← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 168

Sashe 61

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

******
Yau tun safe tayi wanka kai kace makaranta zata je, Zeey da aka sani da baccin safe amma yau ƙarfe bakwai tayi wanka, akwatinta ta buɗe bayan kanta ta shafa tana jin haushi bata wani kwaso kaya da yawa ba gashi tasan gobe dole ta koma don Daddy da kanshi ya kirata jiya yace ta dawo.
Zazzage akwatin tayi ta fito da ragowar kaya kala uku da bata saka ba, ɗaya atamfa ce sai biyu laces, tunani tayi kamar Baqeer bai taɓa ganinta da lace ba hakan yasa ta maida atamfar ta fara duba ɗinkin laces ɗin, light brown riga da skirt ne sam bata son saka kayan da zai takura mata shi yasa bata sa kaya da skirt amma haka nan ta saka shi, turarenta ta fesa ta shafa mai da kwalli sannan ta ɗaura ɗankwali, cike da mamaki Nabeela dake kwance akan gado take kallonta, can ta kasa daurewa tace “Zeey ba dai wata ƙasar zaki babu labari ba?”
Kallonta tayi tace “Wai kin tashi? Asibiti zani.”
Kallonta take da mamaki tace “Asibiti? Kina nufin duk shirin nan na zuwa asibiti ne?”
Kafaɗa ta ɗaga mata tace “Nawa ra’ayin kenan.”
“Wai skirt ma kika sa? Kai kamar ma ɗinkin da Mummy tayi miki wanda taso kisa da taron da aka yi last year kika ce baza ki saka ba tunda skirt ne?”
“To ko ma dai menene yau dai nasa zan tura mata da picture.” Zeey tayi maganar tana duba agoggo.
Ita gani take yi ma lokacin baya sauri “Karfe nawa zaki fita?” Nabeela ta tambayeta itama tana duba agoggo.
“11am ne appointment ɗin.”
Nabeela bata san sanda ta miƙe zaune ba tace “11 shine kika shirya tun 8? Eh lalai wannan da alama dai zance zaku yi ke da likitan.”
Murmushi tayi don ita kam bata san me zata ce ba kuma, da ƙyar ta haɗo tea ta sha don sun yi da Salim 10am zasu haɗu.

*****
Shi kanshi Baqeer yau da wuri yayi wanka ya gunguro kekenshi ɗaki yasa kaya, farar shadda yasa mara nauyi irin mai shara-shara ɗin nan, jin Dada tana ta fama a waje yasa ya fito, ganinta yayi tana surfa wake, yanayin fuskarshi ne ya canza yana kallonta yace “Dada me kike yi hakan?”
Dariya tayi tace “Baqeeru ka fito? Ranar naji Zainabu na maganar ƙosai shine…..”
Ai bai san sanda ya katseta ba yace “Dada shekarunki nawa da zaki yi surfe? In tana so ki jira in tazo sai kuyi tare ko kuma in yara suka zo su tayaki, amma fisabillilahi menene hakan? Salon wani abun ya sameki kuma?” Ya ƙarasa maganar yana nufar inda take, amsar taɓaryar yayi yana kau da kai fuskarshi a ɗaure ya fara bugawa da yake ba iyawa yayi ba gashi a zaune sai turmin ke ta rawa, yanata dukan gefe, dariya tayi tace “Wai da gaske bari nayi inga ko zaka amsa ashe kuwa zaka amsan, ahh Baqeeru kaga shikenan matarka ta huta.”
Bai bata amsa ba sai suka ji sallamar Salim, kallon Baqeer yayi cike da zolaya yace “Shi kenan zamu fara sanar da mutane ana surfe a gidan Dada.”
Baqeer wanda idanunshi suka haɗu da Zeey dake shigowa kawai ya ɗan kau da kai, yanzu me Dada ta jawo musu wannan abun kunya har ina? Aga namiji babba kamarshi na surfe?
Dada ce tasa dariya tace “Shi kenan ba kaga ni na huta ai, Zainabu wai ƙosai zan yi miki kafin ki dawo shine yake tayi, Baqeer ni kam an gama surfen ne? Naga ka tsaya.”
Kallon Zeey yayi kamar ita tayi maganar kafin ya kalli Dada kawai ya ajiye taɓaryar. Dariya tasa ita da Salim, nan suka fito Dada na zolayar shi har suka shiga mota.
Baya ta zauna shi da Salim suna gaba, Baqeer kallonta yake son sake yi sai dai babu dama don tabbas gani yayi kamar yau tafi ko wace rana yi mishi kyau, to wai shi meke damunshi? Kada dai ka manta ƙawar Maryam ce.
A jikin wani shago suka tsaya na ɗinki Salim ne zai amshi sako, Baqeer  ne ya zubawa shagon ido yana kallon yadda suka yi kwalliya da ɗinkuna daga waje, sam hankalinshi ya tafi wurin kalin styles. Zeey idanunta na kanshi tana kallon yadda ya zubawa shagon ido cike da kokonto tace “Ya Baqeer naji ance zane kake yi, kana zanen kaya?”
Waigowa yayi ya kalleta, idanuwansu ne suka haɗu da juna, idanun Zeey dake ɗauke da kwalli ya kalla, wani abu ne yake ratsa zukatansu wanda su kaɗai zasu iya kwatantawa a hankali yace “Haven’t tried it yet amma ina ga I can do it, meya faru?”
Ta ɗan yi murmushi kafin tace “Yauwa! Akwai ɗin kin da nakeso ne ni duk masu ɗinkin dana kaiwa teloli da yawa sun kasa yi mini abinda nake so am sure in kai ka zana zai yi.”
Zai yi maganar Salim ya buɗe ƙofar hakan yasa su yin shiru gaba ɗaya………

ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*

*BAQEER*
     *NA*
*AYUSHER MUHD*
            *DA*
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA TAKWAS*

{38}

Har suka ƙarasa asibitin babu wanda ya ƙara yin magana cikinsu sai Salim da jifa-jifa yake jefo musu hira ganin duk sun share shi yasa yaja bakin shi ya tsuke shima, cikin ranshi dai tunani yake to me ya faru a tsakanin su daga fitarshi da ya sakasu canjawa lokaci ɗaya har haka. Asibitin private physiotherapy clinic ne mai kyau da mahaifin Junaid ya buɗe mishi tun kafin dawowarshi ƙasar aka kuma zuba ma'aikata da kayan aiki masu kyau da inganci aka fara aiki tun Junaid ɗin bai dawo ba. Suna shiga cikin reception ta fito da wayarta daga cikin ƴar ƙaramar jakar hannunta tayi dialing number Junaid, tana fara ringing kamar wanda yake jiran kiranta ya ɗauka. "Hey babe, ya aka yi?" Ɗan yamutsa fuska tayi kamar yana ganinta jin ya ambace ta da babe, "Gamu mun ƙaraso muna reception.”

"Ok, ku tambaya a nuna muku office ɗina sai ku shigo.” Kashe wayar tayi ta mayar cikin jaka sannan ta ƙarasa wajen receptionist tayi mata bayanin abinda Junaid ɗin yace. Tashi tayi ta rakasu har ƙofar office ɗin sannan ta juya tana mamakin su kuma waɗannan ɗin su waye da suka shiga wajen chairman direct, ga dukkanin alamu dai VIP ne don ba kowa yake yarda ya gani ba. Sun shiga office ɗin da sallama, ya taso ya tare su yana murmushi. Hannu ya miƙawa Salim suka gaisa sannan ya bawa Baqeer hannun shima yana tambayarshi yanayin jikin shi, kamar baya so ya amsa mishi da 'lafiya' don haka nan yake jin takaicin Junaid ɗin bare daya lura da wani irin narkakken kallo da yake bin Zainab dashi. Wajen zama ya nuna musu Zeey da Salim suka zauna shi kuwa Baqeer yana zaune akan wheelchair ɗin shi dama, kallon ƙaton office ɗin Salim yayi yana jinjina tsaruwarshi da yadda aka kashe kuɗi wajen zuba kayan aiki a ciki, ya tabbata ba don Zeey ba basu isa su samu ganin Junaid ba bare har ace shi da kanshi zai ke duba Baqeer, to ai ko asibitin baya jin zasu iya zuwa saboda daga gani da ido ma an san ba wajen zuwan mai ƙaramin ƙarfi bane don zai yi muguwar tsada ko daga yawan kayan aikin daya gani kawai.

Kallon Salim yayi ya miƙa mishi wata takarda da yayi rubutu a jiki yace "Please abokina ko zaka je reception kayi musu magana a buɗe mishi file yanzu sai ka kawo min.” Tashi yayi ya karɓi takardar ya fita. Sai sannan yayi wa Zeey magana yace "Ga alama dai yau nayi laifi tunda Zeey ta shigo ko kallona bata yi ba,” yayi maganar yana sakar mata ƙayataccen murmushin shi mai tafiya da tunanin ƴammata. Harara ta watsa mishi haɗe da turo baki gaba ba tare data tanka mishi ba abinda ya ƙara ƙular da Baqeer don sai yaga shagwaɓa ce kawai Zeey ke yi mishi duk kuwa da bata buɗi baki tayi magana ba. Dariya ya saki yace "Hoo Zeey, wai don Allah da gaske fushi kike yi dani? To me nayi miki ne hum, faɗa min, kin san fa bana jurewa fushin ki please kiyi haƙuri ko ɗan murmushi ne kiyi min.” Sai sannan ta ɗaga dara-daran idanunta ta kalleshi sai kuma taji kunyar gwasaleshi tunda dai tasan babu abinda yayi mata kawai dai tana tauna tsakuwa ne don aya taji tsoro, ita tasan Junaid da gaske yake son ta sai dai ita kuma she can't give him anything more than friendship bare a yanzu da take ƙalubalantar kanta da sabon yanayin data tsinci kanta a ciki, ba zata so Junaid ɗin ya zura jiki a sonta ba alhalin she cannot reciprocate his feelings bayan haka ma bai wani girme mata ba ita kuma tun asali bata taɓa jin sha'awar yin soyayya da saurayin da bai bata wasu shekaru da yawa ba. Murmushi ta saki tace "laifin me zaka yi mini, kawai dai i'm not in the mood ne.”
Tafa hannushi yayi yana dariya yace "Ashe kuwa yau za'a yi ruwa da ƙanƙara, dama akwai wani mood da zaki shiga ya hanaki surutu? Kece kuwa Zeey ɗin dana sani ko kuwa dai wata ce me kama da ita?”
Chapter 61 · 0% Book details