Sashe 109
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Girgiza kai kawai take yi ta kasa gasgata abinda kunnenta ya ke jiye mata, ta yaya ma za'a yi ace wai Nabila ke bibiyarshi, Nabila dai data sani wannan mai yawan nutsuwar da kamun kai wacce kullum idan Daddy zai yi mata faɗa da ita yake yin kwatance yace tayi kwaikwayo da kyawawan halayenta ko yace bata ganin yadda Nabila take girmama manya ga son aiki saɓanin ita da bata iya komai ba sai son jiki ga rashin iya magana, kai ba zai taɓa yiwuwa ba ba dai Nabila. Wani irin kallo tayi mishi ta juya zata bar ɗakin sai jin muryarshi tayi yace "Kenan kin fi yarda da ita akan ni ɗan uwanki?" Juyowa tayi ta kalleshi ya ɗaga mata kai yace "Ribar me zan ci idan nayi mata sharri akan abinda bata yi ba, ki yarda dani Zainab wallahi ita ta riƙa bibiyata idan kin lura zaki ga na rage yawan zama a gida to wallahi duk saboda ita ne, ko ƙarfe nawa zan kai a waje idan na dawo gida zan tarar da ita tana jirana ko ta shiga ɗakina ta laɓe kuma duk a hakan ban taɓa gwada nemanta da wani abu ba saboda babu son ta a zuciyata don haka ban taɓa jin sha'awar kasancewa da ita ba, ita ta fara nemana da wannan rayuwar a cewarta romance kawai zamu yi, tun ina kaucewa har nazo na biye mata kuma wallahi ni ban yi mata fyaɗe ba tunda dai kin san bana shaye-shaye bare tace na sha wani abu daya fitar dani daga hankalina har na afka mata ban sani ba. Please Zainab ki yarda dani idan har da gaske cikin dake jikinta nawa ne ki yarda to ba fyaɗe nayi mata ba da yardarta da amincewarta komai ya faru." Gaba ɗaya fuskarshi ta koma kalar tausayi, lokaci guda duk ya rame yayi wani iri alamun yana cikin tashin hankali mai girma wanda sam bata kula da hakan ba sai yanzu. Ita tama rasa tunani guda ɗaya da zata yi, gaba ɗayansu daga Nabilan har Kabir ɗin kowa idan ya tara maka zance sai kaji shine mai gaskiya. Fita tayi taje ta ɗauko first aid kit ɗinsu ta dawo ɗakin sai ta samu ya cire rigar jikinshi ya kwanta akan cikinshi, gaba ɗaya bayanshi ya kwaye tsabar dukan da Daddy yayi mishi. Hankali a tashe ta ƙaraso cikin ɗakin tace "Me yasa ka tsaya yayi maka irin wannan dukan kamar ya samu jaki baka gudu ba?" Zama tayi akan gadon ta wanke mishi ciwukan tana yi tana mitar don me yasa zai tsaya Daddy yayi mishi irin wannan dukan gashi nan duk ya farfasa mishi jiki. Shi dai yana jinta halin damuwar da yake jin kanshi a ciki ne yasa ya kasa amsa mata.
Haka ta wanke mishi duka ciwukan sannan ta tashi ta fita da first aid kit ɗin, kitchen ta shiga tasa masu aiki suka dama mishi oats ta ɗauka ta kai mishi, da ƙyar ta matsa mishi ya tashi ya sha sannan ta ɓalli paracetamol ta bashi yasha har jikinshi ya game da zazzaɓi me zafi sai rawar sanyi yake yi, rufe shi tayi da duvet ta fita ta rufe mishi ƙofar ganin alamun shi kamar bacci yake son yi.
*****
Shi kuwa Daddy yana barin ɗakin Mummy ɗakinshi ya koma abun duniya ya taru yayi mishi yawa, shi yanzu ya zai da abun maganar da Kabir yake neman janyo mishi ace kamar shi ɗanshi yayi wa ƙanwar matarshi ciki. Tashi yayi ya hau zagaye a tsakar ɗakin shi yana neman mafita, gaba ɗaya yana cikin tashin hankali, tension yayi mishi yawa, ga yawon campaign daya sako shi a gaba ko zaman gidan baya samun yi soaaigashi Kabir yaje ya ɗauko mishi wata maganar. Tunani yayi tun kafin maganar cikin nan taje kunnen Inna tace dole sai Kabir ya auri Nabila gara ya nemo mishi mata yayi maza ya aurar dashi. Kai gaba ɗaya ma zai aurar dasu ya huta haka kurum ba zasu janyo mishi magana ba, dama uban Junaid ya daɗe yana so suzo a saka rana shine yake watsar da zancen saboda yafi son a samu fahimtar juna sosai tsakanin Zainab da Junaid ɗin amma yanzu tunda haka ne zai basu dama su fito a tsayar da rana kawai ayi bikin cikin ƙanƙanin lokaci, babu mai janyo mishi matsala a harkar siyasar da yake ganin akwai nasara a cikin tsayuwarshi takara.
Wayarshi ya ɗauka ya ƙira mahaifin Junaid, bayan sun gama ƴan gaishe-gaishensu irin na tsofaffin abokai da suka aminta da juna yace mishi dama akan batun auren Junaid da Zainab ne idan sun shirya su fito a tsayar da rana don baya son abun ya ɗauki lokaci so yake yi ayi auren tare dana Kabir kafin lokacin zaɓe yayi. Sosai baban Junaid yaji daɗi don dama abinda suke ta fata kenan suga auren tilon ɗan nasu da matar da yake matuƙar so. Suna gama waya ya ƙira Junaid yayi mishi albishir, duk da maganar tazo mishi a bazata sosai yayi murna don bai taɓa tunanin Zeey zata sauko da wuri ta amince mishi aurenta ba ganin yadda ko wayarshi yanzu ba koyaushe take amsawa ba. Yana asibiti lokacin da Babanshi yayi mishi wayar haka ya sallami sauran patients ɗin shi akan ba zai iya dubasu a yau ba sai dai su dawo gobe ya tafi gida zuciyarshi cike da ɗokin son ganin Zeey.