← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 168

Sashe 21

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Maryam kam da kyar ta iya jan kafafunta zuwa inda Umma take kame tace “Umma menene ke faruwa?”
Areef ta kalla tace yaje ciki gun Aydah, Hadiza ce ta taho inda take da sauri ta rungumeta kawai tana kuka sosai, haka kawai Maryam ta samu kanta da hawaye a haka ta jata zuwa ɗakin Baqeer, yana zaune akan katifa kanshi kawai ya jinginar a jikin bango duk abinda ke faruwa akan kunnenshi ne, a zaune kawai yake idanunshi yake buɗe wa kawai yana rufewa, Maryam ganin hanunshi a naɗe yasa tace “Na shiga Ya Hadiza meya samu Yaya a hannu?”
Hadiza ta fito da ita suka koma ɗakin Umma sannan ta sanar da ita abinda ya faru, tasha kuka itama ta gode Allah sai dai babu yadda zasu yi ƙaddara ce Allah ya jarabcesu da ita, haka suka fito dukansu suka tattare kayan Baqeer suka shiga dashi ɗakin Kamalu, wanda dama tare yake dasu Bashir, ɗakin kaca-kaca kai kace ba mutane ke kwana a ciki ba, haka suka gyara ɗakin sannan suka saka mishi kayan zanenshi a gefe, sunyi sa’a Salim ya zo don dama yace yana dawowa daga aiki zai zo, nan aka maida Baqeer gefe a cikin ɗakin suka jera mishi komai nashi, duk abin nan da suke yi ba wanda yake iya magana banda kwalla kawai da suke sharewa gashi Baqeer kallo ɗaya zaka yi mishi kasan shi kaɗai yasan meke faruwa akanshi dan idanunshi duk sun shanye kawai kallon kowa yake yi babu alamun mamaki ko magana, sai da suka gama sannan Maryam ta zauna a gabanshi tace “Kome zai faru Yaya muna tare da kai, Allah kuma na tare da kai, don Allah kayi ta addu’a kada ka bari ƙwaƙwalwar ka ta gushe maka tare da kowa.”
Ido kawai ya lumshe mata ya buɗe alamun to, ya ɗauki wayar Hadiza ya miƙa mata, ta girgiza kai tace “Ka dinga saka karatun Alqur'ani kana saurara, ni zan bata ɗayar wayata tunda biyu gareni.”
Baya son magana shi yasa kawai ya maida kanshi kan pillow ya kwanta, karatu ta kunna mishi sannan ta fito daga ɗakin, Salim kuma ya zauna a wurinshi.
“To ni wannan lamari, lokaci ɗaya yarima ya zama bawa? Ina aka taɓa wannan abu? Banda dai shi Malam bashi da hakuri?” Abu ta faɗa tana kallon Fatima dake gyara kayan shanyarta data zuge a labule saboda a wuce da kayan Baqeer.
Jamila ce ta sauke ajiyar zuciya tace “To ai abin ne kin san in aka koroka daga sama yafi ciwo, kin san kuwa yanzu haka har Bashir yaje yayi registration? Yau fa da kanshi Baban nasu ya kai shi makaranta.”
“Yaron nan kin san ba zai faɗa mini ba don baya so nakasheshen mu ya shiga damuwa.”
“To nima ai Salihu ne ya kawo mini gulma, kin san Bashir ɗan albarka ne.” Jamila ta ƙarasa tana zunɗen Fatima.

“To sai aka yi me? Ai Bashir da Salihu da Baqeer duk daya suke sannan ƙaddarar data sameshi bata wuce kan kowa ba, kuma menene ma sabon abu dan mahaifi ya kai ɗan shi makaranta? Banda dai……”
“Maryam!” Umma ta faɗa cikin kakkausar murya wanda hakan ya sakata yin shiru don ita dama bakinta baya shiru, don Daso ma suke ce mata a gidan saboda tsiwarta, sam bata ɗaukan raini kuma bata jiran ta kwana, su kansu Abu da Jamila sun san halinta.
Abu ta zabga mata harara tace “Sai tsabar rainin tsiya ko waye sa’anki anan ni ban sani ba, mu ba’a matsayin iyayenki muke ba? Ko kinji munce wani abu ne mai zafi da zaki faɗa mana magana?”
Jamila ta cafe tana cewa “Yara sai raini da rashin tarbiyya, to mu kunji munce wani abu ne? Ba jimami muke akan abinda ya faru ba?”
Maryam zata yi magana Umma tace “Maryam wuce ciki kizo ki koma gidanki.”
Jita yi kamar zata yi kuka don ɓacin rai, to amma ya zata yi? Haka dole ta wuce ɗaki tana shiga ta rungume Hadiza dake zaune akan kujera banda hawaye babu abinda suke yi, Umma tana gamawa ta shigo ta kallesu tace “Ku tashi ku koma gidajenku tun kafin ku sake samun saɓani da mahaifinku tunda mai kare mana gaba ɗaya kunga yadda Allah yayi mana dashi.”
Maryam ji take yi kamar zata yi hauka, babban baƙin cikinta duk kudin mijinta ace babu abinda zata iya yiwa ɗan uwanta? Ita yanzu account ɗinta ko dubu biyar babu tasan kuma tana yin magana uban mijinta zai fara zancen shima yana buƙatar ganin likita, kuma in tace a ɗauki mai kula dashi tasan kai tsaye ma zasu ce babu kuɗi, haka suka yi mishi sallama suka tafi don ko tanka musu bai yi ba yana kallonsu dai har suka bar ɗakin.
Baqeer har Salim ya bar gidan bayan ya gama yi mishi duk wani abinda yasan zai bukata bai ce ko kalma ɗaya ba, sai da Salim yazo yi mishi sallama ne ya kalleshi yace “Salim nagode!”
Cike da tausayi ya jinjina kai yace “Bello yazo?”
Kai kawai ya girgiza alamun a’a, jiki a sanyaye Salim yace “Naji ance baya nan kenan da gaske ne abinda naji.”
Kallonshi yayi alamun tambaya nan Salim yace “Ban san ina yaje ba na dai ji Habi na maganar ne da muka yi waya.”
Kai ya ɗaga nan ya sake yi mishi sallama ya fita, Baqeer na nan a zaune yana kallon Kamalu ya shigo yana ƴan waƙe-waƙenshi, ko kallon inda Baqeer yake bai yi ba ya gama abinda yake yi ya ciro doya da kwai daya siyo da juice ya shanye sannan yayi miƙa a kan katifa, shiru ne ya ratsa ɗakin don Baqeer ya ɗauka ma Kamalu yayi bacci ne sai ji yayi yace “Yanzu ya kake ji? Gashi dai kai ne ɗan gata ga kuma halin daka tsinci kanka a ciki, ko banza ni ina da kafafuna, ko da ba’a barni nayi karatu saboda kai ba ina da lafiyata wanda kai yanzu baka da ita.”
Idon Baqeer na kanshi sai dai bai tanka mishi ba, zama Kamalu ya miƙe yayi yace “Ka cigaba da zama kamar kurma a ɗakin nan dan in har kana son zaman lafiya da ni to tabbas ka bini yadda nake so don wallahi haushinka da nake ji na shekara da shekaru wannan ciwon naka ba zai saka ya goge ba balle ya hanani tafka maka rashin mutunci.”
Chapter 21 · 0% Book details