Sashe 85
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Baqeer ya samu ya fara zuwa tailoring school ɗin, kullum da safe Tanimu yake zuwa ya turashi zuwa bakin titi inda zai tarar musu adaidaita su tafi Makarantar, daga baya ma sai ya nemi wani mai adaidaitan ɗan nan unguwar suka yi ciniki kullum shi yake zuwa ya ɗauke su ya kai su can makarantar idan lokacin tashi yayi yaje ya ɗaukosu ya dawo dasu gida. Sosai Baqeer ya mayar da hankali akan koyon ɗinkin, matsala ɗaya da yaci karo da ita shine da aka ce dole sai sun koyi ɗinki akan normal keke kafin su fara akan mai aiki da wutar kasancewar shi me matsalar ƙafa duk da a yanzu ya fara iya motsata kaɗan-kaɗan saboda physiotherapy session da suke yi da Junaid ga kuma exercises ɗin da koyaushe yake yi a gida, a hankali a hankali ya fara iya motsa ƙafar saɓanin da da baya jin alamun ta ma a jikinshi, a yanzu ya fara jin feelings a wurin sai dai ba zai iya sarrafata yayi kowane irin amfani da ita ba. Duk da wannan matsalar daya samu ta rashin iya taka keke da kanshi duk da buƙatar hakan da ake yi wajen koyon ɗinkin ya mayar da hankalinshi ƙwarai wajen iya sarrafa almakashi don sosai ya ƙware a iya yanka ya kuma iya fitar da designs masu kyau, ɗinkin ma yana gwadawa akan electric machine ɗin tunda ba zai yiwu yayi akan manual keken ba.
Wani abun burgewa da yayi shine daya saka Tanimu a makarantar koyon ɗinkin tunda ya nuna sha'awarshi ga ɗinkin sai ya biya mishi duk kuwa da tsadar kuɗin makarantar tunda dama tare suke zuwa yana taimaka mishi da ƴan ƙananun abubuwa irin su taimaka mishi ya hau kan kujerar wheelchair ɗin shi da turashi zuwa duk wani wuri da zai je haka a cikin makarantar ko zuwa mishi aiken sayen wani abu na daga kayan ɗinki haka. Duk da har yanzu mutanen can basu ƙara waiwayarshi da batun contract ba da ɗan abinda yake samu daga zanen da yake yiwa Sani tela ya ɗauke nauyin duk wasu buƙatun shi dana mahaifiyarshi da ƴan uwanshi, da yake yanzu akai-akai Sanin yake zuwa yana sayen zane a wurinshi. Har yanzu dai Sanin ne kawai wanda yake yiwa zane yana biyanshi amma dai Alhamdulillah yana samu bakin gwargwado tunda bai nemi komai ya rasa ba, duk wani abu da yasan zasu buƙata yana ƙoƙarin ganin ya ajiye musu shi, haka nan Umma kullum cikin yi mata aiken kuɗi yake ita da ƴan uwanshi Hadiza da Maryam. To itama Hadizar ga yadda yake ji tana samun rufin asiri da injin markaɗenta don haka ya ƙara samun kwanciyar hankali tunda yasan a yanzu basu da wata gagarumar matsala a rayuwarsu.
*****
Yau tun safe suke zuba lissafi suna tusawa, ya rasa inda kuɗaɗen shi suke tafiya kullum a maimakon ya cigaba sai baya yake ci ga wasu ƙananun sata da ya rasa wanda yake yi mishi a cikin yaran kantin nashi, duk wasu matakan tsaro daya sani ya zuba musu amma har yau ya kasa dacen kama ɓarawon da yake yi mishi sata. Akwai ranar ma da har an gama ciniki da wata mata da tazo sayen atampopi sai da aka zo saka mata a leda guda ɗaya tace ɗaukeni. Haka aka yi ta nema ba'a gani ba sai wata aka ɗauko aka bawa matar shi kuma yana ji yana gani ya ɗauki asara don kowa yace bashi bane ya kuma rasa ta yadda zai yi ya fitar da ɓarawon daga cikin yaran shagon nashi. Haka nan dai ya haƙura aka gama lissafin ya ware kuɗin da za'a zuba wasu kayan, sai yaga ɗan abinda ya rage mishi bai taka kara ya karya ba gashi kuma dole ya biya ma'aikatan shi hakkinsu. Haka nan ba don yaso ba ya biyasu albashin su ya tattare ɗan abinda ya rage ya tafi gida yana huci kamar yana fatan wani ya shiga gonarshi ya huce takaicin shi a kanshi.
Tun daga ƙofar gida yake surfa ruwan bala'i akan tumakin maƙwabta da suka yi mishi kashi a ƙofar gida, yana shigowa tsakar gidan yaci karo da bokitin ƙarfen Jamila a tsakar gidan, ƙafa yasa yayi ball dashi yana masifa akan don me za'a ajiye bokiti akan hanya salon yayi tuntuɓe ya faɗi idan yaji ciwo basu da asara.
Daga Jamila har Abu tsayawa suka yi suna kallonshi babu wacce tasa mishi baki, a yadda suka ga ya shigo ɗinnan sun san idan suka ce zasu yi magana idan ransu yayi dubu sai ya ɓaci don sun daɗe basu ganshi cikin tashin hankali irin na yau ba sun san dole akwai abinda ya ɓata mishi rai a waje sun san cewa idan suka saka mishi naki a kansu zai huce su kuwa babu wacce ta shiryawa tijarar shi ta fama da idan ya fara baya jin yi haƙuri idan aka bashi haƙuri shi kamar ana turashi ya ƙara ruwan tijarar da yake yi.
Fatima ce me girkin ranar tana jin shi yana faman tijararshi bata fito ba sai da taji shigarshi ɗaki sannan ta fita ta haɗa kayan abincin shi ta ɗauka ta nufi ɗakin nashi dasu. Da sallama ta shiga ɗakin cikin nutsuwarta data zame mata jiki. "Sannu da dawowa Mallam," tace tana ajiye tiren abincin a gabanshi. Wani irin kallo yayi mata idonshi cike da fitina yasa hannu ya buɗe kwanukan abincin nashi sai yaga tuwon masara ne da miyar kuka. Watsi yayi da kwanukan ƙiris bai sameta ba tayi sauri ta kauce kwanukan suka watse anan tsakar ɗakin. "Mallam lafiya kuwa?" Tace tana kallon ɓarnar da yayi a tsakar ɗakin tana jin takaicin wannan wulaƙanci na Badaru, yanzu abincin da wasu suke can suna nema basu samu ba shine shi ya samu don wulaƙanci ya zubar. Nuna abincin yayi da yatsa yace "Miye wannan?" Yana bin miyar data kwanta a tsakar ɗakin da wani irin mummunan kallo kamar wanda yaga kashi. Kallon miyar itama tayi yadda ta kwanta a ƙasan ɗakin sannan ta ɗago ta kalleshi sai dai bata ce mishi komai ba tsabar takaici.
"Ke dai Fatima wallahi kin yi asara, baki ji daɗin rayuwarki ba wallahi sam uwar baƙin ciki da mugun hali, abincin ma don mugun hali kin daina tsayawa ki girka mai kyau sai dai ki kwaɓa mana shi duk yadda ta raya miki." Hannu tasa ta tattare kwanukan ta haɗasu wuri ɗaya kafin tace "abinda ka kawo ai shi zaka gani, da ɗin ma da nake yin irin wanda kake so ai ba da cefanenka nake yi ba ka sani Baqeer ne ya ɗauki nauyin yin cefane yanzu kuwa daka koreshi kaga dole ayi da iya abinda ka kawo kawai tunda mai kawowar baya nan."
A fusace yace "Yauwa ga maganata nan ta fito, kawai dama kice kina baƙin ciki don nace nakasashen ɗanki ya fita ya bar mini gidana shine kike nuna mugun halinki a abinci ba kya tsayawa kiyi shi da kyau kamar da, to sai dai mugun halinki ya ƙare a kanki, ɗanki ne dai ya bar gidan nan har abada kuma ban yafe dukiyata da lokacina dana ɓata a kanshi ba wallahi in dai baza ku biyani abinda na kashe ba." A razane ta ɗago kai ta kalleshi tace "Baqeer ɗin kake yiwa Allah ya isa kamar ba ɗanka ba Mallam? Wannan wacce irin rayuwa ce da bawa bai san ya karɓi ƙaddara ba, shi ya ɗorawa kanshi ne ba Allah ne ya ɗora mishi ba."
"Oho dai wannan kuma ke kika sani, ni dai a biyani kuɗina idan ana son zaman lafiya dani ato." Tashi tayi kawai ta kwashe kwanukan tace "Allah ya ganar da kai Mallam amma In Sha Allahu sai kayi alfahari da haihuwar Baqeer." Tsaki yayi yace “Wa? Nakasashen ne zan yi alfahari dashi?” Bata ƙara kulashi ba ta fice ta bar ɗakin, ajiye kwanukan tayi a wajen wanke-wanke ta shige ɗakinta tana jinjina rashin tawakkali irin na Badaru da har yau ya kasa yarda da ƙaddarar data samu Baqeer.
*****
Tunda satin bikin ya kama Asiya ta kasa zaune ta kasa tsaye don kuwa biki ne suke shiryawa na ƙarya irin wanda za'a daɗe ana labari. Events ma wajen kala biyar suka tsara za'a yi kuma duk Bello ne ya ɗauki nauyi koda yake ina iyayenta suka ga kuɗin da zasu yi mata irin wannan bikin na ƙarya. Duk wani ɗan abinda Bello ya mallaka ya shige a cikin sabgar bikin nan sai dai bai wani damu ba ganin ya kusa barin ƙasar yasan daga inda yaje ya fara aikin paintings ɗin shi shikenan zai mayar da fiye da abinda ya salwantar a wajen harkar bikin. Bayan kayan lefe da yayi mata duk wasu kaya da zata saka na fitar biki shi ya ɗinka mata tsadaddu don tace ai abun kunya ne a ga tayi kwalliyar biki da kayan lefenta sai ma ƙawayenta su raina ajinta a cewarta. Da bridal shower aka fara taron bikin inda Bello ya kama mata wani restaurant anan kusa da unguwarsu, duk wani abinci da aka ci a wurin taron restaurants ɗin ne suka basu. Haka event ɗinnan yayi ta yawo a social media, abinda ke ƙara sawa Asiya taji kamar kanta zai fashe don girma, tana ganin itama yanzu ta faso gari lokacinta ne yayi da zata shana tayi rayuwar ƴanci rayuwa irinta ƴaƴan masu kuɗi kamar yadda take da buri. Haka duk wani event da aka yi a bikin yayi ta yawo a social media har aka yi ɗaurin aure. A irin hotunan ne Baqeer yaci karo da hoton ɗaurin auren inda aka ɗauke su Bello ya rungumo kafaɗarta suna fara'a, duk da yanzu ya ajiyesu a gefe ya daina saka damuwarsu a ranshi sai da yaji wani abu ya mintsine shi a zuciya, a tunanin shi ko kowa zai yi mishi butulci bai kamata ace har da Bello ba bayan irin taimakon da yayi mishi a rayuwa.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000