Sashe 76
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*******
Bello tare suka je Abuja da Asiya wurin visa ɗinshi, a jirgi suka je zasu yi a ranar su dawo, tunda suka je Abuja suke yawon restaurant bayan an gama application ɗin babu abinda take yi sai ɗaukan pictures tana ɗaurawa a IG ɗinta, suka sayi zobe iri daya suka saka sannan tayi caption a ƙasa wai ‘His wife!’ Nan fa kan Bello ya ƙara fasuwa don tabbas yana son Asiya, bayan sun dawo sun je gidan da zata zauna ƙaton apartment ne, don su mahaifiyarta da Habi da suka zo ganin gida sai baki suka sake,
Habi tace “Asiya ina Bello yaga kuɗin biyan wannan ƙaton gidan?”
Wani mugun kallo ta zabga mata tace “Bana jin wannan damuwarki ce ke dai kiji da naki ruɓaɓɓun samarin in kuma kishi kike yi to.”
Dariya Habi tayi tace “Akan me zan yi kishi ni kuwa? Bayan banga abin kishin ba?”
Fusata Asiya tayi tace “Ke in baki gani ba ni na gani.”
Ran Habi ne ya ƙara ɓaci tace “Ko banza dai Baqeer yafi shi komai wallahi kuma dai a dinga tsoron Allah.” Tana kaiwa nan ta fito cike da ɓacin rai, ita ma Asiya takaicin Habi ne ya hanata binta, kwanan nan sam basa jituwa, to dole ne? Tace bata yi da Baqeer in ita ta damu taje ta aureshi mana. Nan tayi tsaki ta sanarwa iyayensu akan wai taje wani wurin, su kansu mamakin gidan ya ishesu Baban Asiya yace “Gaskiya ba zai iya gyara ɗaki uku ba shi ko biyu ma ba zai iya ba don haka ɗaki dayan nan da falo kawai zai gyara in su suna da hali nan gaba sayi amma ba zai kwashe komai yayi mata kayan ɗaki alhalin Habi na tasowa ita ma.
Kalmar nan ta ƙonawa Asiya rai tace “To ita a kwashe ayi mata in yaso in auran Habi yazo ita zata sa Bello yayi mata.”
Shi dai yace a’a babu ruwanshi da wannan gangancin, da haka suka fito ta rufe gidan ranta duk ya gama ɓaci don ita gaskiya kayan ɗakin da take so masu tsada ne tafi so a zo biki kowa ya koma da mamakinta a ranshi, dole tasa Bello yayi mata wani jeren amma ba za’a zubar mata da class ba haka kawai.
******
Baqeer kam har ya isa gida ƙasan ranshi wasai ko banza ya san Junaid yau yaji a salansa, haka yayi ta duba wayarshi amma babu message akan designs ɗin daya ɗaura, sake gyara profile dinshi yayi akan duk hotunan da ya saka basu zai bada ba sai dai duk da haka shiru har ya kwanta yayi bacci.
Kallon rose ɗin dake hannunta Zee tayi ta saki murmushi tace “Muje muga Dad ɗinki?” Tayi maganar tana rufe fuska sai kuma ta saki huci tace “Me kike tunani?” Cikin ranta tace “Yanzu kamar ni one sided love nake yi?” Tasa mayafi a kanta tasa rose ɗin a cikin jakarta, kan gadonta ta kalla yau Nabeela bata shigo ba, ta fito tana kiran mai aiki akan ta gyara mata, Mummy ce ta fito daga ɗaki ita ma da alama fita zata yi don ta shirya cikin lace tsadadde, rungumeta Zee tayi Mummy ta shafi bayanta tace “Baby ni kam kwanan nan lafiya kike? Kullum sai dai na ganki da kayan mu na gida?”
Murmushi tayi tace “Ya zanyi Mummy? Ni kaina ban san ya aka yi na koma haka ba.”
Kuncinta taja tace “Yafi son kayan gida ne?”
Cike da kunya ta shige jikin Mummy tace “Hmm duk da ban san yanzu ko ya canza ba.”
Kallon mamaki tayi mata tace “Kin san shine da?”
Laɓɓanta ta haɗe tace “Labari ya banu.” Tayi maganar tana juya kai, Mummy tace “Nima zan fita ne akwai abinda zan siyo Daddynki matar abokinshi ta haihu zan je barka.”
Kai ta ɗaga alamar to sannan tace “Aunty Nabs fa?”
“Wallahi ban sani ba, bari naje kafin nayi yamma.”
Nan ta fito ita kuma ta leƙa Nabeela, tana kwance cikin bargo tana daddanna waya, Zeey ta buɗe tana kallonta tace “Aunty Nabs? Meke faruwa?”
Kai ta girgiza alamar babu komai kafin tace “Kawai bana jin tashi ne yanzu.”
Maimakon tace wani abu kawai ta maida ƙofar ta rufe ta fito ta shiga mota, a hanyar fita mai gadi ke bata labarin yaron nan ya sake dawowa ya bashi kayan amma yace ba zai amsa ba. Shiru tayi tana tunanin me zata yi mishi, don duk ranar da Daddy yasan ana biyota har gida lallai ranta ne zai ɓaci.
“Yaushe yazo?”
“Mai gadi ya ɗan kalli waje yace ai bai ma dade ba don in na fita a guje ma zan ganshi.”
“Zaka tuna kayan da yasa?”
Ya ɗan yi dariya yace “Shadda ce taji jiki daga ruwan sararin samaniya ta koma wata kalar daban.”
Ta kula neman magana mai gadin yake ji dashi hakan yasa tace “Bani kayan.”
Da sauri ya miƙa mata tasa a gefe sannan ta fita, da ɗan sauri take tafiya, a gefen wani saurayi tayi parking, kallon motar yaiy garin mamaki saura ƙiris ya faɗi ƙasa, da sauri ya riƙe gefen motar yana haɗiyar yawu yace “Roshni?”
“Kana da sana’a ne?”
Sumar kanshi ya fara shafawa yana ɗan gyara tsayuwa yace “Eh mai gidan mu nada shago.”
“Hmm da alama, hope ba satowa kayi ba?” Tayi tambayar tana nuna mishi ledar, yayi ɗan yi yaƙe yace “Roshni ya kike haka?”
Fuska ta tamke sosai sannan ta miƙa mishi. Kamalu kamar zai yi kuka yasa hannu ya amsa, sannan ta kalleshi tace “Sata dai sata ce sai a canza hali.” Tana kaiwa nan ta mayar da glass na motar tayi gaba, da kallo yabi bayan motar sam kasa motsi yayi, da ƙyar ya iya jan ƙafarshi zuwa gida, sam ya manta ledar dake hannunshi ya shiga.
Abu ta leƙo waje don ta zubar da shara ta ganshi, sam bai ji maganar da take yi mishi ba yana tafe kamar ba shi ba, mamaki ne ya rufe shi tasa hannu ta riƙo ledar tana cewa “Kamalu lafiya kake ina magana ba ka ji?” Tayi maganar tana riƙe da ledar, jan jikin da zai yi sai ledar ta yage, atamfa ce ta faɗo, ido ta zaro da sauri tace “Kamalu ina ka samo ta? Ba dai a shagon Babanka ka ɗauko ba?”
Sai a lokacin ya kalleta ya kalli atamfar, Abu da sauri ta ɗauka ta ɓoye tayi ɗaki da ita ta samu wuri ta ɓoye a ƙasan gado, tabbas tun kafin ta janyo wa kanta da yaranta magana gwara ta ɓoye a inda ba za’a gani ba.
*******
Yana zaune a ɗaki ya zuba wa wayarshi ido anya kuwa za’a dace? Kai ya girgiza da sauri ai komai haƙuri ake yi dashi ba zai yiwu abu kwana biyu ba jikinshi ya karaya, idanun ya ɗan runtse, Zee ya gano tana yi mishi smiling, shima murmushin yayi a bayyane nan ya ɗauko takarda ya fara zanen ɗinki, yana cikin yi yaji Dada tana lale lale da yar albarka.
Kofar ya ɗan kalla yace “Da kullum sai tazo yanzu kuwa sai bayan kwana bibbiyu.”
Bai motsa daga inda yake ba sai dai hankalinshi gaba ɗaya yana waje, mamaki ne ya kamashi ganin tafi minti goma da zuwa amma har yanzu ko Dada bata ƙwanƙwasa mishi ƙofa ba, gani yayi haƙurinshi ya ƙare yasa ya wawwaiga ɗakin, kwanon da yaci abinci ya ɗauko ya gunguro kekenshi ya fito “Dada kina ina?”
Abinda ya fara cewa kenan.
Ido suka haɗa da Zee dake zaune akan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ta zuba mishi ido, gyaran murya yayi yace “Dada fa?”
“Kawai?”
Turo keken yayi zuwa cikin falon yana kallonta yace “Yaushe kika zo?”
“Yaushe jikinka ya baka?”
Kai ya kauda tasan tunda yayi haka ba zai amsa ba, tana murmushi tace “Faɗa mini Ya Baqeer in banzo ba kana damuwa?”
Kallonta yayi nan da nan idanuwansu suka ɗan sarke da juna yana mamakin yadda mace bata kunyar magana haka.
Kai ta karkatar tace “Baka yi?”
Nan ma bai ce komai ba sai dai yanzu ya ɗan canza yanayin kallon da yake yi mata, neman juyawa yayi da sauri ta rike handle ɗin keken, hakan yasa ya tsaya, juyo da keken tayi inda zai ganta sosai tace “Baka bani labari ba kaje wurin J ɗin?”
Kallon da yayi mata ne yasa ta gane me yake nufi tace “Ya plan ɗin school din?”
Waya ya ɗauko ya buɗe mata page ɗinshi na IG mai ɗauke da sunan ‘MOHBAQ’ da yanda ya tallata abun, daɗi ne ya kamata da sauri tayi following ɗin shi, tace “Ko nasa kayan da aka ɗinka mini sai nayi pic daga wuya ne kasa sample?”
Wani mugun kallo yayi mata, ita ma dama tayi ne don ta gwadashi, tace “Inyi?”
Yanda yake mata kallo ne yasa ta shagwaɓe tace “Me kuma nayi? Ni sarkin laifi?”
Kai ya kauda ranshi ya ƙara ɓaci wai tama san me take cewa kuwa?
Langaɓar da kai tayi tace “In baka so ba gwara kace a’a ba da kayi shiru, menene a ciki?”
Waigowa yayi yace “Na saki?”
“Wai so nake yi ka sakani.”
Jan keken ya fara ƙoƙarin yi tayi sauri ta ƙara riƙewa tace “Naji na haƙura, shikenan? Amma fushin na menene daga tambaya?”
Shima tambayar kanshi yayi fushin na menene? Anya Baqeer? Yayi soyayya da Asiya amma bai taɓa jin abinda yake ji akan Zeey ba bayan ya daɗe da ita ya kuma so ta kowa ya sani.
Dada ce ta shigo falon hakan yasa ya juya, Zeey da kallo ta bishi tana murmushi.