← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 168

Sashe 29

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sannu dai" Kamalu yace yana ɗaga mishi hannu. "Yauwa sannu" maigadin yace bayan ya fito waje ya janyo ƙofar ya rufe yana ƙarewa Kamalun kallo. "Lafiya dai ko? Wa kake nema?"
Wani kallo Kamalu ya jefa mishi irin na kada ka raina mini wayo kafin cikin maganarshi irinta gagararrun ƴaƴa yace "ka gane ba wato akwai Roshini ɗita wata ƴar black beauty nan haka tana jan wata jar Honda Accord ance nan ne gidansu, da Allah ita zaka yiwa magana kace mata Kamel ne yake sallama" yana yi yana gyara zaman rigarshi irin a dole shi ga gayu ɗinnan.
Wani irin kallon banza maigadin ya watsa mishi yace "Kai kama kalli kanka a madubi kuwa kafin ka fito? Anan gidan ne kake da wata Rashida take ko wa? Don Allah ɓace mini da gani tun kafin kayi mini sanadin aikina, in banda sakarci ma irin naka ta yaya kamar kai guntun ƙwaya da wiwi zaka ce kazo wajen wata ƴa a cikin gidan nan, ni wallahi da farko na ɗauka wajen Alhaji kazo irin ƴan bangar siyasar nan ne ashe wai kai wajen Rashida kazo, to babu Rashida a gidan nan sai ka ƙara gaba ko zaka yi dace da samunta a wani wurin.”Ya juya zai bar wurin Kamalu ya damƙo wuyanshi yana cewa "Kai kasan koni waye da har kake faɗa mini maganar banza? Kai matsiyaci ma maigadi har ka isa ka hanani ganin Roshni? Tun Roshnin bata fito ba har kana da bakin kore mata NI, to wallahi baka isa ba, ko ka shiga ciki ka kira mini ita ko nayi maka rotse a wajen nan.” Ya hankaɗa shi jikin gate ɗin yana sakin huci.
Shi kuwa maigadi yana jin an sake shi ya shaƙi iska ya kwasa a guje yayi cikin gidan ya datse ƙofar gate yana mayar da numfashin wahala don ba ƙaramar shaƙa yayi mishi ba.
Leƙa gate ɗin Kamalu yayi ta tsakankani, motoci ya gani yace “Ai Roshni ina auranki wancan zan amsa don babu shakka ita ta dace dani.” Ya sheƙe da dariya yana tuno wata ragwargwajajiyar motar Baba wanda ake faɗa akanta a gidansu, kafin yaja tsaki yace “Ni yanzu nafi karfin shiga Golf ɗin ku sai kuje can ku karata.”
Ya ɗan daka tsalle tare da sake kallon mai gadin yana ji kamar ya zabga mishi mari.
Horn suka ji daga cikin gidan da sauri Mai Gadi ya nufi wurin shi kuma Kamalu ya maƙale a lungu yana leƙe, ganin an fito da ɗaya daga cikin motocin nan yasa yabi wanda ke cikin motar da kallo, namiji ne da bai fi sa’anshi ba, huci ya furzar yana jin ina ma shine a cikin motar nan? Ko da yake an kusa ai.

An kusa me Kamalu?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

#Baqeer
#MBB
#Zeey
#Hawayen zuci
#Kaddara
#Kamalu KB
#AYUSHERMUHD
#UMMASGHAR

*BAQEER*
     *NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*

*PAID BOOK*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS*

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

08142800199
07068558096

{18}
Tun jiya da dare take dakon shigowar mai gidan nasu sai dai har lokacin barci yayi ta shiga ɗaki ta kwanta bata ji ɗuriyarshi ba, hakan yasa yau tun sassafe ta fito tsakar gidan ta zauna sanin halinshi ba wai ya kula da bin ɗakunan matanshi ya duba lafiyarsu idan gari ya waye ba, haka nan idan bada wani ƙwaƙƙwaran dalili ba baya taɓa shiga ɗakunan baccinsu sai dai su haɗu a tsakar gida idan kuma kece da girki ki iskeshi a ɗakinshi, ko wacce irin magana gareki sai dai ki faɗeta a tsakar gidan gaban kowa don bai yarda da bin bayanki don kuyi sirri ba, ita ce ma take da wannan alfarmar ada lokacin da ɗanta yake da mamora ba yanzu ba da ya gama yi mishi amfani yayi watsin ruwan tsarki da al'amarin da duk ya shafe su. Tana nan zaune Jamila ta fito ta hau kici-kicin ɗora abun karyawa.

"Ina kwana" tace mata ganin bata lura da zamanta a wajen ba. Waiwayowa tayi ta kalleta sai kuma ta taɓe baki tace "ke kuma lafiyarki kika fitowa mutane tsakar gida da duku-dukun safiya, ko kuwa dai wani sabon salon munafurcin ne kika ɓullo dashi". Bata tanka mata ba jin bata amsa gaisuwar da tayi mata ba sai ma wasu ƙananun magangnu data bita dasu. Jamila na aikinta tana sakin maganganu ita dai tana jan carbinta don tun zamanta dama abinda take yi kenan shi yasa ma zaman wajen bai gundureta ba. Har Jamila ta gama ɗumamen tuwo ta dama koko ta zubawa kowa nashi, sai sannan ta tashi ta ɗauke nata dana Baqeer ta kai ɗaki ta ajiye ta dawo ta cigaba da zama a ƙofar ɗakinta tana dakon fitowar Mallam ɗin.

Bai fito ba sai can da rana ta take ya fito da shirin shi na fita kasuwa. "Ina kwana Mallam" ta gaishe shi a ladabce cikin muryarta mai sanyi. Juyowa yayi ya kalleta ya watsa mata wani banzan kallo kafin ya juya yana miƙawa Jamila kuɗin cefanen su na ranar, ganin ya nufi hanyar fita yasa ta ɗan ɗaga murya tace "Mallam magana ce dani don Allah". A fusace ya juyo yace "sai aka yi yaya idan kina da magana? Ko kuwa saboda maganarki sai na fasa fita kasuwa, banda kinibibi da kutinguila sai da kika ga na gama shiri zan fita sannan zaki tsayar dani salon ki sakani makara, ko kuwa yau nake cikin gidan da baki samu lokacin magana ba sai da na fito zan fita".

"Kayi haƙuri" tace kanta a ƙasa. "Tun jiya nake tsumayen dawowarka har bacci ya ɗaukeni baka dawo ba, dama maganar komawar Baqeer asibiti ne da aka ce bayan sati shida a koma don a kunce ɗaurin da aka yi mishi zan yi maka ganin yau har an ƙara kwana uku akan sati shidan da aka bamu ban ji kace komai ba". A fusace cikin masifa da tijara irin tashi ya hau nunata da yatsa yana cewa "kinga Fatima ki kiyayeni, na lura raini kike neman kawo mini a cikin gidan nan, au bayan kin gama zuge ɗan naki yayi fatali da dukkan sadaukarwata a kanshi yaƙi yin abinda na sakashi shine yanzu zaki kwaso jiki ki tareni da batun mayar dashi asibiti? Don bance ku biyani kuɗaɗen da yasa nayi asara a kanshi ba shi yasa kike tunanin zan mayar miki dashi asibiti a kunce ɗauri, to ya dauwama a haka mana ina ruwana tunda dai babu wani amfani da zai yi mini na ƙare kashe kuɗina a kanshi a banza ba tare dana amfana da gina shin da nayi tayi ba sai ma nakasa da yayi yana nema ya ɗora mini wahala, to ba zan yi ba idan kinga zaki kai shi asibiti ban hanaki ba amma sisina ba zai ƙara yin ciwon kai a kanshi ba, sai ku gode abincina ma da yake ci a kullum ba tare da yayi wata wahalar nemowa ba, mtsew" ya saki wani dogon tsaki ya juya ya fice daga gidan yana huci kamar kububuwa.

Yana fita suka yi kaciɓis da makwabcin shi Mallam Nuhu, ɗauke kai yayi ya wuce kamar bai ganshi ba. Yana ƙoƙarin saka makulli ya buɗe motar yaji muryarshi daga bayan shi yana cewa "Mallam Badaru barka da asuba, an tashi lafiya?" Juyowa yayi irin kamar sai yanzu ya ganshi ya bashi hannu suka gaisa. "Kwana biyu bamu gaisa ba, ina taso na leƙo ma nayi maka jaje ashe tsautsayin da ya afkawa Baqeer kenan ban samu dama ba, wallahi Mallam Badaru sam bani da labari sai shekaranjiyan nan dana hange shi ana tura shi a keken guragu ake ce mini ai mota ce ta buge shi sanadin hakan har ya rasa ƙafafu gashi hannun nashi ma ya karye don haka ko gasar masu zane da zai je bai samu zuwa ba sai abokin shi ne ɗan wajen Alhaji Bala yaje a madadin shi. Allah ya kiyaye gaba ya mayar kaffara".

Tunda Mallam Nuhu ya fara magana Baba ya ƙara ɗaure fuskar nan tamau kamar bai taɓa dariya ba yana jifanshi da wani irin kallon wulaƙanci. Tsaki yaja yace "Ai sai ka kauce ka bani wuri tunda dai ka gama abinda ya kawo ka, in banda gulma da tsugudidi da can baka san Baqeer ɗin yayi hatsari ba sai yanzu zaka tareni da wasu zancen banza?” Ya buɗe motarshi ya shige ya jata a guje ya bar wurin yana baɗe Mallam Nuhu da ya bishi da kallon mamaki da ƙura, abun arziƙi ya taɓa zama na tsiya ne dama?
Chapter 29 · 0% Book details