← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 168

Sashe 83

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

   Sun saka filin a kasuwa dan haryau dai mutanen basu ce komai game da contract ɗin Baqeer ba shima kuma yana tunanin in ya nemesu zasu ga kamar a matse yake, haka Salim yazo aka sa fili a kasuwa, Umma har sadaka tayi akan Allah yasa komai ya tafi daidai ya bawa Baqeer sa’a don ita kam kwanan nan rayuwa kawai take yi amma babu abinda ke faranta mata rai, a koda yaushe tunaninta yadda zata taimakawa Baqeer har yau tana mamakin yadda ko da wasa Badaru bai taɓa tambayarta Baqeer ba illa harkarshi kawai da yake yi, wannan abu na daure mata kai, wai mahaifi?
Yau tana zaune tana fanken sadaka, Abu ta fito da ƙatuwar leda ta ajiye a waje tana kiran Jamila, Umma ko kallonsu bata yi ba balle ta so sanin menene a ciki, Jamila ta fito tana kallonta tace “Saƙon Nusaiban ne?”
Abu ta ɗan kalli Umma ta gefen ido tace “Wallahi shine ai dai babu abinda yafi komai daɗi irin Allah ya baka ɗan da zai fitar da kai kunya, yanzu ke kiga abinda ta aiko mun, da ana yi mata kallon wacce bata dashi sai gashi yanzu tafi wacce tayi auran daɗi taimakon iyayenta.”
Dafata Jamila tayi tace “Yoo wai ba ita ce naji ana zargin uban miji na sintiri ba? Yayi shima ɗa yayi?”
Tsabar tashin hankalin da Umma ta shiga taje jefa fanke cikin mai sai ji tayi man ya ƙonata ashe hannunta ta kai kai, cike da tsoro ta kalli Jamila tace “Jamila ni kam kin san harshe yana daga cikin babban abinda ke kai bawa wuta ko?” Kallon Umma tayi tace “To ni dai ba dake nake ba balle kiyi mini wannan mumunan zaton, zance ne nake yi akan labarin da naji a radio, bana son sharri ban kuma san ayi mini ƙazafi.”
Abu tayi saurin fito da kaya tana cewa “Meye abun tsarguwa in har kun san kuna da gaskiya?“ Umma komawa tayi ta zauna tasa ruwan sanyi ta cigaba da suyar ta idanunta sunyi jaa, tabbas sai Allah ya yiwa Maryam sakayya, dama ya za'ayi uban miji ya zauna a cikin gida? Tasan ko ba daɗe ko ba jima wani sai ya faɗa musu baƙar magana akan hakan, da ƙyar ta gama suyar ta zuba musu ta ajiye sannan ta bada aka fita dashi. Tana shiga ɗaki Jamila tayi tsaki tace “Wai kuɗin kujerun ne har yanzu bata cinye ba?” Abu ta ɗauke kai tana duba atamfar da aka kawo mata, sai yanzu ma data kula taga mai arhace haushi duk ya isheta ta maida ita leda tana cewa “Inba su ba ina taga kuɗin kashewa? Bayan yanzu ficika Mallam baya bata?”
Nan dai suka cigaba da gulmace gulmacensu na hassada suna yi suna cin fanken.

*****
Yau Baqeer cikin farin ciki suka tashi don an samu mai siyan fili, an turo rabin kuɗin suka je shida Salim ya cike form akan zai fara zuwa, sun yi mamakin ganin gurgu da zuwa koyon ɗinki amma jin yace da keken electric zai yi yasa suka amince, sun yaba sosai da yanda duk da rashin ƙafarshi bai hanashi neman abinda zai taimaki kanshi dashi ba, Baqeer nada kyau sannan yana da cikar zati hakan yasa ko a baya mata ke sonshi, a yanzun ma in ba ganinshi aka yi akan wheelchair ba ba’a kawowa yana da nakasa, sun fito bayan sun yi registeration, ajiyar zuciya yayi ya kalli Salim wanda shima kallonshi yake yi kafin a hankali suka yi murmushi yace “Yanzu gobe zaka fara zuwa?” Kai ya ɗaga alamar eh yace “Zamu dinga zuwa da Tanimu kai dai ka cigaba da zuwa kasuwarka kafin na gama In Sha Allahu.”
Cike da gamsuwa ya jinjina kai yace “Hakan yayi amma ragowar kudin filin fa? Zan turoma yanzu.”
Kai Baqeer ya girgiza alamar a’a yace “ In har da hali yanzu muje bank mu buɗe wani account na saka a ciki ya zama na sana’a ne, bana son mu saka kuɗin a gaba kuma in na gama koyan muzo babu halin buɗe shagon.” Kallonshi yayi yace “Hakan yayi, mu je?”
Nan suka hau adaidaita sukaje bank na GT suka buɗe account aka tura ragowar kuɗin ciki sannan suka koma, a hanya ya turawa Umma, Hadiza da Maryam kuɗi daga cikin na fili, sannan ya turawa Salim, suka ɗan ƙaro abubuwan gida sannan suka dawo a gajiye gashi gobe zai fara zuwa school.
Sun shiga gida yana shiga tsakar gidan idonshi ya sauka kan Zee dake tsaye rike da ludayi, kallon mamaki yayi mata sannan ya kalli ludayin hannunta yayi mata sign da gira akan me take yi? Cike da sakalci tace “Oho, nima Dada tace na tuka mata wai tuwo.”
Ya kalli ludayin miyar dake hannunta sannan yace “Da wannan?” Ludayin tayi saurin ajiyewa tace “Ahh na manta bari na amsa waya tuntuni ake kirana, tayi maganar tana guduwa daga wurin, Dada ce daga ciki take cewa “Zainabu? Kin tuka?” Ta ƙarasa maganar tana fitowa daga ɗan store ɗin da suke ajiyar kayayyakin su na buƙata, ganin Baqeer tayi a zaune yana kallonta shima ta ɗan waiga tace “Tana ina?”
Alama yayi mata da ciki yace “Yaushe tazo?” Ta ɗauki muciya tana cewa “Dazu, kun cike fam ɗin?” Ya ɗaga kai yana shiga ciki, Zeey kuwa data samu ta gudu tana zama a kujera ta sauke ajiyar zuciya lallai tasha da ƙyar wai, me yafi wannan abun kunya in Baqeer yasan bata iya komai ba? Shigowa yayi ya ɗan tsaya gefen ɗakin shi yana kallonta, ita ma kallonshi tayi zuciyarshi na sake jin wani daɗin ganinta da yayi, kwantar da kanta tayi saman kujera tace “Shine ka tafi babu ni?” Wani kallo ya mata tayi saurin cewa “Bafa da wani abu ba amma da mun je tare, ko nima na shiga makarantar mu dinga zu……” kallon da yayi mata ne yasa ta turo baki ta sake maida kanta tace “Na haƙura to,” tayi maganar tana kallonshi. Ɗan murmushi yayi kaɗan wanda ya sata zuba mishi ido ita kam ya zata yi da son Baqeer? Ya dago yace “Sai kuma kice zaki shiga makarantar koyon ɗinki saboda me?” Har yanzu kanta na kan bayan hannunta akan hannun kujerar tace “Kawai!” Ya maimaita kalmar tare da cewa “Ban saki ba, kema ki duba abinda kike so kiyi.” Ji tayi cikin ranta tace “Kai ne ai.” Kallonta yayi jin kamar yaji alamun maganar ta amma bai ji komai ba yace “Me kika ce?” Da sauri ta zauna tace “Ban ce komai ba.” Kai ya jinjina zai yi magana sai ga Dada ta shigo tana cewa “Abu ashe kina ciki?” Tace “Waya aka yi mini daga nan kuma na zauna, au bari na tuƙa miki tuwon.” Tayi maganar cikin ɗan dauriya, nan tace “A’a yi zamanki ma don ni kam na riga na tuƙa ai, kada ki damu.” Ta kalli Baqeer tace “Kayan da Salim yasa a shigo dasu duk namu ne?” Kai ya ɗaga yana cewa “Eh.” Ta koma ta shigo da leda tana cewa “Wannan naga kayan shafe-shafe ne? Anya nawa ne ba na Zainabu ba?”
Ɗagowar da zai yi sai yaga idon Zeey a kanshi da sauri yace “Naki ne mana Dada.” Ta kalleshi tana cewa “A’a fa ban yarda ba ina ni ina shafa irin wannan man? Zainabu ba irin shi bane wanda kika taɓa shafa mini wani mai kalar manshanu?” Dariya suka yi, Zeey tana kallonta tace “Mugani.” Miƙa mata tayi Zeey tana buɗewa taga brand na man da take shafawa, hand lotion ɗin irinshi ne sak wanda take sawa a jakarta, da mamaki ta kalli Baqeer wanda yayi saurin shafar bayan kanshi kawai ya gurgura kekenshi yayi ɗaki, sam ya manta lokacin da suka siyo bai ɗauke shi ba daga cikin kayan, yanzu gashinan Dada ta gama bashi kunya don shi kam bai isa magana ba. Zeey kuwa murmushi tayi don ta tabbatar nata ne, sai ga Dada ta sake shigowa da wata ledar tace “Ahaf ni nasan wannan naki ne, kinga mai gurguwa gashinan nawa.”
Murmushi tayi tana cewa “Kila dai wannan ɗin ma ke ya sayawa.” Baki ta taɓe tace “Ni dai kam na bar miki in ma ni ɗin ce don ban isa  ba.” Har Zeey ta fito daga gidan Baqeer bai leƙo ba.
Chapter 83 · 0% Book details