← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 168

Sashe 63

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ita kam Zainab bata daddara da sharetan da yayi ba cikin shagwaɓar da bata ma san tayi ba tace "Please mana Ya Baqeer" ta wani lanƙwasar da kai tana kallonshi fuska a kwaɓe kamar zata yi kuka. Sosai yaji shagwaɓar nan tata har cikin ranshi don haka ya kasa yi mata musu sai ma ce mata da yayi "Kayan suna wurin Dada," kamar baya so yayi maganar. "Yayyy" tace tana ɗan  tsallen murna daga zaune tace "Amma ai zaka yi mini ko? Um?" Tana ɗan turo baki gaba irin na shagwaɓaɓɓun yara, sai yaga ta ƙara yi mishi kyau a yadda take yi kamar wata yarinya wacce bata da wata damuwa a rayuwarta don haka bai san lokacin da ya saki murmushi ba har kumatunshi na lotsawa ciki ba. Dariya tasa tace "laaa Ya Baqeer yau kai ne kake yi mini murmushi?" Da sauri Salim ya kalleshi jin abinda Zeey tace, duk ƙoƙarin shi na ganin ya gimtse fuska sai ya samu kanshi da kasawa don haka kawai ya kawar da kai bayan ya gallawa Salim harara. Shi dariya ma ya bashi don haka ya ɗaga hannayenshi sama in surrender yace "nifa babu ruwana, ah to". Bin bayan Dada tayi ɗakinta ta karɓo kayan zanen da yace suna wurinta, miƙa mishi tayi ta zauna tana kwatanta mishi yanayin style ɗin da take so. Kallonta kawai yake yi yadda take kwatance kamar wata malama a gaban aji tana bayar da darasi. Idanunshi ya rufe ya ɗora pencil ɗin akan takardar, ga mamakinshi sai yaga yadda Zainab ta kwatanta mishi style ɗin tar a cikin kanshi, da sauri ya buɗe idon shi ya ɗauki paper ya fara yin zanen sauri-sauri. Tunda ya fara sketch ɗin bai ɗago ba sai da ya gana ya miƙa mata yace "duba ki gani haka yayi?"

Wani ɗan ihu Zainab ta saki tana cewa "Wow! Ya Baqeer haka kake da talent dama? Don Allah duba yadda style ɗinnan ya fita kamar yadda na kwatanta mishi abinda teloli da yawa suka kasa yi shi a cikin ƴan mintuna yayi" ta miƙawa Salim takardar, karɓa yayi ya duba sai yayi murmushi don dai bai yi mamaki ba a irin baiwar da yasan Allah yayi wa Baqeer ɗin ta fitar da zane duk da ba zanen kaya yake yi ba. Fitowa Dada tayi daga ɗakinta tana cewa "Kai lafiya kuke yi mana ihu?" Itama sakin baki tayi tana kallon ikon Allah ganin yadda Baqeer yayi zanen ɗinki kamar dama can irin zanen da yake yi kenan.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar CE*
            *Da*
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
     *NA*
*AYUSHER MUHD*
            *DA*
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA TARA*

{39}
Chapter 63 · 0% Book details