← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 168

Sashe 128

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tashi tayi jikinta yayi wani irin sanyi ta nufi ɗakin Ummi, tana tsaye a gaban wardrobe ɗinta tana neman abu Zainab ta shigo ta zauna a bakin gado. Juyowa tayi ta kalleta sai taga tana share hawaye. Cike da kulawa tace "wani abu aka yi miki kike kuka?" Girgiza kanta tayi sai kuma tace "wai Daddy ne yace na koma gida gobe." Murmushin takaici tayi tace "ke kuma shine kike kuka? Gidan naku ne ba kya son ki koma ko ya aka yi?"
Gaba ɗaya sai ta fashewa Ummin da kuka don bata gaji da ganinta ba, da ta ɗauka cewa bata da buƙatar Ummin a rayuwarta domin Mummy ta cike mata dukkanin wasu gurbi na uwa don haka nema bata damu da rashin Ummin a rayuwarta ba sai yanzu da ta zauna da ita na wasu ƴan kwanaki tasan ashe lallai babu wani giɓi da wani zai cike maka na mahaifiya kowacce irin kulawa yake yi maka kuwa, ashe ita uwa matsayinta daban ne, ganinta gata ga Ummin kaɗai wata irin nutsuwa da farin ciki yake sakata wacce duk tsawon rayuwarta bata taɓa tsintar kanta a ciki ba.
Zama Ummi tayi a kusa da ita ta kamo hannayenta ta riƙe cike da tausasawa irin ta uwa tace "ai bamu rabu ba kenan Zainab, tunda kika zo kika ga wuri nasan idan kin tafi ma zaki sake dawowa. Kada ki saɓa umurnin mahaifinki ki shirya ki koma kamar yadda yace ga waya nan ai zamu dinga gaisawa kin ji?" Ɗaga kai tayi alamun amsawa sai dai har wannan lokacin bata daina kukan ba. Haka Ummi tayi ta lallashinta tana bata baki har ta samu ta sassauta kukan da take yi. "Tashi kije ki wanke fuskarki kada Inaya ta shigo ta tarar dake kina kuka," ɗan murmushi tayi sai ta tashi ta koma ɗakin Inaya inda aka sauketa tunda tazo anan suke kwana ita da Inaya.
Da dare suna zaune a ɗakin Ummi tana haɗa mata kayanta tana yi tana mata ƴar nasiha ita dai Zainab tana saurarenta sai dai bata jin daɗin tafiyar da zata yi ta bar Ummin, bata gaji da zama da mahaifiyarta ba duk da ba wani sakewa take samu daga Ummin ba komai tayi sai tayi ta mata faɗa tace bata iya ba hakan bai sa taji zata gujewa zama da Ummin ba. Inaya na maƙale da ita tunda Zainab ɗin ta faɗa mata gobe baza ta dawo daga school ta isketa ba. "Aunty Zeey idan kin tafi yaushe zaki dawo?" Ta tambayeta. Ɗan shiru tayi tana kallon Inaya da duk tayi wani iri kamar tasa kuka, kawar da kanta tayi daga kallon Inayan tace "In Sha Allah bazan daɗe ba zan dawo kin ji," ɗaga mata kai tayi alamun amsawa. Ummi na kallon duk abinda suke yi ita kanta bata jin son tafiyar da Zainab ɗin zata yi saboda tana son zama da ƴarta ta koya mata hidimar kula da gida da ba'a koyar da ita ba to amma ya zata yi tunda ubanta yace lallai ne ta koma.

*****
Maryam yau ta samu kanta cikin tsantsar farin ciki sakamakon ƙiran ta a waya da Baban Aareef yayi yace mata yana tafe da kyakkyawan albishir wanda ta daɗe tana jiran samuwarshi ta tanadar mishi tukuicin da zata bashi. Duk da ta kasa iya tuna menene wannan abu da ta daɗe tana fatan samuwarshi amma ta samu kanta cikin ɗoki da son sanin abinda ta samu da yasa maigidanta kasa jira ya dawo kafin ya faɗa mata, tasan dai ko menene abun alkhairi ne. Tashi tayi ta ƙara kimtsa gidan ta shiga kitchen ta shirya mishi kyakkyawan abinci, stir fried spaghetti tayi sai chicken salad da sharma milk (kunun shinkafa). Haka ta jere komai akan table sannan ta shiga tayi wanka tayi kwalliya cikin atampa julius holland da aka yi mata ɗinkin straight gown, sosai kwalliyarta tayi kyau kayan suka bi jikinta suka kwanta suka fitar da duk wasu curves na jikinta.
Dawowa tayi parlour ta zauna, ƙamshin turaren wutan data saka ya haɗu dana jikinta da sanyin ac ya bada wani sassanyan ƙamshi mai kwantar da zuciya da sanya nutsuwa. Tana zaune taji shigowar motarshi don dama yace mata zai biya ta school ɗin su Aareef ya taho dashi shi yasa yau bata fita zuwa ɗaukarshi ba. Tashi tayi taje ta tsaya daga bakin ƙofa tana jiran shigowarshi. Da fara'arta ta taresu ta karɓi jakar hannunshi. "Sannu da zuwa Daddy," tace tana rausayar da kai gefe. Ɗan rungumota yayi a jikinshi cike da kulawa. Sai da ta cirewa Aareef uniform tayi mishi wanka ta bashi abinci sannan ta koma wajen Babanshi. Taimaka mishi tayi ya cire kayan jikinshi ya shiga wanka bayan ta haɗa mishi ruwan wankan. Fito mishi da kayan da zai saka tayi ta feshe su da turare ta ajiye akan gado sannan ta koma parlourn wajen Aareef don bata cika son barinshi ya zauna shi kaɗai ba sai yaje yayi mata wata ɓarnar bata sani ba.

Bayan ya fito daga wankan ya shirya sannan ya fito parlourn, direct wajen dinning table ya nufa itama tashi tayi ta bishi, yana zama ta ɗauki plate tayi serving ɗin shi abinci ta ajiye a gabanshi, kujerar dake gefen damanshi taja ta zauna yana cin abincin shi suna ƴar hira har ya gama cin abincin ya tashi ya koma wajen kujeru ya zauna ita kuma ta tattare wurin ta mayar da kayan kitchen sannan ta dawo ta zauna a kusa dashi suna taya Aareef kallon tashar cartoon, duk ta ƙosa ya faɗa mata albishir ɗin shi kuma sai faman ja mata rai yake yi. Sia da ya gama wanata sannan yace ta ɗauko mishi jakar laptop ɗin shi a ɗaki, tashi tayi taje ta ɗauko ta kawo mishi ta koma wajen zamanta ta zauna. Buɗe jakar yayi ya fito da wata takarda ya miƙa mata, hannu biyu tasa ta karɓa tana karantawa. Ai tun bata gama karanta abinda ke jiki ba tasa ihu tana ɗan tsallen murna daga zaune, shi dai sai dariya yake yi yana jin daɗi cikin ranshi saboda farin ciki da ya yasa ta. Offer ce ta aiki daya daɗe yana nema mata sai yau Allah ya nufa ta samu.
Sosai ta nuna farin cikinta da samun wannan aikin itama ta samu ta tallafawa Umma ba komai sai an jira Baqeer yayi ba ga kuma Hadiza a gefe da itama take buƙatar taimakonsu don ma yanzu Allah yasa albarka a cikin markaɗen da take yi bata rasa abinda zasu ci abinci ita da yaranta har ma tayi wasu ƴan buƙatun nata a ciki. Sai murna take yi ta kasa ɓoye farin cikinta, ƙasa yayi da murya don baya son Aareef dake kusa yaji ne zai ce yace mata "sai murna kike yi har yanzu baki bani goron albishir ɗin ba," wata ƴar dariya tayi cike da kissa tace "kai ma kasan goron albishir ɗin ka na nan na tanadar maka sai mun shiga daga ciki," ta amsa mishi tana lumshe ido.
Haka suka zauna cikin farin ciki har lokacin sallar magriba yayi ya tashi ya fita masallaci, tashin Aareef tayi suka shiga ciki sai da tasa shi a gaba yayi alwala ya fara sallar sannan ta tafi ɗakinta tayi sallar itama. Tasan Baban Aareef baya dawowa sai yayi sallar isha'i tukunna, turaren quta ta ƙara kunnawa gidan tana jin daɗi cikin ranta don tuni ta cire rai da smaun aikin nan ganin an daɗe ana nema ba'a dace ba ashe rabonta ne a gaba shi yasa tuntuni bata samu ba sai yanzu.
Tare suka fito daga masallaci shi da Baffa, suna tafe a hanya suna ƴar hira ta tsakanin ɗa da mahaifi anan ne yake faɗa mishi batun samun aikin da Maryam ɗin tayi. Wani kallo Baffan yayi mishi yace "Kai yanzu daka sama mata aiki ka gama yarda da ita ne?"
"Ban gane ba," ya tambayi Baffan nashi da mamaki. "Eh ka gama yarda da ita ka tabbatar baza ta ci amanar ka ba ka amince ta fita aiki inda zata je tana cuɗanya da wasu mazan? Wai me yasa baka yin abu da tunani ne? Baka yi shawara ba babu komai kaje ka nemawa mace aiki matan nan da ba amana ce dasu ba kana zamanka lafiya lau aje a yayibo cuta a saka maka ko a kawo maka ɗan da ba naka ba cikin gida. Ka dai yi tunani wannan maganar aikin a barta gara ta zauna a cikin gida ta cigaba da kular maka da gidanka kai kuma ka fita ka nemo ka kawo mata tunda ai Alhamdulillah komai da take buƙata ka ɗauke mata shi to me take nema da har sai ta fita aiki zata samu."
Shiru yayi yana jinjina maganar da Baffan ya faɗa, sai yaga kuma haka ne fa wasu matan basu da kamun kai suna fakewa da fita aiki suna yawon banzar su, duk da yasan Maryam yasan bata daga cikin irin waɗannan matan to amma maganin kada ayi kada a fara gara kawai a haƙura da aikin tunda Allah yasa bata fara ba.
Sallama yayi wa Baffa bayan sun shigo harabar gidan ya nufi part ɗin shi shima ya shige nasu.
Chapter 128 · 0% Book details