bayan tasan ba laifi bane amma ba wanda zai yadda da ita? Hannu biyu tasa ta shafi fuskarta.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*

*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA HUƊU*

{44}

Da sassafe ya tashi ya shirya don baya so Salim yazo ya samu bai gama shiryawa ba, tun jiya dama ya faɗa mishi yazo yau da safe zai yi mishi rakiya wani wuri, Salim ɗin bai bi ba'asin inda zai raka Baqeer ɗin ba sai ma daɗi da yaji na ganin ya fara warewa ya fara dawowa da walwalarshi, rayuwarshi ta fara hawa kan saiti kamar yadda take a daa ba kamar yadda ya ƙuntata rayuwarshi tun bayan da ya gamu da larurar nan ba. Ita dai Dada tana kallonshi ƙanzil bata ce mishi ba, tana kallon lokacin da ya haɗa wuta sannan ya ɗebo ruwa a randa ya zuba a tukunya ya ɗora ruwan wanka, bayan yayi zafi da kanshi ya sauke ya juye a bokiti sannan yaja boktin a hankali ya kaishi har wajen randar ya surka, a hankali ya dinga tura bokitin yana kan wheelchair ɗin shi har ya kai banɗakin, bai nemi taimakon Dada ba ita ma bata ce zata taimaka mishi ba kamar yadda take yi a mafi yawan lokuta da idan taga yaje zai yiwa kanshi wani abu zata tashi ta karɓa tayi mishi ko bai ce ba. Haka yayi tara-tara da dabara ya kai ruwan wankanshi da kanshi ya tuɓe yayi wankan bayan ya gama ya fito ya shirya cikin wasu kayanshi wankakku sai dai babu guga. Kallon kanshi yayi yana tunanin wai shine Baqeer wannan ɗan ƙwalisan saurayin da komai nashi ya fita daban dana matasa ƴan uwanshi gashi yau ko ɗan turaren da zai fesa a jikinshi baya dashi, shine yau yake saka sutura babu guga, tabbas dole ya saita rayuwarshi ta koma daidai ya tsaya da ƙafafunshi ya nemi abinda zai rufawa kanshi asiri ba zai yiwu ya cigaba da zama a haka ba yana ƙuncin zuciya kawai don Allah ya jarabce shi da wata larura ya mayar da kanshi mara amfani ba, bai ma ƙara tabbatar da nakasa ba kasawa bace sai da yake ɗan fita waje a yanzu yana ganin yadda mutane suka tashi tsaye da neman na kansu, akwai wani makaho anan inda yake yawan zama yake ganinshi yana sana'ar gyaran takalma har yana mamakin ta yadda yake iya yin gyaran alhalin baya gani, ranar daya fara ganinshi sosai abun ya tsaya mishi a rai don yaga dai ga wanda yafi shi zama nakasashe tunda shi ko ganin ma baya yi amma bai zauna ya dogara da kowa ba ya fito yana neman na kanshi to ahi kuwa don me yasa don ya gamu da larurar ƙafa kawai zai koma ya zauna yana jiran komai sai anyi mishi.

Salim bai zo ba sai can wajen ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe. Yana jin muryarshi suna gaisawa da Dada yayi zuruf ya fito yana maka mishi harara. "To ko dai na koma don naga kamar baka yi maraba da zuwana ba, daga ganina kawai sai ka riƙa aiko mini da harara?”Hararar tashi ya ƙarayi yace "Tun ƙarfe nawa nace maka kazo shine baka tashi zuwa ba sai yanzu?” Shima hararar tashi yayi yace "Anƙi azo da wurin Mallam daga zuwana zaka wani tareni da faɗa ko tambayar abinda ya tsayar dani baka yi ba?”
“Au haka ma zaka ce?"
"Eh ɗin" Ita dai Dada tana jin cacar bakin da suke yi tana dariya sai da suka gaji suka bari don kansu sannan suka yiwa Dada sallama suka fita. Sai da suka fita waje Salim ke tambayarshi inda zasu je, sai sannan yayi mishi bayanin zanen da yayi wa Zeey ranar nan bayan ta kaiwa telan ya ɗinka mata ya nemi da yayi mishi wasu ya saya da duk yadda aka yi dai har ma da kuɗin daya samu shine yake so ya rakashi kanti ya sayi ƴan abubuwan buƙata. Jinjina kai Salim yayi kafin yace "Kai amma nayi maka murna abokina, wallahi sosai nayi farin ciki, don baka san yadda zamanka a haka yake damuna ba don nasan har da hakan yake ƙara maka yawan damuwa tunda ba sabawa kayi da irin wannan zaman ba, tun baka gama mallakar hankalinka ba kasan neman na kanka to yanzu kazo baka iya yin komai kaga kuwa ai dole ka shiga damuwa amma yanzu Alhamdulillah da Allah ya kawo maka wani abun yin cikin sauƙi, Allah ya sanya alkhairi yasa wannan shine silar warwarewar duk wasu matsaltsalunka.”
Chapter 71 · 0% Book details