Sashe 58
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Kamalu dake ta shiri zai fita ya fito yaga Baba na zabgawa Hadiza faɗa shi abun dariya ma ya bashi yayi waje yana fito don abinda babu ruwanka daɗin kallo gareshi.
Salim ya hango tsaye jikin mai baron sayar da yalo, kusa dashi ya ƙarasa yana tafiya yana cigaba da fito har yazo inda yake ya kalleshi yace “Kana dai da kuɗin yalon ko ba sata kazo yi ba?”
Cike da takaici Salim ya kalleshi kawai ya kauda kai, Kamalu ne ya kalli mai yalon yace “Ka tabbatar ya baka kuɗin ka don ɓarayi ko a ina suke sai sun nuna halinsu.”
“Wai ni kam Kamalu meye damuwarka dani?”
“Damuwata ka fita hanyar Roshni yanzu ma can zani zance ko baka ga gayun da nayi bane? Irin babban yaro da babbar yarinya ba wai kai maloho ba, sannan ka sanar da abokinka yazo ya kwashe tsohuwar shi da ƙanwarshi dan tsoho ya sallamasu.”
Gaban Salim ne ya faɗi hankali a tashe ya riƙoshi yace “Me kake nufi?”
Fizge rigarshi yayi ya nunashi da yatsa yace “Wallahi kaji na faɗa maka ka shiga hankalinka dani inba haka ba na fasa ma baki.” Yana kaiwa nan ya ɗauki yalo ɗaya babu alamun zai biya kuɗin yayi gaba, haka Salim ya biya kuɗin haɗe da nashi, hankalinshi kasa kwanciya yayi tunda Baba na gida yasan bai isa yaje gidan ba don haka dole ya kira Baqeer ba don yaso ba.
Baqeer na zaune a ɗaki yana ta gwada exercise ɗin da Junaid ya koya mishi, ajiyar zuciya yayi a fili yace “Kamar wani yace ta kawo mana saurayinta har gida.”
Sai kuma yayi shiru tunda yasan taimakon shi aka zo yi, shi dai sam ya rasa me yasa zuciyarshi ke sake hango mishi Junaid da Zee tsaye kusa da juna, tsaki yayi ya cigaba da exercise ɗinshi, jin wayarshi na ƙara ya ɗaga da sauri ganin Salim ne.
Tun daga yadda Salim ya amsa mishi sallamar yasan akwai matsala, jiki a sanyaye yace “Salim wani abu ya faru ne?”
Kamar yace a’a sai dai yasan ba lokacin ƙarya bane in wani abun ya samu su Umma fa alhalin ya sani? Cike da sanyin jiki ya sanar dashi abinda Kamalu yace.
Hankalin Baqeer ba ƙaramin tashi yayi ba nan da nan idanunshi suka canza kala sosai, wayar ya kashe a fusace ya fara tura kekenshi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi, har ya gama sanin meya faru in dai Hadiza ce tayi yaji “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” abinda zuciyarshi kawai ke faɗa kenan, matsalar nan dai ta kuɗi ce yanzu kam ko aikin ƙarfi ne tabbas zai yi in dai zai fitar da ƴan uwanshi daga halin da suke ciki, wani yanayi yake ciki mai wuyar fassarawa, sam bai ji kiran da Dada ke kwaɗa mishi ba ganin yana tura keke yayi hanyar waje, ita kuma ganin bai dawo ba yasa ta ɗauka fitar da yake yi kwanan nan ita ce yake son sake yi, hakan yasa ta koma ta cigaba da aikinta tana cewa “In zaka fita ai ka sanar mini banda dai Baqeer kai ma halinka sai kai.”
Baqeer huci kawai yake yi, yau tana daga cikin rana mafi muni da wannan rashin ƙafar ta janyo mishi don gashi a titi amma bai san me zai yi ba.don duk hannun da yake ɗagawa babu mai adaidaitan daya tsaya mishi, waigawa kawai yake yi idanuwanshi na sake yin wani jaa, takaicin wannan rayuwar duk ta gama isarshi.
A hankali motar ta tsaya a gabanshi, kallon motar kawai yayi yasan ta wacece don kuwa ya ganta a ciki kwanan nan, sauka daga titi tayi tare da yin parking idanuwanta kawai ta samu suna zubar da ƙwalla, ta fito zata kawo ma Dada irin abin motsa jiki data sayawa Baqeer a daren jiya kawai ta hangoshi a titi, ita da tayi niyyar bawa Dada ta koma ba tare da ta ganshi ba sai gashi a titi gwanin tausayi, share ƙwallarta tayi sannan ta fito daga motar, bata ce komai ba har tazo kusa dashi, hannun keken ta baya kawai ta riƙe ta fara turawa, yanzu kam ta tabbatar akwai abinda zuciyarta ke auna mata akan Baqeer don sam idanunta neman cigaba da zubar da ƙwalla suke yi sai ƙoƙarin maidasu kawai take.
Shi kanshi Baqeer tunda ya ganta ya kasa magana, har wannan lokacin da take turashi kasa magana yayi, sai da suka bar kusa da titi yace “Zan iya.”
Bata tanka shi ba ta cigaba da turawa har suka shiga wani kwana da zai sada su da gidan Dada.
“Zan iya!” Baqeer ya faɗa cikin yanayi na jin haushin rayuwarshi, yanzu kam ya tabbatar yasan dalilin da yasa Asiya ta gujeshi.
Tsayawa tayi a ta bayanshi tace “Meya faru?”
Wani abu ya hadiya zuciyarshi na zafi yace “Ba komai.”
Cikin wata kasalalliyar murya tace “Ya Baqeer haka zaka cigaba da rayuwa?”
Damm gabanshi ya faɗi, Ya Baqeer? Yaji tasan sunanshi amma haɗashi da Yayan na menene? Don tana ƙawar Maryam? To amma damuwa dashi fa? Ko bai waiga ba muryarta cike take da tausayin shi.
Zeey kuwa ji take yi ina ma zata san yanda zata yi taga ya miƙe? Bata son ganinshi cikin wannan halin, zuciyarta zafi take yi……
Waigowa yayi ya kalleta itama idanunta ta sauke cikin nashi, idanunsa sun yi jaaa ita kuma idanunta ciki suke taf da ƙwalla dake ƙoƙarin saukowa saman kuncinta, wani yanayin kallo suke yiwa junansu ko wane da abinda yake ayyanawa a cikin ranshi.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA SHIDA*
{36}
Shi ya fara kawar da kanshi yana ƙoƙarin danne abinda yake ji yana neman taso mishi. Cikin dabara tasa hannu ta ɗauke ƙwallar data taru a cikin idanunta tana kawar da fuskarta daga kanshi itama tana mai jin kunyar dogon kallon da suka yiwa juna, hannu tasa ta cigaba da turashi har suka isa gidan Dada kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyarshi. Sai da suka isa ƙofar shiga gidan sannan ta saki keken ta gewaye shi ta shige cikin gidan ta bar shi anan, bin bayanta yayi da kallo yana mamakin yadda take neman shiga cikin rayuwarshi ta ƙarfi don a yanzu in har bai ganta ba sam baya jin daɗi. Tana shiga Dada dake zaune ta tadda a waje tana gyaran waken da zata yi musu fate, tana ganinta ta fara yi mata lale maraba fuskarta ƙunshe da fara'a don tayi wani irin sabo da Zainab ɗin da idan ta kwana biyu bata zo ba zata yita cigiyarta tana jin kewarta. Itama murmushin ta saki duk kuwa da bata cikin yanayi mai daɗi ta soma gaisheta. Hannu tasa tana tayata gyaran waken tace "Yau gidan shiru Dada, sai ke kaɗai?"
Kafin Dada ta buɗe baki ta bata amsa har ya gurguro kekenshi ya shigo gidan, bin bayanshi suka yi da kallo har ya shige ɗakinshi ba tare da ko kallonsu yayi ba, wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Zeey ta saki tana jin wannan baƙon yanayin yana sake ziyartar ta, taɓe baki Dada tayi tace "Ashe yawon naka ba mai tsawo bane, ai ni a yadda naga ka fice na ɗauka yau ma sai na ganka.”A surutu irin na Zeey a yau sai ta samu kanta da kasa amsawa Dada duk hirar da take yi mata har Dadan ta tambayeta "Lafiyarki ƙalau kuwa ƴar nan?" A ɗan firgice ta kalli Dada tace "Me kika gani?" Don duk a zatonta ko ta fahimci halin da ta samu kanta a ciki ne. Girgiza kai kawai Dada tayi tace "Ganinki nayi ba a yadda na saba ba shi yasa na tambaya ko ba kya jin daɗi ne?”
Dariya tayi duk don ta kawar da tunanin Dadan tace "Da a yaya kike ganina?"
"A yaya nake ganinki kuwa banda a yadda na sanki, sam ba'a raba fuskarki da walwala da fara'a gaki da yawan son barkwanci da hira yau kuwa duk kin yi wani sukuku dake tamkar ba ke ba shi yasa kika ji ina tambayar ko ƙalau kike.”
Ƙoƙarin danne wani abu da taji yana neman taso mata tayi cikin muryar dake ɗan rawa tace "Lafiyata ƙalau Dada kawai dai ƴan maganar ne basa kusa ina jin shi yasa kika ganni a hakan.”
"To Allah ya kyauta muku, kema kin koyi irin na Baqeeru kenan haka nan ana zaune dashi lafiya-lafiya gabaki ɗaya kuma sai kiga ya birkice sai kace wani mai jinnu.”
Dariya ta saki tace "Kai Dada, Ya Baqeer ɗin ne mai jinnu, maza dai yaji ki wallahi babu ruwana.” Dariya ita ma Dada tayi tace "Yo sai me idan yaji ni, ko a gabanshi ma sai na faɗa tunda dai ba tsoron shi nake ji ba.”
"To shikenan ni dai babu ruwana, ato.” Bata wani jima sosai ba ta tashi ta yiwa Dada sallama ta tafi, cikin zuciyarta ji tayi kamar ta leƙa ɗakin shi ta ƙara ganinshi sai dai kuma tayi wa kanta faɗa tace ki leƙa ɗakin shi kice mishi me? Don haka ta wuce ba tare da ko kallon ƙofar ɗakin tayi ba.
Shi kuwa har ta bar gidan yana jikin ƙofa yana sauraren su duk da rabin hirar ba jinta yake yi ba sai dai jin tana dariya yasa yaji wata irin nutsuwa na saukar mishi.