Sashe 64
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zeey cike da zumudi tace "Dada kalla ki gani?"
Amsa tayi cike da mamaki tace "Baqeeru yaushe ka iya zanen ɗinki haka?"
Kallon Zeey yayi kaɗan ƙasan ranshi yana jin wata irin nutsuwa, ashe dai yana da amfani? Ya ɗan kawar da kai yace "Ita ta faɗi ya take so ayi." Dariya Zeey tayi tana kallon Dada tace "Dada don na faɗa ai mai zanawa shine mai ƙoƙarin ko?"
"Dukkanku dai kun yi ƙoƙarin kai Masha Allahu." Tayi maganar tana komawa ciki zuciyarta na wani irin sanyi da nutsuwa. Zeey ce ta kalli Baqeer ta ɗan karkatar da kai tace "Tukuicin aiki fa?"
Kallonta yayi fuskarshi sam babu alamun fara'a yace "Ki bawa saurayinki." Yana kaiwa nan ya fara tura keken yana jin wani irin yanayi da bai taɓa ji ba, me yasa take karkatar da kai a gabanshi gashi tana neman ja mishi ciwo a zuciyarshi da yadda take bugawa da ƙarfi. Har ya shiga ciki Zeey tana kallonshi murmushi ya kasa barin fuskarta, wai saurayi? To wa kenan? Da yake ba shine a gabanta ba hakan yasa bata kula ba, sallama ta yiwa Dada tana jiyota daga ciki ta fito, wata irin nutsuwa take ji wacce ita kanta bata san daga ina take saukar mata ba, anan ta bar Salim don yace shi ba yanzu zai tafi ba. Kai tsaye wurin tailor dinta ta wuce, ta kai mishi dinki tace ya sayi atamfar da zata yi kyau da ɗinkin, don ita yawanci kayanta sai dai ko Mummy ta ɗin ka mata amma sam bata iya zuwa shopping ta sayi kayan mu na hausa ta kai a ɗinka don ita a ganinta babu abinda ya kai hakan ɓata lokaci da wahala, yanayin sa ne ya canza ya sake kallon takardar sosai yace “Hajiya waye yayi wannan zanen?”
“Menene?”
“Ai tun kafin a ɗinka ma hankalina ya tafi kai na tabbatar in aka yi ɗinkin nan tabbas zai yi kyau sama da yadda kike tunani.”
Murmushi tayi tace “Ka fara ɗinkawa sannan ni na kawo style ɗina ba kuma naso wasu su gani suce kayi musu irin shi, na dai yadda kayi tallan shagonka dashi amma ba ka ɗinka irinshi ba.”
Kuɗi ta bashi sannan ta fita hankalinta ya ƙara kwanciya jin yaba ɗinkin daya yi in har masu abu sun yaba alamu ne na komai yayi yanda ya kamata.
Wayar Mummy ce ta shigo wayarta wanda hakan yasa ta gangara gefen titi ta ɗauka cike da shagwaba tace “Mummy na!” Maimakon Mummy ta amsa sai tayi ajiyar zuciya wanda hakan yasa jikin Zeey yayi sanyi, kashe wayar tayi kai tsaye ta nufi gida maimakon ta koma gidan Inna.
Kabir ta gani a falo yana cin abinci ta jefa jakarta kan kujera tana tambayarshi inda Mummy take, wani kallo ya watsa mata yace “Sai yanzu kika tuna da ita sai da kika gama yawon gantalinki?”
Tsaki tayi tace “Matsalarka kenan kai maganar arziki ma baza ayi da kai ba, tayi ɗakin Mummy da sauri, a kwance ta ganta cikin bargo hakan yasa ta ƙarasa da sauri tana bin ɗakin da kallo wanda mai aiki ke ta faman gyarawa, kallonta tayi wani abu yazo mata tace “Ɗan bamu wuri.” Fita tayi hakan yasa ta ɗago Mummy, da sauri Mummy ta share ƙwallarta ta rungumeta tace “Baby kin dawo?”
Idanun Zeey ne suka fara canzawa sosai nan da nan ƙwalla suka cika taf a cikin idon tace “wani yazo daga Ɗambatta ne?”
Kai Mummy ta girgiza mata alamar a’a, Zeey baƙin ciki ne ya isheta ta goge ƙwalla tana sauke huci tace “Ba Daddy ya hanasu shigowa ba?”
“In Daddy ya hana ni na isa na hana ne? Haka kuma rayuwar zata kasance?”
Cikin takaici tace “Mummy please ki daina magana haka, sai yaushe ne zaki ƙwatarwa kanki ƴanci? Haka zaki zauna suna abinda suka ga dama? Kiyi hakuri Mummy tsautsayi ne yasa nima nace zanje wurinsu kwanaki na tuba bazan sake ba………” kuka ne yaci karfinta wanda ya hanata karasa maganar, Kabir ne dake tsaye jikin ƙofa shima tun dazu ranshi a ɓace yake yace “Mummy daga yau kema kar ki sake bari a buɗe musu ko gate ne sannan har Ɗambattan zan je wallahi enough is enough bama son akuyanci.”
“Akuyanci?” Mumy ta maimaita fuskarta a matukar ɓace, kai ya kauda kawai ya bar ɗakin don duk wanda zai taɓa Mummy to fa baza su yarda ba.
Mummy ce tasa hannu ta ɗago Zeey ta rungumeta tace “Ya isa haka nan please ba gashi kun zo ba? Ni ku kaɗai kun isheni rayuwa.”
Hawayenta itama ta goge tana kallonta cike da tausayi sam basa shiri da mahaifiyarta sannan ga mutanen can na Ɗambatta da suke kara takurawa rayuwarta, ya zata yi ta sanyaya ran mahaifiyarta?
“Mummy in dawo gida?”
Kai ta ɗaga da sauri tana riƙeta, murmushi tayi tace “Zan yiwa Aunty Nabs magana tazo in kuma bata zo ba bazan ƙara bin ta ba nima.”
Cike da jin daɗi Mummy ta ɗaga kai tana sake rungume Zee rungumar da sai ka ɗauka wani ne zai ɗauke mata Zee ɗin.
Waya ta yiwa Nabeela ta sanar da ita ta dawo gidan don Mummy bata jin daɗi, jin haka yasa tace zata zo itama, tana kashewa ta ƙira Daddy wanda yaje Abuja yau saboda wani taro. Yana ɗauka Mummy tayi saurin ƙwace wayar daga hannunta ta kashe tace “Zeey me kike yi haka?”
“Sanar dashi zan yi yayi musu magana.”
Ido Mummy ta zaro tace “Baki san yanzu akan haka tashin hankalin da zai sake faruwa yafi wanda ya faru ba? Bafa wani abun bane ya faru sosai.”
Cikin ɓacin rai tace “Mummy please! Nifa bazan bar wani abu ya sameki ba yanzu kalli har kwalbar turaren wuta an fasa nan gaba in wani abun ya sameki fa?”
“Babu abinda zai faru In Sha Allahu, ba dai gaki ga Kabir ba babu komai In Sha Allahu.”
Rungume Mummyn tayi tausayi na sake shiga ranta, dole ta kula da Mummy don bazata bari a cigaba da sa musu ita kuka ba da girmanta.
Nan ta kira mai aiki ta gyara wurin don Zee ko gyaran gadonta ba yi take ba sanda taje karatu sai dai in ɗakinta taga ya gaji da datti ta kira cleaner ta mata deep cleaning amma sam bata son aiki bare shiga kitchen, taɓ ai iya kacinta da kitchen to fa ruwan zafi zata dafa a kettle ko kuma abinci zata yi warming a microwave haka tayi rayuwa a school nan kuwa ruwan zafin ma sai dai tasa a dafa mata.
Ɗaki ta wuce ta kwanta tana jin zuciyarta har yanzu tana zafi, waya ta ɗauka ta kira Baqeer, yana zaune haka kawai yake sake auno Zee yana sake yin wani zanen ɗinkin mamaki yake yi yadda idea ta ɗinkin ke sake floating cikin mind ɗin shi, yana gamawa yaji wata idea ɗin ta sake zuwa, nan ya sake ɗaukan pencil ya fara, wayar Zee ce ta katseshi ya kalli sunan da yasa mata a hankali yayi smirking sannan ya ɗauka.
Shiru yayi itama shirun tayi kafin tace “Raina a ɓace yake.”
“Why?”
“Hmmm family issues.”
“Umm!”
Gyara kwanciyarta tayi tace “Shikenan abinda zaka ce?”
“Umm!”
Baki taɗan turo tace “Mutum ba kara, tambayata ya kamata kayi ko am alright?”
“And then?”
Ta ɗan yi jim kaɗan tace “Sai nace maka eh.”
“And?”
“Hmm sai ka tambayeni ina ina?”
“And then?”
“Sai ince ina gida.”
“And?”
Shiru ta ɗan yi kafin tace “Sai na tambayeka ni kuma, me kake yi?”
“And?”
Cike da shagwaba tace “And ɗin me? Allah ni har kasa ma naji bana son kalmar.”
Shiru yayi tace “Ka tambayeni to.”
“Ai kin bada amsa.”
Shiru tayi can tace “Allah wayau akayi mini ban yarda ba a sako daga farko.”
Bai yi magana ba hakan yasa tace “Kaji?”
“No!”
“Allah in nayi fushi baza ka ƙara ganina ba, in baka yi mini magana ba naiy counting 5 bazan sake nemanka ba nima.”
Nan ta fara “5,4,3,2,1,1,1,1”
Zata kashe yace “Okay!”
Cike da takaici tace “Shiyasa ma budurwarka ta gudu ta barka.” Tana kaiwa nan ta kashe wayar, kan gado ta cila ta don ita bata tauna magana ma take faɗa, haka Allah yayi ta komai ya fito bakinta faɗa take yi.
Baqeer ne ya kalli wayar maimakon yayi fushi sai murmushi ya suɓuce mishi, idanu ya rufe yanayin yanda ta langwaɓar da kai dazu kawai yake hangowa, shi kam bai san meke kanshi ba.
Zeey kuwa pillow ta cillar ƙasa tace “Allah nayi fushi.”
*****
Nabeela sai dare ta samu ta iso, Zeey da kanta ta kaiwa Mummy abinci a ɗaki, tana jinsu suna waya da Daddy kamar babu wani abu da ya faru da ita da rana, itafa ko aure tayi gaskiya bazata ɓoyewa mijinta komai ba dole yasan duk abinda ke faruwa ya kuma sanar da ita itama don bata son sirri a aurenta.
Jin muryar Nabeela yasa ta leko tace “Aunty Nabs ina wurin Mummy.”
Shigowa tayi ta dubata sannan ta fito ta bar Zeey a ciki, ɗakin Kabiru ta nufa fuskarta ɗauke da murmushi, yana zaune yana game a PS5 ɗin shi da yake ɗakin shi nada girma sai akayi mishi sitting area daga gefe kaɗan, knocking tayi ya amsa sannan ta buɗe.
A jikin kofa ta tsaya tace “Dama nayi tunanin game kake yi.”
Bai kalleta ba yace “Kin dawo?”
Kai ta ɗaga tace “Kayi tunanin abinda na faɗa maka kuwa?”
Kallonta yayi kaɗan ya ɗauke kai yace “Ba sai nayi tunani ba don its a big NO.”
“Ka tabbatar?”
Yana kallonta yace “Yes!”
Murmushi ta sakar mishi tace “Shall we make a bet?”
Kallon mamaki yayi mata yace “Na me?”
Tace “Na maganar mana, mu sake magana in 2months.” Tana kaiwa nan ta juya, ɗakin Zainab ta fara shiga ta gyara sannan ta koma nata ɗakin, exams ne da ita hakan yasa ta ciro books ɗinta ta fara karantawa.