Sashe 93
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA BAKWAI*
{57}
A waje ta gansu suna neman tarar adaidaita, gabansu ta tsaya tace "Mu wuce Ya Baqeer?" Kai ya kauda yana dube-duben abin hawa, mamaki ya ƙara kamata gani take ko kishi ne ai bai kamata ya ɗin ga banza da ita haka ba, Zee kamar ke ana binki kina wulakanta mutane yau kece kike bi ana wulakantaki? Ido ta kafamai, haka kawai ya juyo yaji zuciyarsa nasan ganinta, kallan juna sukai nan danan idanuwanta suka ciciko kallanta yai shima sai kuma hankalinshi ya tashi, meya mata? Ya ɗauka barinta da saurayinta shine daidai? Jan motar tai kawai ba tare da tace komai ba tai gaba, jiki a sanyaye yabi motar da kallo, wata iska ya furzar yanajin haushin kansa, to menene laifinta? Ai tun farko yadai san Junaid saurayinta ne to jin haushin na menene? Meya sameshi? Haushin kanshi ne ya isheshi har suka isa gida baice komai ba, Dada tana zaune a waje tana jin radio yau lale na dungurmi irin na tsofafi yarinyar makota tazo ta mata tace ta bari sai dare amma yarinyar ta nace akan sai ta mata yanzu, hakan yasa ta kyaleta, ganinsu Baqeer yasa ta saki fuska ta ɗan rage sautin radio ɗin tana cewa "A'a Malam cunkumi an dawo?"
"Sannu da gida Dada, amma cunkumin na menene?"
"Yo fuska ce kamar an aiko ma da sakon mutuwa me kake so a kiraka dashi?"
"Babu." Abinda yace kenan yai cikin ɗaki, Tanimu ne ya kalleta yana gaisheta ta girgiza kai tace "Hala an taboshi ne?" Ya girgiza kai yana cewa "Wallahi ban sani ba Dada."
Baki ta taɓe tace "Bakinku ɗaya ai can ku kuka sani." Ta cigaba da sauraran radio ɗinta tana cewa "Ga abincinka can Tanimu." Ɗaukan na Baqeer yai ya fara kai mai sannan ya ɗau nashi yai godiya ya fita.
Takaici duk ya gama isar Baqeer me take nufi da kallan datamai da kuma hawayen dake idanunta? Bayan ita kullum cikin fara'a take? Sam zuciyarshi ta kasa nutsuwa ji yake kamar yaje ya sameta yaji meke faruwa.
****
Zeey kuwa gida ta wuce kai tsaye, tana shiga ta ruga ciki tai falan Mumy, Nabeela na falansu tana ganinta ta girgiza kai sai kuma ta canza yanayin fuskarta sannan ta mike tana cewa "Zeey lafiya? Menene?" Bata ko kulata ba sai ɗakin Mumy datai, a tsaye ta ganta tana ninke sallaya da alama lokacin tai sallar la'asar, rungumeta kawai tai tasa kuka, mamaki ne ya kama Mumy ta kalli Nabeela dake bakin ƙofa ta mata alama data tafi, hakan yasa ta juya tana taɓe baki, kallanta Mumy tai bayan sun zauna a bakin gado ta ɗag fuskarta tace "Menene Baby na? Waye ya taɓamin ke?" Kara kankameta tai wanda hakan yasa Mumy tace "Babu wanda ya isa ya samin ke kuka in kyaleshi, Junaid ɗin da kikace zaki je kija mai kune ne wani abin ya faru?" Cike da shagwaba tace "J har isa ya sani kuka Mumy kema kinsan bai kai ba, sannan kunne fa naje jamai akan ya dakatar da iyayensa dan ni bazan aureshi ba."
"To meya faru kuma? Nifa kukan ne bazan ɗauka ba." Kwantawa tai luf tana cewa "Mumy ni kawai haushin kaina nakeji, inyi ta bada kaina amma yana wulakantani, haka zan cigaba da rayuwa?"
"To ki rabu dashi mana dole ne? Nifa bamga wanda ya isa ya cigaba da samin ke kuma ina kyaleshi ba." Dagowa tai tace "Shine bazan iya ba Mumy yanzun ma ganin yanda ya kalleni ne yasa naji ina neman yin hawaye, anya Mumy kaina kalau kuwa? Bayan ko kalmar so bai taɓa furtamin ba?"
Shafar kanta tai tace "Zeey ya kikeso nai dake? Haka kikeso na cigaba da sa miki ido kina wannan san haukan? To shi bama ki da tabbas yana sanki kenan?" Kallan Mumy tai idanunta yai raurau tace "Inadai ganin alama."
"Alama shine ya barmin ke ki taho gida kina kuka? Bani numbershi."
Nan danan ta zaro ido tace "A'a Mumy abinfa baikai haka ba, kawai dai haushin yanda bai kulani bane yasa naji zafi amma zamu shirya."
"Zeey kinsan dai ko kowa a duniya zai gujeki ina bayanki ko? Banasan ki dinga kaskantar da kanki dan Allah ki cigaba da zama Zainab dana sani wace bata barin abu ya dameta." Kai ta ɗaga ta rungumeta tace "Insha Allahu Mumy na, thank you."
Ya dade a ƙofa yana san shigowa amma baisan Nabila ta ganshi ba dan takardun abokinsa daya manta ba tabbas da bazai dawo ba, sam taki tashi daga falan, ganin Zeey ta shigo da mota yasa ya ɓoye da sauri, yana kallo ta shiga Nabila ta bita yasa yai saurin lalaɓowa ya shigo, ɗakin sa yai ya ɗauko takardun sai dai yana buɗe ƙofa yaga Nabila a tsaye ta rike kugu, turashi tai cikin ɗakin sannan ta shiga tasa key, kallanshi tai tace "Ya Kabir badai gudu na kakeyi ba?" Matsar da ita yai tare da yin hanyar ƙofa yana cewa "In gudun naki nake ma ai ba laifi tunda kina neman zama abin gudu." Yana kai nan yai saurin yin waje sam yana mamakin Nabila, tana daga cikin mutane masu hankali daya sani a mata amma baisan me ya sameta ba tunda ta fara nuna tana sanshi yake ganin wasu halaye nata da ke tsoratashi a kullum ana haɗata da Zeey sai dai ko kaffara bazaiyi ba Zeey ko tanasan mutum bazata bada kanta ba, dan tasha yin samari abokansa sai dai ba wanda ma taba fuskar soyayya bare akai ga yin waya, haka zasu karashi binta su hakura, a haka kuma Inna kullum mitarta Zeey batada tarbiyya Nabila ce mai tarbiyya shima kuma Dady kullum maganar kenan.
********
Badaru da tsamin jiki ya tashi dan ko sallah a gida yai, sai wani nishi yake yana wash-wash, Abu kam tun dare take nazari dan tasan Badaru bazai taɓa kyalesu ba daga ita har Kamalu, gashi kuma tunda ya fita jiya haryanzu bai dawo ba balle ta zaunar dashi suyi magana a samu mafita, ƙofa taji an buɗe wajen karfe shiga na safe da sauri ta leka wajen Kamalu ne ya shigo cikin sanda, lekowa tai tamai alama daya shigo ɗakinta hakan yasa ya shigo suka shige kuryar ɗaki, kallansa tai tace "Kamalu ina kake kai kayayyakin Malam da kake ɗauka kadai san bazai barmu ba balle abinda kamai ɗazu." Kallanta yai yace "Amma kina kallo shekani barzaho yaso yi?"
"Na sani amma kai dai kasan halinshi, laifinka kawai zai gani ba nashi ba." Taja numfashi ta cigaba "Ina kayayakin daka ɗauka suke? Wai ma nikam Kamalu me kake da atamfofi da lasuka kamar mai tara lefe?"
Kai ya kauda ya zauna a bakin gaso yace "Lefe nake tarawa sannan wai me yake min ma da zaice yamin a matsayinsa na uba?"
Baki ta saki tace "Lalai Kamalu, lefe kake tarawa? Lefen uban wa kake tarawa da kudin sata?" Cike da ɓacin rai yace "Kinga Umma karki kuskura ki ƙara zaginta, ta wuce duk yanda kike tunani, Roshini dinace, sannan ba abinda zan dawo dashi wallahi sai dai yai abinda zaiyi." Yana kai nan ya mike ya fita daga ɗakin ya barta da baki a buɗe.
Jamila ce tai sallama a ƙofar ɗakin Fatima, ta bata izinin shiga, zama tai tana kallan Fatima nata faman tsinke zogale tace "Fatima kinsan yarancan ya jawo Malam ciwo? Shine na zo in akwai ƴan canji a gunki ki bani na siyo mai magani dan jikinshi yayi tsami."
Kallanta Umma tai tace "Dama garin neman faɗa da yara ake jawo raini, mutum sai masifa sam ba hakuri ba yadda da kaddara?"
"To yanzu dai mu bar maganar ki bani kuɗi dan Malam yana warkewa sai ya hukunta Kamalu dole kuma musha kallo da guda." Wani kallan takaici Umma ta mata tace "Ke kina tunanin kin tsira kenan? Hmm kema kiyi a hankali daga ke har yaranki ba tsira kukai ba, sannan ni banida kuɗi ɗari biyar ce gata nan ki sai mai magani ita kenan gareni." Amsa Jamila tai ta fito tana cewa "Ko gidan ubanwa take samun kuɗi dan dai baza'ace kuɗin kujeru ne haryanzu take dashi ba." Magani ta siyowa Badaru ta bashi yasha tana cewa "Sai hakuri Malam, mata da yarane baka tara na kwarai ba banda ni na damu dakai da haka nan zasu kyaleka kudin magani wannan ba wanda ya iya taimakon mu dashi, yooo sannu wannan a cikinsu wanene yama?" Shi dai Badaru banda takaici ba abinda ke damunsa gashi ya kasa mikewa, a cike yake fam da kowa jira yake ya samu sauki duk sai yaci zarafinsu.