Sashe 84
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
******
Badaru ne ya dawo daga kasuwa duk yana jinshi a gajiye, ganin abokanshi yayi a zaune suna hira da alama wani abun ne ke shirin faruwa, wajen yaje yana cewa “Ahh Malam Iro kune?” Ga mamakinshi ɗif suka yi kamar ba sune ke hirar nan ana dariya ba, nan fa ranshi yayi mugun ɓaci ganin sun fara watsewa ɗaya bayan ɗaya, nan fa ya sake kaiwa bango ya kalli Malam Iro yace “Wai har da kai? Wani irin cin zarafi kuke neman yi mini ne?” Malam Iro yayi gyaran murya yace “Kai matsalarka kenan faɗa da kuma zargi, zancen Bello muke yi da zai tafi ƙasar waje bayan auransu da kwana biyu to mun san halinka shi yasa muka yi shiru.” Ai kuwa kamar an taɓoshi ya fara cewa “Ya tafi sararin samaniya ma ba ƙasar waje ba, yo dama munafiki har ya isa a daraja shi? To sai me? Sai me in yaje? Ko banza dai da ba don ɗana ba bai isa ya zama wani ba, banzaye kawai munafukai.” Ya juya yana cigaba da zazzaga masifarshi, yana shiga gida kai tsaye ɗakin Fatima ya shiga, a lokacin tana waya da Baqeer tana yi mishi faɗa akan don me zai turo musu kuɗi bayan yana da abubuwan yi masu muhimmanci a gabanshi, ai tana jin muryar Badaru ta kashe wayar da sauri, sai kuwa gashi ya shigo rai a ɓace yace “Allah ya isa cutata da kuka yi, kun munafurceni yaron nan don baƙin hali ya hanani jin daɗin rayuwa wallahi sai kun san kun yi dani.” Umma cike da takaicin kalamanshi tace “Mallam yanzu ya dace ka riƙa yin magana akan ɗanka haka?” Yatsa ya nuna mata yace “Kafin na zabga miki mari kiyi mini shiru, kece ai baƙar munafukar.” Ya juya rai a ɓace ya bar ɗakin, wayarta taje ɗauka me zata gani? Ashe bata kashe wayar ba, hankali a tashe tasa wayar a kunne tace “Baqeer?” Kasa magana yayi kawai ya kashe wayar yana jin wani abu ya tokare mishi maƙoshi yana neman hanashi numfashi. A hankali ya shiga neman jawo numfashinshi yana sauke ajiyar zuciya, wayarshi ce tayi ƙara ya ɗauka Umma ce sai yaga Zeey ce, saƙo ta turo mai ‘In nawa ne thanks in ma ba nawa bane thanks’. Kallon sunan ta yayi yana tunanin yanda ta shigo rayuwarshi daidai lokacin da yake neman wanda zai fahimci halin da yake ciki, ta shigo rayuwarshi daidai sanda yake neman wanda zai nuna mishi hanya. Saƙo ta sake turowa ‘Me kace?’ Maimakon ya amsa mata sai ya kira Umma saboda ƙaramar nutsuwar da tazo mishi din yasan tana cikin wani hali yace “Umma karki damu, bansa abinshi a raina ba ina fata kema bazaki saka ba.” Bayan sun yi sallama ne taji hankalinta ya ƙara kwanciya Allah dai ya raya mata Baqeer ya kare mata shi.
*****
Zeey kuwa fitowa tayi daga ɗaki ganin Baqeer bai mata reply ba, kitchen ta shiga ta kalli masu aikinsu tace “Babba ni kam ya kuke tuƙa tuwo?” Da mamaki Mummy dake tsaye tace “Ke kuma me ya haɗaki da tuƙa tuwo?”
Kallon Mummy tayi sai kuma ta ƙarasa wurinta ta rungume ta tace “Haka kawai naji curiosity na son in sani nasan naga suna yi amma ban taɓa gwadawa ba.” Shafar kanta tayi tace “Kada ki wani damu da harkar kitchen ke ƴar gata ce duk mai aurenki ma sai ya amince da mai aiki sannan ni da kaina zan nemo mai aikin ke dai ki zauna cikin farin ciki kici kisha.” Nabeela ce ta girgiza kai cike da takaici tace “In kuma mijinta yace sai tayi mishi girki fa?”
Wani kallo Mummy tayi mata tace “Wannan kuma ba damuwarki bane, sannan in tayi auren in baya son me aiki sai na dinga aika mata abinci daga gidan nan, Nabeela wai ni kam menene matsalarki?” Kai kawai ta sake girgizawa ta juya, Zeey tabi bayanta da kallo. Hanyar ƙofar ɗakin Kabir tayi bata san Mummy ta biyota ba sai ji tayi tace “Uban me zaki yi anan?”
Waigowa tayi da sauri ta ɗan kalleta a tsorace kafin tace “Babu komai kawai airpod ɗinshi zan ara.” Wani kallo ta sake yi mata tace “Wuce kafin ranki yayi mugun ɓaci, wallahi kin sani nace a’a bana son hauka bana son rashin hankali da tunani.” A fusace tayi ɗakinta tana tunani ai zata tafi ta kwanta don haka dole ne taga Kabir babu mai hanata.
Zeey kuwa ɗaki ta shiga ta duba wayarta saƙon Baqeer ta gani yace ‘Me kika ce?’ Murmushi tayi tace “Inyi godiya?” Shima reply yayi mata “An yafe miki shi.” Bargo ta shige ta sauke ajiyar zuciya tana jin ƙaunar Baqeer na sake ratsata, gaskiya tana buƙatar hoton Baqeer a wayarta, especially in tayi missing ɗinshi.
A hankali ya shigo gidan don ya tabbatar sun yi bacci, tun sanda Nabeela tayi mishi kiss yake jin wata irin sha’awa na taso mishi, gudun ɓarna yasa yaƙi zaman gidan, hannunshi yaji an riƙo, dayake duk fitilun gidan a kashe suke yasa yace “Waye?” Jan hannunshi tayi zuwa ɗakinta, yana shiga dim light ɗin dakin yasa ya ganeta, ajiyar zuciya yayi yace “Nabee……” Sumbatar da ta kai mishi ne yasa ya kasa ƙarasawa….
😒Umm Asghar ne da Ayusher suka kalli juna suka ce "to meke faruwa ne"❓
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA BIYU*
{52}
Bai san lokacin da ya fara mayar mata da martani ba domin kuwa ta tayar mishi da wani tsumi ne da bai san dashi ba, tun da ta mamaye shi tayi mishi kiss ɗinnan shikenan ya shiga cikin wani hali, dauriya kawai yake yi amma sai yaji babu abinda yake da buƙata face son kasancewa tare da ita hakan yasa ya kasa tanƙwara zuciyarshi har yaga rashin dacewar abinda suke yi sai kawai ya biye mata suka cigaba da aikawa da juna zafafan saƙonnin da suka sake fitar dasu daga hayyacinsu, kafin wani lokaci har sun dire akan gadonta sai da tafiya tayi tafiya tukunna Kabir ya dawo cikin hayyacinshi ya tuna wacece Nabila a wurinshi da abinda suke shirin aikatawa. Hankaɗeta yayi daga jikinshi ya tashi ya mayar da suturar shi da tuni suka yi watsi dasu suka yi nasu wuri, ko kallonta baya son yi don baya son ganinta a yanayin da take ciki, shi ya rasa wace irin jaraba ce wannan duk yadda yake kakkauce mata sai da tayi nasarar ribatarshi, in banda Allah ya kiyaye yasan da ƙyar idan basu aikata ɓarna ba. Yana gama saka kayanshi ya fice daga ɗakin yana sauke ajiyar zuciya ranshi fal takaicin Nabila. Yana fita tabi ƙofar ɗakin da kallo tana jin takaicin haƙanta da bai cimma ruwa ba don ita a tunaninta idan har ta ribace shi wani abu ya shiga tsakaninsu dole Mummy ta haƙura ta ƙyalesu suyi aure don a ganinta Mummyn ce babbar matsalarta ba wai Kabir ɗin ba. Tashi tayi ta faɗa banɗaki ta kimtsa jikinta sannan ta fito tayi shirin kwanciya bacci ta haye gadonta tana tariyo abinda ya faru a tsakaninsu bada jimawa ba tana jin wani irin daɗi da shauƙi yana ɗibarta.
Shi kuwa Kabir yana shiga ɗakin shi ya dannawa ƙofar key don baya so Nabila ta ƙara mamayar shi ta shigo mishi ɗaki bai sani ba, yanzu in banda Allah ya kiyaye da bai san a wane hali zata saka shi ba gashi nan yanzu ta tayar mishi da abinda daa can kwata-kwata bai san dashi ba. Haka ya kasance cikin wani hali har ya dinga ji ko dai ya tashi ya buɗe ƙofar ɗakin ne watakila ta biyoshi sai dai kuma yana kwaɓar zuciyarshi akan wai me yake tunanin aikatawa, shin yana da tabbacin idan ta shigo ɗakin nashi zai iya controlling kanshi kamar yadda yayi a baya? Bai san lokacin da bacci ya ɗaukeshi ba ya dai saka a ranshi cewa dole ne ma ya taka mata burki idan ba haka ba taja shi ga aikata dana sani, shi kuma abinda baya fata kenan a rayuwa.