Sashe 108
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
****
Zee kuwa miƙewa tayi ta sauko daga kan gado ta zauna akan sofa ɗin ɗakin tana nazari, ya aka yi Daddy ya sani? Waya sanar dashi? Don dai kaf cikin wanda suka sani bata jin akwai wanda zai sanar dashi, fitowa tayi daga ɗakin kai tsaye ta nufi ɗakin Kabir, a kulle taji shi sai dai tasan dama da ƙyar in zai barshi a buɗe, hakan yasa ta nufi ɗakin Nabila saboda ta tabbatar ba Mummy bace wannan kam bama sai tayi tunani akai ba. Nabila har yanzu na nan kwance a inda ta barta, zama tayi a bakin gado fuskarta a tamke sosai babu alamun wasa take kallonta, kafin tace “Aunty Nabs ke kika sanar da Daddy?” Gaban Nabila ne yayi wani irin faɗuwa don sam bata tsammaci tambayar nan daga wurin Zee ba, zama tayi ta kalleta tana goge ƙwalla kafin tace “Ba….”
“Kar ki ce ba ke bace don Ya Kabir ba zai taɓa sanar dashi ba balle Mummy duk da kema bansa a raina zaki yi ba sai dai nafi tunanin ke akan su, na farko Kabir yasan in Daddy yaji shine zai shiga tashin hankali sannan mun yi dashi akan kwana biyu kenan gobe ne lokacin dana bashi, wanda nasan goben ma sai mun kai ruwa rana zai yarda a sanar.”
Cike da rawar murya tace “Nima ban sani ba mistakenly ne naje tura text ma Dr ashe Daddy na turawa ban kula ba, kin ga dukkansu D ne to ina kwance kaina na ciwo sam ban kula da wanda na turawa ba har sai da Daddy ya dawo ya kirani nan ya fara tambayata akan meya faru shine na sanar mishi, kema kin san wallahi a san raina bazan sanar dashi ba.” Kallon zargi Zee kawai take yi mata, mistake? Ganin bata gamsu ba yasa ta ɗauko wayarta da sauri ta nunawa Zee text ɗin wanda a ciki ma Dr ta rubuta akan ya zata yi da ciki ƙarami ba wanda ya sani a gidansu tana kuma tsoron aji.
Miƙa mata wayar Zee tayi kafin tace “A ina kika san Dr ɗin da har zaki yarda ki sanar dashi irin wannan babban sirrin?”
Nan ma wata faɗuwar gaban ce ta kamata, mamaki take yi yaushe Zee ta fara wayau haka? Don a iya saninta ta yarda da ita in har ta faɗa mata abu bata taɓa bincike take yarda, anya bata yi ganganci ba kuwa wurin tura saƙon nan? To amma kuskure ne ai ba laifinta bane, kallon Zee take cike da rauni tace “Na sanshi don sanda nayi BUK yana level 5 ina level 1 to muna shiri sosai, bayan ya fara aiki ma duk yawanci abubuwana wurinshi nake zuwa.”
Kai Zeey ta jinjina alamun fahimta duk da ta rasa me yasa zuciyarta ke shakku akan abinda ke faruwa, miƙewa tayi ta nufi ƙofa ta waigo ta kalli Nabila sannan ta fita, ɗakin Mummy tayi, daga waje tana juyo sababin da Daddy yake yiwa Mummy yana cewa “Kina zaune a gidan nan har yaron nan yayi wa yarinyar nan fin ƙarfi? Ke kin san yadda na yarda dake na jingina amanar gidana a hannunki ashe da abinda zaki saka mini kenan? Tun yaushe nake sanar dake yaron nan sam ban yarda da wasu daga cikin dabi’un shi ba?”
Mummy cike da tausayin Kabir tace “Senate ƙaddara ce fa Allah ya ɗauro mana wallahi ni nasan Kabir ba zai aikata abin nan da sanin shi ba, ka duba ka gani duk yawon da yake yi da ƴan matan da ke sonshi ka taɓa ji an kawo ƙararshi ance yana neman wasu? Ko kuwa duk matan dake sonshi za ace su basu kai Nabila bane? Allah shine shaidata ni nasan ba da saninshi bane sannan ita ma Nabilan ka daina bata gaskiya gaba ɗaya…….”
“Ba wani kema kin san Nabila dai bazata taɓa kai kanta wurin Kabir ba, yanzu me kike so ayi in har Inna taji? Bayan kece shaida dama tana jin haushin yadda na sakar miki kula da yarana. Tana ganin kamar ni na hanaki haihuwa."
Kamo hannunshi Mummy tayi tace "baza ma taji ba, in har babu wani abu ka bari suyi aure, ita kanta Inna baza tayi faɗa ba in taji aure suka yi kaga ko haihuwa tayi a ƙalla za ace ai ta haihu da wuri ne tunda cikin nan ƙarami ne, ina tsoron garin zubar da ciki wani abun ya faru ne, sannan in tsautsayi yasa Inna tasan abinda ya faru daga baya wallahi har ƙara zata iya kaimu kasan yadda take ji da Nabila.”
Zama yayi a bakin gado ranshi na ƙara ɓaci shidai gaskiya ba dai aure ba, ba wai baya son Nabila bane sai dai gaskiya ba zai bari su ƙare a gidansu Inna ba, shi ya auri Mummy ne don babu yadda zai yi wanda daga baya ya maida ita class ɗin da yake so, amma banda Nabila don ɗan shi gaskiya sai dai ya auri yarinyar da zata taimaka mishi a siyasa, ba wai wacce ba’a sani ba. Kallon Mummy yayi don ba zai iya sanar da ita dalilinshi na ƙin auran ba sai cewa yayi “Ki shirya zan kira Dr Suhail kuje a zubar da cikin nan, salin alin ba tare da wani ya sani, kinga daga nan ta koma wurin Inna kawai ni zan nema mata miji na nunawa tsara ayi aurensu cikin rufin asiri.” Mummy ta jinjina kai tace “Shikenan!” Jin haka yasa Zee ta bar wurin, ɗakin Kabir ta ƙara komawa don zuciyarta ta kasa nutsuwa, in har ita bayanta ya fashe haka da shatin bulala ina ga shi? Ƙwanƙwasawa tayi tace “Ya Kabir buɗe.”
Kamar bazai buɗe ba sai kuma ya buɗe bai jira ta shigo ba ya koma ciki ya zauna a bakin gado tare da haɗe hannayenshi waje guda, jingina tayi da jikin ƙofa tana kallonshi tace “Yanzu menene plans ɗin ka?”
“Banda wani plan kema kin san sai abinda Daddy ya tsara.”
Cike da takaici tace “Kai ma Yaya why? In mace kake so me yasa baza kayi aure ba? Yanzu fisabillilahi me ka jawo mana?”
Idanunshi da suka yi jaa ya ɗago ya zuba mata yace “Nake son mace a ina? Ke kinsan da a matse nake da tun kan ki dawo nayi aure, kawai bani da ra’ayin ajiye iyali ne yanzu.”
Ranta a ɓace da jin kalamanshi yasa tace “Ba kada niyyar ajiye iyali amma kana da niyyar yin fyade? Sannan a cikin gida? Ba kunya ba tsoron Allah, abinda Aunty Nabs ke ji....”
Cike da ɗaga murya yace “Wai kowa ni yake ɗaurawa laifi? Ita fa? Ko don ina namiji shi kenan nine mai yin komai? Kuna ina sanda take biyoni har ɗakin nan don na kulata? Kuna ina sanda take nuna soyayyarta a gareni ina rejecting ɗinta? Kuna ina sanda nake korarta daga ɗakina amma take ƙin fita? Ko don ni ban bayyana abubuwan da take yi mini ba shi kenan kuma sai laifi yayi ta zama nawa?”
Hankali a tashe Zee ke kallon Kabir tana mamakin jin kalaman dake fita daga bakinshi, kanta take ji yana wani irin sara mata, me take ji yana faɗa? Nabila? No way……..
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce*
*Da Ayusher Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA SHIDA*
{66}