← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 168

Sashe 60

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

   Da kallo yabi Dada tabbas tsanar kanshi duk ta isheshi, babu shakka shi ba kowa bane in babu zane, wace irin rayuwa yayi da bai dogara da komai ba sai shi? Idanunshi ne suka yi jaa yana tuno lokacin da yana yaro ko wasa zai fita waje Baba hanashi fita yake yi akan dole ya koma ɗaki yayi practicing painting tun yana shekara huɗu yake yi haka zai yi ta yin shirme amma Baba na yaba mishi a hankali yazo daya ƙara wayau ya fara zane abubuwa kamar dabobi da yake Allah ya bashi baiwa ga kuma Baba dake sakashi yi a koda yaushe yasa tun yana ƙarami hannunshi ya ƙware da yin zane, da ya shiga school kuwa bama a competing dashi don kowa yasan zanenshi ya fita zarra, a kuma nan makarantar ne suka haɗu da Bello wanda basu san unguwarsu ɗaya ba, yanzu shi me zai yi? Me ya iya? Hawaye ne suka cika taf cikin idanuwanshi nan ya haɗiye wani abu daya makale mishi a maƙoshi, yana jin zuciyarshi na wani irin zafi.
Idanuwanshi ya rufe, kalaman Zeey ne ke sake yi mishi yawo a ƙwaƙwalwa, dole yasan abun yi ba zai bar mahaifiyarshi da ƙannenshi cikin tashin hankali haka ba. Wayarshi ya ɗauka ya kira Umma.
Ringing uku ta ɗauka ganin sunan Hadiza wanda ya tabbatar mata da Baqeer ne, jiki a sanyaye yayi sallama, ta amsa cike da jin daɗi, muryarta na rawa tace “Ya jikin?”
Cikin dakewa yace “Da sauki Umma, komai lafiya?”
Ta sake daurewa tace “Komai lafiya Baqeer kai ne abun ji ai.” Zuciyarshi ce ta sake karyewa yace “Kada ku damu dani komai lafiya, ya wurin su Hadiza da Maryam?”
Umma tayi ajiyar zuciya tace “Suma duk lafiya ƙalau, Hadiza ma taso zuwa nace ta jinkirta don muzo tare.”
Wani yanayi ya tsinci kanshi a ciki ganin Ummanshi na ƙoƙarin ɓoye abu saboda shi, ya zai yi?
“Baba fa? Ya bar takura muku?”
“Kar ka damu da wannan Baqeer shima yanzu ya daina, ya Dada?” Yace “Lafiya kalau.” Shiru suka yi kamar basu saba ba, jin alamun kukan Aydah yasa tayi saurin yi mishi sallama ta kashe wayar. Saman goshinta ta shafa don kanta wani irin ciwo yake yi wanda take jin har wajen idanunta yake tabawa.
Haka ta kwanta sai dai har wajen ƙarfe uku bata yii bacci ba, tashi tayi kawai don tayi alwala ganin ya fiye mata kwanciya tana saƙe-saƙe.
Zabura tayi a waje ganin mutum na ƙoƙarin rungumar bango, sai kuma ya girgiza kai yace “Sorry Roshni na tsaya ƙyam salute!” Ya dan buga ƙafa yana daidaita tsayuwarshi, kafin yayi hanyar shiga ɗakin Kamalu, Umma tsorata tayi ta fara neman son yin ƙara taji yace “Shhhhh! Malama nine.”
Kallonshi tayi da mamaki tace “Kamalu? Me kake yi a waje a daren nan?”
Cike da takaici ya ƙaraso yace “Wannan kuma ba damuwarki bace ke da kike waje yanzu me kike yi?”
Mamaki me ya hanata magana don daga yanda yake magana ma ba wai kanshi ƙalau bane, ba dai zargin da ake yi mishi na yana shaye-shayen kayan maye da gaske ba ne? Tana ganinshi ya shiga ɗaki.
Alawala tayi ta koma ɗaki, a iya saninta Baba da wuri yake rufe ƙofa to tabbas ta katanga ya sauko kenan, Innalillahi lallai Kamalu bashi da kai dole a dage da yi mishi addu’ar shiriya, tasan yanzu tana yin magana za ace din taga ɗanta ya rasa ƙafa ne take neman ƙaƙabawa Kamalu laifi.

*****
Wayarta ta ɗauka tana jujuyata, jibi zasu je asibiti wurin Junaid sai dai tun yanzu tana ji zuciyarta baza ta iya haƙuri da rashinshi ba, ido ta runtse tare da jan bargo ta lulluɓe fuskarta, Nabeela ce ta girgiza kai tace “Allah Zeey akwai abinda ke yawo akan ki, anya kuwa.”
Juyowa tayi dukanta tace “Aunty Nabs ya zaka yi ka cire mutumin da kake tausayi daga ranka?”
Kallonta tayi tace “Ya zaka yi dai ka cire wanda kake so a ranka?”
Tsaki tayi tace “Ke fa matsalarki kenan sam baki fahimta to mu bar maganar.”
Sauka Nabeela tayi ta fito daga ɗakin hakan yasa Zeey sauke ajiyar zuciya, waya ta ɗauka ta kira Salim nan ta sanar dashi zuwan da zasu yi asibiti yace to zai zo da safe, tace “Yauwa bani number shi zan tura mishi text na abubuwan da zamu tafi dashi.”
Salim yace “To shikenan.” Zata yi magana taji muryar mace tana cewa “Waya kake yi?” Zee cike da tsokana tace “Wacece?”
“Habi ce ƙanwar Asiya saƙo na kawo mata.”
Da mamaki tace “Asiya?”
Gyaran murya yayi yace “Budurwar Baqeer tada.”
Mamaki ya kama Zeey tace “Me kake yi tare da kanwarta?”
“Saƙo kawai zan bata na juya, sannan ita babu ruwanta kinga duk abinda ya faru ma daga wurinta muka ji.”
Murmushi tayi tace “Anya kuwa saƙo ne kawai?”
Yasa dariya yace “A’ah fa ba komai tsakaninmu.” Nan suka yi sallama ya tura mata number Baqeer.
Sa wayar tayi a ƙasan pillow ta daki saman goshinta tace “No babu abinda zan yi, Zeey calm down and take a deep breath.” Nan ta fara breathing in and out tana cewa “Ba komai a raina, tausayi ne, tausayi ne, da kuma zumuncin Maryam.”
“Yaushe kika je gidan Maryam? Yaushe kika kirata ko a waya? Yaushe ma kika nemeta?”
Kai ta girgiza ta fito daga ɗakin da sauri babu kowa a falon, baki ta taɓe sam Inna babu ruwanta da ita, ƙofar ɗakin Inna taje ta ƙwanƙwasa.
Suna zaune ita da Nabeela suna hira suna dariya, kallon Inna tayi a shagwaɓe tace “Inna a dai dinga yi mini kara.”
“To ai ko ban miki ba kina yiwa kanki.”
Zama tayi kusa da ita tace “Hirar me kuke yi ni aka warenj?”
“Ba ji zaki yi ba, ke ni kam me yasa kike da son jin abinda bai shafe ki ba.” Shiru tayi don tasan Inna dama baƙar magana zata faɗa mata, ga mamakinta shiru ɗakin ya koma, jiki a sanyaye ta miƙe ta bar musu ɗakin tunda babu amfanin zaman nata.
Wayarta ta kalla ta kalli number Baqeer, taɓawa tayi nan da nan wani abu yazo mata hankali a tashe ta ɗauki wayar zata kashe, tana kai hannu zata kashe shi kuma ya kai hannu ya ɗauka, ido ta runtse da sauri ta kara wayar a kunnenta.
Baqeer wanda ke zaune a ɗaki wayarshi ce tayi ƙara, kallon sunan da yayi saving number yayi ‘ƙawar Maryam’ kallon wayar ya sake yi yana mamakin ashe tana da numbershi? Kenan tasan lokacin da ya kirata? Nan ya ɗauka yana son tabbatar da itan ce ko a'a don in haka ne lallai yayi abun kunya.
Zeey ganin ya ɗauka yasa ta zaro ido tare da sauke ajiyar zuciya, shiru yayi shima don bai san me zai ce mata ba.
A hankali tayi gyaran murya tace “Hmm nace na kira Salim.”
Yace “Toh!”
Toh? Ta maimaita a ranta sannan tace “Na sanar dashi maganar zuwa asibitin shine nace zan kiraka don na faɗa maka ka taho da takardun da aka baka a Aminu Kano.”
Ga mamakinta yanzun ma toh kawai yace, takaici ne ya kamata tace “Toh toh bye.” Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta kifa kanta akan pillow sai kuma ta ɗauki wayar tayi saving ɗin numbershi da ‘Toh’
Baqeer kuwa tana kashewa ya kalli wayar yace “Meye abun fushi to? Ba dai nace toh ba?” Ya ajiye wayar yana mamakin fushin na menene.

******
Washegari Umma ta bawa Hadiza dubu uku a cikin kuɗin nan sannan tace “Kije in muka yi magana da Maryam sai ki samu ko injin markaden ne ki siya ki fara sana’a don zamanki haka babbar illa ce.” Ita dai Hadiza taso ta sake kwana ɗaya amma babu halin yin hakan don ita kanta tsoron Baba take kada ya dawo yazo ya tarar da ita ga kuma karatun yara da babu yadda zata yi, takaicinta ɗaya ko waya bai yi ba balle ma ya nuna yayi dana sanin abinda yayi.
Haka ta fito riƙe da yaranta idanunta fal da kwalla, Jamila ce ke shara a tsakar gida, ganin Hadiza yasa tace “Dije tafiyar zaki yi?”
Kallonta tayi dao sam bata ma san me zata ce mata ba, Abu ce ta leƙo tace “Dije to kinga dai kafin ki maida ku zawarawa daga ke har uwar taki gwara ki lallaɓa ki riƙe aurenki da daraja, in kuma ba gidan Maryam zaki tare da zama ba ayi abun kunya.”
Mamakin kalamanta ne yasa Hadiza kallonta tace “Dadinta dai kema kin taɓa yin yajin.”
Baki Abu ta saki, ai kuwa kamar an tsungunota cike da masifa tace “Uban wa kike faɗawa haka? Ni? Eh lallai kam wuyanki ya isa yanka, lallai yarinyar nan, ba dai zugoki aka yi a ɗaki don kiyi mini rashin kunya ba ko?”
Ita dai Umma tana jinsu bata san magana don maganar ma ƙara tada husuma zai yi, daga ciki tace “Hadiza bana son shirme fa ki wuce ki tafi gidanki.”
Fita tayi ranta a matukar ɓace, ta tsani cin kashin da suke yi musu kwanan nan don kawai Ya Baqeer ya samu nakasa shikenan sai a maidasu kamar ba yaran gidan ba? Ita dai ko ina babu daɗi, wannan wace irin rayuwace?
Chapter 60 · 0% Book details