Sashe 79
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
*****
Da Asiya ta kafa naci sai da Bello ya ware wasu kuɗi daga cikin kuɗaɗen daya ajiye a bankin saboda sayen fili ya fara gini tunda gashi Allah yasa zai fara ajiye iyali dole ne yayi planning yadda rayuwarsu zata kasance. A cikin kuɗin ne ya cire wani abu yayi mata sauran kayan gadon da iyayenta suka kasa yi mata saboda takurar da tayi mishi ta hanashi sakat wayar safe daban ta yamma daban ta dare daban duk dai akan ya daure ya sayi sauran kayan ɗakin don kamarsu bai dace ace an shigo gidansu aga ɗaki ɗaya kawai suka iya shiryawa ba. To da yake shima ɗan ƙaryar ne irinta da tayi mishi bayani sai yaga fa eh lallai haka ne shine ya cire kuɗin aka sayi sauran kayan gadon da za'a saka a ɗakunan biyu da suka rage, haka shi ya sayi gas cooker dasu fridge da freezer har da washing machine aka zuba a gidan. Ai kuwa kan Asiya sai ya ƙara girma ta dinga iyayi tana fi'ili ita a dole ta kerewa sa'a ta shiga sahun manya a yanzu. Haka zata kalli Habi ƙanwarta ta sheƙe da dariya tace "ke kam ina ga ai sai dai kiyi amfani da gawayi don banga alamar wanda kike kulawa zai iya yi miki hidimar arziƙi irin wannan ba.” Ita dai Habi ko kulata ma bata yi don tace ɓata lokaci ne tsayawa ta biyewa Asiyar suna rigima akan abinda tasan ba lallai ne ya ɗore ba.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
“
Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA TARA*
{49}
Tunda Umma ta tafi yake zaune yana lissafi, wayarshi ya janyo jiki a sanyaye tunda har yanzu babu wanda yayi mishi magana, ga mutumin daya amshi zanen nan ya biyashi har yanzu bai sake yi mishi magana ba shima. Saƙo ya gani ta shigo ta direct message ɗinshi buɗe wa yayi don yana da tabbacin Salim ne. Business account ɗin daya gani ne yasa ya buɗe cike da mamaki don daga yanayin dp ɗin ba masu ɗinki bane, yaso shiga cikin profile ɗin su yaga me suke yi sai dai idanuwanshi ne suka gane mishi saƙo ana tambayarshi akan sketch na ɗinki, iska ya furzar sannan ya danna reply akan guda nawa suke so, waya ce ta shigo ta IG ɗin ganin daga su ne yasa ya ɗauka, namiji ne mai maganar nan ya sanar dashi a Abuja suke amma suna da branch anan Kano, zasu turo representative ɗin su yaga inda yake saboda gudun kada su sayi abinda ya watsa gari dole su tabbatar ba zai cucesu ba sannan ba zai bawa wasu zanen da yayi musu ba, don haka suke son sai yayi signing contract sannan su dinga siya. Kai tsaye yace babu matsala shima baya son yin business da mutanen da bai sani ba, mutumin yace “Sai dai mu muna neman ragi gaskiya akan zamu dinga siyan ko wane ɗaya akan naira dubu talatin, saboda yanzu abubuwan ba sauƙi garesu ba, suna kuma son su dinga fito da styles kala-kala wanda zai ƙara inganta business ɗin su.”
Baqeer yayi ɗan jim kafin yace “No, gaskiya sketching is not that easy sannan ku idan na sai da muku ya zama naku ya tashi daga nawa.”
“Mun sani amma muna so kasan mu business ɗin gaske muke son yi da kai, muna da branches a kusan garuruwa goma, sannan mu ba ƙananun mutane bane contract zamu yi duk wata zaka dinga bamu kuma duk wata zamu dinga biyanka, in muka yi requesting sketch 20 a watan nan zamu biya ka naira dubu ɗari shida.”
“In kuma baku yi ba fa?” Baqeer yayi tambayar jin ana neman dauke mishi hankali da abinda ya kamata ya sani, “Well in har bamu yi ba still zamu baka dubu hamsin sai mu ƙara a cikin contracts, ka duba business account ɗin da nayi maka magana dashi.” Nan Baqeer ya buɗe ganin yadda suke da mabiya sosai da yadda abinsu ya bunƙasa. Ya sani sarai babu yadda zai yi tunda bai iya yanka da ɗinki da kanshi ba, zai amince dasu sai dai baya da tabbas akan zai dogara dasu.
“Okay, sanda zaku turo wani sai muyi arranging inda zamu haɗu.” Nan suka yi sallama ya kashe, shiru Baqeer yayi yana bin account ɗin su da kallo sam zuciyarshi bata gama yarda dasu ba kawai dai babu yadda zai yi shi yasa ya amince da hakan. Har zai kifa wayar sai kuma ya dubo sunan Zainab, so yake yi yaji ya take sai dai bai san me zai ce ba, shiru yayi yana tunani, tunowa yayi da ƙofarin da tayi mishi ne yasa yayi mata text, “All good?” Ya tura tare da kallon wayar yana tunanin zai ga reply sai dai shiru babu komai.