Sashe 165
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A daren ranar ta sami Dady a ɗakin shi bayan kowa ya tafi ya kwanta, durƙusawa tayi a gaban gadon shi tana kuka tana bashi haƙurin abinda tayi mishi, to shima bai wani ja da nisa ba yace ya yafe mata don a shekarun nan nashi yana buƙatar companionship Zainab aure zata yi haka ma Kabir dole yana buƙatar abokin zama don haka ya yafe mata suci gaba da haƙurin zama da juna, sannan in ya duba wani bangaren lefin nan ba nata bane ita kaɗai shi ma yanadashi a matsayinsa na namiji sam baiyi aikinsa ba, nan ta sanar dashi damfarar da aka mata, nan ma bai nuna jin haushinsa ba yace dama dukiyar ba hakkinsu bace gwara ma da aka kwashe. Mumy tai alkawari akan bazata sake yin wani abin da bai dace ba wanda yasa hankalin Dady kara kwanciya.
Zeey na zaune a parlour ita da Kabir, tsare-tsaren biki suke yi don fa Zeey ba wasu ƙawaye ne da ita ba, dama dai Nabila ce a yanzu kuwa ko son ganinta bata yi don haka Kabir ɗin dai shine abokinta. Ƙiran wayar Baqeer ne yasa ta ajiye littafin dake hannunta tana rubuta abubuwan da suke buƙata a hidinar bikin. Ɗauka tayi cikin yauƙi tace "Ya Baqeer." Daga can ɓangaren Baqeer sai da ya lumshe idonshi saboda yadda muryar ta ratsa shi. Gyaran murya yayi saboda yadda yaji ta shaƙe kamar wanda ya daɗe bai yi magana ba sannan yace "Ba kya jin magana Sweetums bayan na faɗa miki ɓarnar da wannan shagwaɓaɓɓiyar muryar taki ke yi min ki adanata a gefe sai mun je gidanmu sannan kiyi amma kin ƙi bari ko?"
Fuskarta ta rufe cikin jin kunyar abinda yace kamar yana gabanta tace "Wallahi zan kashe wayata idan baza ka bar yi min irin wannan maganar ba." Shima cewa yayi " Nima ki bar yi min magana da wannan shagwaɓaɓɓiyar muryar taki bana so." Dariya tayi tace "to na bari, ya kake yasu Ummana da Dadata?"
"Duk suna nan lafiya kullum Dada sai tayi zancen ki wai yanzu kin daina nemanta." Dariya kawai tayi tace "Dada kenan, zan je ne amma ba yanzu," murya ƙasa-ƙasa yace "sai yaushe zaki ko sai kin zama Mrs. Baqeer tukuna?"
"Umm," kawai tace cikin jin kunya. Sai da suka gama soyayyarsu sannan yace mata ranar Saturday zasu je Ɗambatta da wa zata haɗa su da zai yi musu rakiya. Cewa tayi "tunda weekend ne sai na yiwa Mubashir magana yazo ya raka ku," Kabir na jin abinda tace ya girgiza mata kai, "kai zaka?" Ta tambayeshi, ɗaga kai yayi alamun amsawa sai ta cewa Baqeer "To kaji wai Ya Kabir ne zai raka ku sai kace ba jiyan nan ya dawo daga Ɗambattan ba, naga alama nema yake yi ya ƙwace mini Ummi don shagwaɓar da yake yi mata ko Inaya bata yi yayi ta bata kunya cikin mutane bayan ita tana yi mishi karar ƴan fari sam baya gani."
Harararta Kabir yayi jin abinda tace, bata miye mishi ba ta cigaba da yin wayarta da Baqeer sai ma tashi da tayi zata shiga ɗakinta sai ga Mummy ta fito daga ɗakin Daddy, hannunta da karamar roba da towel da alama dundumamai gun ciwon tai, ɗauke kanta Zeey tayi ta shige ɗakinta tana ƙunƙuni. "Ke kuma ke da wa?" Baqeer ya tambayeta, tsaki tayi tace "Mummyn nan mana, ni wallahi ko ganinta bana son yi."
Girgiza kanshi yayi yace "kada ki kasance daga cikin butulallun mutane mana Zainab, matar nan duk da abinda tayi muku nasan ba za'a rasa alkhairin da tayi muku ba tsawon zamanku da ita to ko don haka baki ga ya dace ki yafe mata ba, tayi laifi sannan tayi nadamar abinda tayi ke da bakin ki kike faɗa mini baki da fargabar tafiya ki bar Daddy yanzu saboda tana tare dashi tana kuma kula dashi to ai ko don wannan yaci ace an yafe mata ki manta da abinda ya faru tunda Allah yasa yanzu kuna tare da Ummi komai ya wuce don ina ganin wannan ne mafi girman laifin da tayi muku raba ku da mahaifiyarku da tayi ko?" Kamar bata so tace "umm," yace "to kin gani, don Allah ayi baƙuri a yafe mata, abinda ma kwana kaɗan ya rage miki ki bar mata gidan." Haka dai yayi ta lallashinta yana yi mata nasiha har taji abranta zata iya yafewa Mummy abinda tayi musu.
Shiru tai ta kwanta akan gado tabbas duk muguntar da Mumy ta mata ta kula dasu, ta basu kulawar da ko mahaifiyarsu basuji suna nema ba.
*****
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
DA
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊARI DA BIYU*
{102}
Ranar asabar da wuri suka ɗauki hanyar Ɗambatta, Salim ke tuƙin motar sai Kabir a kusa dashi Baqeer kuma yana baya. Suna tafe suna hirarsu cikin raha da nishaɗi kamar waɗanda suka daɗe da sanin juna tun ma ba Salim da Kabir ba abota suke yi sosai yanzu. Ƙarfe sha ɗaya na safe a ƙofar gidan Ummi tayi musu, da yake Kabir ya sanarwa da Ummi batun zuwansu yasa Ummi ta tashi da hidimar tarar su. Tun daga bakin gate Mubashir da yazo gida weekend ya taro su, shi yayi musu jagora zuwa parlourn Babansu kafin yaje ya sanar da zuwan nasu, shi kuwa Kabir tuni ya shige cikin gida wajen Ummi don ƴan kwana biyun nan da bai ganta ba kewarta yake yi duk da ma kullum ne sai ya kirata a waya sun daɗe suna hira yana jaddada neman gafarar wofantar da ita da suka yi tun ma bashi da ya kasance babba ba.
Tare Ummi da Daadan su Inaya suka shiga parlourn, gaba ɗaya sai suka ƙara nutsuwa Baqeer dake zaune akan wheelchair ma ƙoƙarin zamowa ƙasa yake yi don haka nan ya samu kanshi da jin matsananciyar kunyar Ummin. Daada ne ya hanashi sauka yace mishi babu komai yayi zamanshi ai sun san yana da larura. Cike da girmamawa suka gaishe su, Ummi dai a kaikaice take kallon Baqeer tana tasbihi ga Allah cikin ranta tana yabawa da zaɓin ƴarta, duk da taji wani iri lokacin da Zainab tace mata ai gurgu ne wanda take so don babu uwar da zata so ace yau ƴarta na auren gurgu amma data ganshi yanzu sai taji wata irin nutsuwa da zaɓin ƴar tata don tasan rashin ƙafar ce kawai tayi mishi cikas bayan haka kyakkyawa kuma nutsatsen mutum ne wanda tsantsar kamalar shi bata ɓuya ba.
Tashi Ummi tayi ta basu wuri bayan sun gaisa sai Daada ne ya zauna yana yi musu ƴan tambayoyi irin wanda duk uba na ƙwarai yake yiwa manemin auren ƴarshi. Mubashir da Inaya ne suka yi ta shigar musu da kayan abincin da Ummi ta tanadar musu, tashi Daada yayi ya basu wuri don yasan ba zasu sake su ci abincin a gabanshi ba.
Basu bar gidan Ummi ba sai da suka yi sallar azahar bayan sun ajiye musu tsarabar drinks da ruwa da suka ciko boot ɗin motar su dashi. Daga nan gidajen ƴan uwan Ummi aka raka su duk inda suka je aka nuna Baqeer a matsayin wanda Zainab zata aura sai anyi mamakin ganin shi gurgu sai dai kuma duk wanda ya kalleshi sai ya ƙara don sun san Zeey ɗin fa ta iya zaɓe rashin ƙafar ne kawai yayi mishi cikas baya ga haka baya da wata makusa a jikin shi. Duk gidan da suka je sai Baqeer yayi musu kyautar kuɗaɗe abinda ya ƙara toshe bakin ƴan ƙananan tsegunguman da suka fara tashi.