← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 168

Sashe 18

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*****
A guje Mummy ta rungume Zeey cikin tsananin murna itama ta ƙanƙame ta, Nabeela dake gefe tana kallonsu ta girgiza kai tace "Aunty na ɗauka kunnenta zaki ja? Kinga abinda ta yiwa guy ɗin nan kuwa?"
Hararar Nabeela tayi tace "To kanwa uwar haɗi, har wani abu ma nayi mishi?"
Mummy zata yi magana suka ji ana kwallawa Zeey kira cikin magana mai sauti, Kabir ne shiyasa basu wani ɗagawa kansu hankali ba har ya ƙaraso, kallonta yayi cike da masifa yace "Kina nufin abokina kika yiwa kallon driver? Kika wulakantashi a gaban mutane? Kalli..."
Yayi maganar yana nuna mata wayarshi inda da alama wasu ne suka ɗauki video ɗin abinda ya faru suka watsa a social media.
"Calm down bro, meye kake exaggerating ɗin abun haka wai? Chill out!"
Takaici ne ya sake rufeshi yace "Kinsan Allah zan zabga miki mari, ina miki faɗa kina cemin wani chill out?"
"To chill in shikenan?"
Kallon Mummy yayi yana ji kamar ya shaƙota ya zabga mata mari, Mummy ta ɗan murmusa tace "Ya haƙuri Kabir am sure ba da saninta tayi ba, kayi haƙuri kaji? Kema bashi haƙuri."
Huci Zeey ta saki kafin  tace "S" Kabir ji yai kamar yayi hauka don takaici, a fusace ya bar parlourn yasan shi kenan yanzu zaman gidan zai fara bashi haushi don sam yarinyar nan ta gama rainashi.
Harararta Mummy tayi tace "Me kika yii haka?"
Tace "Ban fa sani ba, na ɗauka driver ne."
Daga waje suka jiyo shigowar motar Dad cike da jin daɗin dawowar Zeey.

A ɓangaren Bello kuwa tunda ya samu aka kirashi zuwa wajen deputy gwamna gashi har an mayar da sunanshi a madadin na Baqeer a matsayin wanda zai wakilci Jihar Kano a wajen gasar da za'a yi yake murna. Shi dai kam yasan kakarshi ta yanke saƙa, ya taki sa'a irin wacce bai taɓa zaton zai samu ba a rayuwa, wannan accident ɗin na Baqeer ai shi aka yiwa don a komai Baqeer ɗin na gabanshi gashi yanzu cikin ruwan sanyi ya samu abinda ya daɗe yana mafarkin samu. Fifikon da Baqeer yayi mishi na matuƙar baƙanta mishi zuciya ganin dai harkar zanen duk ita suke yi hasali ma ita ce ta fara haɗa su abota sai dai kafin a ambace shi a waje sai an fara kiran Baqeer kafin a ambace shi sau ɗaya an ambaci Baqeer sau babu adadi, duk wani alheri daya tunkarosu to wajen Baqeer yake fara zuwa kafin su, a komai sai dai ya samu sauran Baqeer, abinda yake baƙanta zuciyarshi don a ganinshi Baqeer bai fi shi da komai ba sai tsantsar sa'a da tsayayyen uban dake tayashi wajen faɗi tashin ganin ya cimma burinshi.

Shirye-shiryen tafiyarshi Abuja kawai yake yi inda anan ne za'a yi gasar da za'a zaɓi waɗanda suka yi nasara a ɗauki nauyin faɗaɗa karatunsu a harkar zane a ƙasashen ƙetare. Yana ta shirin shi ba tare da ya bari wani daga cikin abokansu yasan shi zai tafi a madadin Baqeer ba don baya ma so kowa ya sani har sai yaje yayi abinda ya kaishi ya dawo inda yake fatan nasara ta zama tashi, a lokacin ne zai nunawa duk masu cewa Baqeer yafi shi da masu cewa baya iya yin zane sai da taimakon Baqeer ko shi waye, a lokacin zasu yi dana sanin wulaƙanci da cin fuskar da suka yi tayi mishi suna nuna mishi iyakarshi suna ganin shi ba kowa bane.

*****
Har aka kwana biyu Baqeer na ƙunshe a ɗaki baya fitowa ko tsakar gida bare ya fita waje dama kuma yana da banɗakin shi a cikin ɗaki don haka ya ƙara takure kanshi da zaman ɗakin don sosai yasa maganar Baba a ranshi ta kada ya ƙara ganinshi a waje don kada mutane su ganshi ayi mishi dariya. Inda Allah ya taimaka ma kullum Salim ke zuwa safe, rana da dare yana taimaka mishi wajen turashi zuwa banɗaki ya taimaka mishi yayi wanka da duk wasu ƴan buƙatocin shi dai amma haka Salim zai zo ya ƙari maganarshi Baqeer ba zai ɗaga kai ya kalleshi ba bare ya tanka mishi sai dai ko kusa hakan bai taɓa damunshi ba sosai yake yi mishi uzuri tunda yasan da can ba haka yake ba yanayi ne kawai ya mayar dashi hakan.

Yau Umma na wankin kayanta dana Baqeer da suka yi datti, wankin da a baya ta manta yadda ake yi don kayanta na yin datti Baqeer zai haɗa ya fita dasu sai dai ya kawo mata a wanke a goge iyakaci ta shirya a cikin wardrobe amma gashi yau kuɗin sabulun da zata yi wankin ma da ƙyar ta samu Baba ya bata bayan ya gama sauke mata kwandon tijara akan shi fa ba zai iya da tsirfarta ba idan ma zata nemi abun yi gara ta nema don bai ɗaukewa sauran matan shi sabulun wanki dana wanka ba ba zai fara a kanta ba.

"Umma yau da kanki kike wankin da tsakar ranar nan? Ina Yaya Baqeer ɗin bai samu ya fita dasu ba?"

Jin maganar yasa ta ɗaga kai tace "Hadiza? Yau kece da safen nan?"
Shigowa tayi tana sallama Hadiza, ƴarta ta biyu ce  wacce ke bin Baqeer, tana shigowa tana cewa "Umman mu abin ne ya bani dariya kece da wanki?"
"Da kaina nake yi Hadiza, ku shiga daga ciki yanzu zan ƙarasa na shigo nima."

Bata shiga cikin ba sai ma saka hannunta da tayi a bokitin wankin tana cewa "Kawo na ƙarasa miki Umma ki zauna ki huta kema."

"To kuma daga zuwanki ko zama baki yi kin huta ba sai ki kama wanki?"

"Idan ban yi miki ba Umma wa zan yiwa, don Allah ki bari na ƙarasa, gashi naga ma ƙarashe ne wankin naki." Haka nan ta sakar mata kayan ta ɗauki jakarta da ƙaramar ƴarta data yaye suka shige ɗaki, sauran abincinta na safe ta ɗaukowa yarinyar ta zauna tana bata a baki kamar tasan da zuwansu dama. Ai kuwa yarinyar ta ware ciki tana cin abinci sai kace kuncen yunwa, tas ta cinye abincin duk kuwa da yana da ɗan yawa, ita kanta Umman tayi mamakin yadda yarinyar ta cinye abincin tas ga alama daɗaɗɗiyar yunwa ce a jikinta, ganin ta fara gyangyaɗi yasa ta miƙe ta ɗebo ruwa ta bata ta sha sannan tasa zani ta goyata, kafin wani lokaci har bacci ya ɗauketa. A daidai wannan lokacin Hadiza ta shigo, ganin ƴarta a baya yasa tace "Wannan ƙatuwar yarinyar kika goya Umma salon ta saka miki ciwon baya?"

Harararta tayi tace "Ina abun girma a wannan ƴar yarinyar da bata haura shekara biyu ba banda dai lalaci da yayi muku yawa ba kwa son goyo." Zama tayi akan doguwar kujera ƙwaya ɗaya dake ɗakin Umman wacce Baqeer ne yasa aka yi mata ita tana dariya.
"Umma ina yini?
"Lafiya lau Alhamdulillah, duk ƙalau kuke? Ya yaran?"

"Lafiya ƙalau Alhamdulillah, kwana biyu bamu gaisa ba gashi ni wayar tawa akwai da babu sunanta ina ta roƙon ya bar ni nazo ya hana sai yau Allah ya nufa ya barni nazo a hakan ma wai kada na kai yamma, Allah yasa dai Yaya Baqeer na nan don ina son ganinshi." Kallo ɗaya zaka mata kasan cikin damuwa take, gaban Umma ne ya ɗan faɗi, Allah dai yasa ba wani abin bane mai girma itama tazo dashi?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

#Baqeer
#Shalele
# RayuwadaKaddara
#Hawayena
#UMMASGHAR
#AYUSHERMUHD

Umm Asghar Ce
Da
Ayusher Muhd

*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*

*DADANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA BIYU*
Chapter 18 · 0% Book details