Sashe 25
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Baqeer ne duk hankalinshi yaƙi nutsuwa, baya son ya cika zargi amma dole ne yayi, wayar nan ya ɗauka ya kira Salim, ringing biyu ya ɗauka jiki a sanyaye yace “Salim don Allah gobe idan Bello ya dawo ka taimaka kazo ka kaini inje in ganshi in dai har shi bai zo ba, ina sin sanin amsoshin tambayoyin dake kaina.”
Yace “Shikenan nima anjima zan zo dama na gyara ka.” Daga haka suka yi sallama ya maida kanshi kan katifa kawai yana addu’oin samun nutsuwa don zuciyarshi tuni take ƙissima mishi wasu abubuwan da bai dace ba.
Kamalu ne ya shigo gidan ranshi a matuƙar ɓace, bokitin dake tsakiyar tsakar gidan yayi fatali dashi wanda hakan yasa Abu fitowa da sauri, don ta ƙule cikin ɗakin ne tana hada sirrin matsi na ‘tif da taya’ wai in dai mace tayi amfani dashi da yamma suka sadu da miji to fa shikenan sun zama gamgam, bata so Jamila ta gani balle ta fara mata surutan banza “Kamalu?”
Ta faɗa tana yi mishi alama da yazo don dama nemanshi take yi, shiga yayi sai kumbura fuska yake cikin ƙunar rai yake cewa “Kinga Mama karki ɓatan lokaci don sauri nake yi ina so in ɗauki chager na wayata ne zan koma waje.”
Ƙofar ta mayar ta rufe bayan ta tabbatar babu wanda ya ganshi tace “Kamalu haka zaka zauna yanzu Bashir ya kwace fadar mahaifinku bayan Baqeer?”
Cikin kakkausar murya ta irin fitinanun mazan nan yace “Wannan ya rage nasu ni abinda ya dameni daban, suje can da yawarsu.”
Iska ta furzar tace “Kai matsalarka kenan sam ba’a faɗa maka kaji, ko so kake wulakancin daka sha shekarun baya ya sake faruwa?”
“Kinga Mama ba wulakanci ba suyi abinda ya fishi ma ni bai dameni ba, wannan ina zaune ya lalata ƙafa dan da ina da dama ma ni da kaina zan karya ƙafar da hannun to amma tunda wani ya rigani kinga na huta amma wannan mahaukacin ya rainani wallahi zaki jishi a maƙabarta.” Yayi maganar a fusace tare da buɗe ƙofar ɗakin zai fita, ji yayi tace “Kamalu magana nake yi maka fa?”
Kallonta yayi kawai ya fice tare da bugo ƙofar da ƙarfi, babu abinda ya tsana irin a dinga haɗa shi da mutane shi kenan daga a haɗa shi da wannan sai a haɗa shi da wancan to wallahi ba zai yiwu ba. Ɗakin shi ya nufa rai a ɓace.
Baqeer yana zaune bayan Salim yazo ne da zai tafi yace ya sakashi akan kujerar dake gefen table ɗin zanen shi, pencil yayi ta ƙoƙarin riƙewa sai dai hannunshi na gocewa, sam ya kasa taɓuka komai, kanshi ya dafa yana tunani, shi ba wani abin ya sani ba balle yace zai gwada wani abin, zanen nan kawai ya iya da kuma shi ya dogara, yanzu ya zai yi da rayuwarshi? Ajiyar zuciya yayi gashi an ɗauke mishi waya bai samu ya kira mutanen da suka amshi aikinshi ba tare da sun biya ba, da wanda suka amshi aikinsu suka fara biya basu gama ba, ya zai yi? Banko kofar da Kamalu yayi ne yasa ya kalleshi, a fusace Kamalu ya shigo yace “Uban me kake kallo?”
Baqeer ya kawar da kai dan baya son tanka mishi sam, hankaɗe table ɗin gaban Baqeer yayi yace “Wawa kawai in ma zaka farka daga shirmen mafarkin da kake to kayi ka farka don anyi gaba an wuceka, sannan daga yanzu na maka iyaka a cikin ɗakin nan kada ka kuskura ka wuce nan zagayen din nan ɓangarena ne.”
Ya ƙarasa maganar yana nuna mishi sashin da yake nufi, kallonshi kawai Baqeer yayi ya kauda kai wanda hakan ya sake tunzuro shi yace “Ni kake kawarwa da kai?”
Bai tanka mishi ba sai ajiyar zuciya da yake don shi yanzu komai na rayuwar nan mamaki kawai suke bashi, yanzu yadda zai yi ya samu kudi ya sayi magungunan da aka rubuta mishi yake nema, don a gabanshi aka bawa Baba takardar magungunan daya kamata a saya mishi amma har yau babu abinda aka bashi sai paracetamol da Umma tasa aka sayo mishi sanda ya dinga fama da yawan ciwon kai.
Takaici ne ya ƙara rufe Kamalu ya ɗauki charger wayarshi ya fito yana zazzaga masifa dama ranshi a matukar ɓace yake sakamakon tun safe yake yawon neman Zeey babu ita babu labarinta, duk wanda ya yiwa kwatancen yar masu kudi baƙa kyakkyawa sai dai a hankada shi wani gidan, akwai gidan da yaje ma kare ya biyoshi tun daga nan ranshi yake a ɓace gani yake ta leko ta koma Zee tayi mishi.
*******
Ɗakinta ta kulle tana ji Kabir nata bubbugawa har sai da Mummy tayi mishi magana sannan ya ƙyaleta, gashi dama Dad baya nan yaje Gombe taron jam’iyarsu.
Ko da Daddy yayi waya Mummy ce mishi tayi basu daidaita ba amma sun sulhunta tana saka ran inya sake zuwa su daidaita.
Takaici ya kama Kabir yace “Mummy wai ba zaki bari na farfasawa yarinyar nan baki ba? Haka zamu zauna tana mayar da mutane kamar wasu yaranta?” Fuska sosai Mummy ta ɗaure wanda hakan yasashi tashi yabar parlourn.
******
Washegari…….
Daf da magriba Bello ya sauka a Kano ta jirgin sama wanda murna da yake ciki ba zata misaltu ba, mahaifinshi da kanshi yazo ɗaukan shi a airport. Yallabai ya sake yi musu godiya da sanar dasu akan za’a kirasu wanda suka ci na ɗaya zuwa na uku a sake karramasu kafin a tallafa musu akan karatunsu zuwa kasashen ƙetare.
Nan suka shiga motar mahaifin Bello, basu fita daga airport ba yace “Bello meke faruwa? Baka sanar dani akan tafiyar nan ba? Sannan a iya sanina ba Baqeer bane mai zuwan?”
Ajiyar zuciya yayi yace “Baba nima ba’a son raina hakan ya faru ba, Baqeer yayi hatsari wanda ƙafarshi da hannunshi suka samu matsala, shine ya tursasani akan sai naje a madadin shi nima banyi niyyar zuwa ba ganin kamar hakan bai dace ba sai dai ya matsa don haka na tafi kawai.”
Jin kalaman Bello yasa hankalinshi ya ɗan kwanta, da sauri Bello yace “Shi yasa na kasa sanar daku don ni kaina kunya nake ji gani nake yi kamar ban kyauta ba.”
Cike da jin daɗi yace “Masha Allah wannan abotar taku tana sanyaya zuciyata Allah ya ƙara kareku, da hankalina ya tashi amma yanzu na fahimci MBB ma da kayi amfani dashi hala saboda asan shine kai?”
Bello yayi murmushi yace “Sosai Baba shine dalilina, don Allah ko zaka bari in sauka don ina son na fara nuna mishi sakamakon abinda ya mayar dani.”
Baba ya ƙarasa gida sannan yaba Bello key ɗin motar yace “Amma karka dade Goggonka na jiranka.”
Cike da jin dadi ya ja mota ya bar wurin.
Salim ne zaune shi da Baqeee sun kira Bello a waya har sun gaji bai ɗauka ba, Salim ya kira Baban Bello inda ya sanar dashi ai yana nan hanyar tahowa wurinsu. Mamaki ne ya kama Baqeer ya kalli Salim tare da ƙara kiran Bello sai dai yanzu ji suka yi ma wayar wai a kashe.
Habi ce ta kira Salim wanda ya ɗauka don sanar da ita tayi hakuri zai kira ta daga baya.
Sai dai me? Yana ɗagawa ta sanar dashi wai Bello yana ƙofar gidan su.
Kallon Baqeer yayi wanda bai san me ake cewa ba sai dai yanayinshi kaɗai zaka kalla kasan akwai zargin da yake yi, Salim na kashewa ya kalleshi, jinjina kai Baqeer yayi yace “Salim zaka iya kaini gidan su Asiya?”
Dafa hannunshi Salim yayi yace “Baqeer ka share kawai.”
“Please! Ganinsu ne kaɗai zai tabbatar da abinda nake tunani kuma shine zai ɗauke kokonton da nake yi akan su.”
Shiru yayi sai dai shi kanshi zuciyarshi ta kasa nutsuwa, Umma na murjin taliyar hausa da take yi in ta samu masu auna, so take ta samu kuɗi ta taimakawa Baqeer ya samu mai taimaka mishi da safe don bazai yiwu su cigaba da takurawa Salim ba.
Da mamaki ta kallesu tace “Sai ina?”
Salim ne yace “Zamu ɗan fita shan iska ne tunda duhu ya ɗan kawo kai.”
Kamar ta musa sai dai tace “Sai kun dawo.”
Haka suka yi ɗan tafiya kaɗan kafin su isa kwanar su Asiya duk cikinsu babu wanda ya iya tanka wa wani.
Tun daga nesa Baqeer yake kallon motar mahaifin Bello don kuwa rabin hawa motar sune suke yi, Salim ne yace “Baqeer don Allah mu juya.”
“Please Salim!” Yayi magana cikin wata karyayyiyar murya, suna tafe yana tuno rayuwar da suka yi da Asiya mai tsafta, harta gama boarding school shi ke mata shopping a ɓoye don iyayenta ba wani abun kirki suke iya saya mata ba to shi ke saya mata abubuwa da yawa, da yadda take tsananin ƙaunarshi, a rana in bai kirata sau biyar ba ta dinga tambayarshi ko lafiya? Balle rayuwarsu da Bello wanda ke cike da farin ciki, yawanci zancen da yake zuwa ma dashi yake zuwa.
Cak ya tsaya daga gefen gidan dake gaba da nasu kaɗan gidan mai kyau ne sosai dan fitilun gidan ne suka haske inda Asiya da Bello ke tsaye, daidai lokacin Bello ya matso tare da ciro award ɗinshi ya miƙa mata, wani irin murmushi ta saki ta ɗan jingina da gaban motar cikin farin ciki take yi mishi wani kallo, kafin daga bisani ya ɗauko waya ya fara ɗaukan ta hotuna tana tsaye rike da award din kai daga ka gansu kasan love ake sha.
Baqeer kanshi ne yaji yayi mishi wani irin nauyi, shekara kusan guda kenan yana ayyana wannan ranar yana cikawa Bello baki akan duk ranar da ya amshi award ita zata fara gani ya sakata a gaba yayi mata hoto, ashe ba shi bane hakan zai faru dashi Bello ne? Idanunshi ne suka canza launi sosai da sosai yana jin zuciyarshi nayi mishi wani irin zafi, ya zai yi da rayuwarshi? Ina zai saka kanshi yaji daɗi?
Asiya ya hango ta miƙawa Bello award ɗin ga mamakinshi hannunta ya riƙe ita kuma tana murmushin ta dake sanyaya mishi rai a baya wanda yake gani shi kaɗai take yiwa……