Sashe 101
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Baqeer kuwa yana kwance akan katifarshi tunanin Zeey da halin damuwar data shiga a ɗazu ne suka tsaye mishi a ranshi, yasan ba ƙaramin abu ke damunta ba tunda har ta iya yin kuka a gabanshi bayan kasancewar ta very jovial mai yawan raha da son wasa da dariya. Wayarshi ya janyo ya tura mata text, "Are you okay?" Ya ajiye wayar a gefe ya lumshe idanunshi yana tunanin abubuwan da yake son yi idan ya gama makarantar koyon ɗinkin daya shiga, bai sani ba ko kuɗaɗen daya ajiye zasu ishe shi buɗe shago ya kuma zuba irin kekunan da yake so domin a tailoring school ɗinnan an koya musu amfani da kekunan yin designs kala-kala yana kuma son ya zuba su a shagon da yake son buɗewa sai dai matsalar kuɗi ce zata kawo mishi cikas. Ƙarar shigowar text ne ya katse mishi tunanin da yake yi. Cike da ɗoki ya janyo wayar yana doka murmushi tun bai ga abinda ta rubuto ba don dai ya tabbatar message ɗin daga wajen Zeey yake.
"Am good" kawai ta rubuto. Ajiyar zuciya yayi sai dai har yanzu hankalinshi bai gama kwanciya ba da amsar data bashi. Kafin yayi typing reply wani message ɗin ya shigo.
"Me kake yi har yanzu baka yi barci ba?"
"Sketching?" Ta ƙara turo wani saƙon.
"Nope" ya mayar mata. Sai kuma ya sake tura mata "Ke me kike yi har yanzu da baki kwanta ba?"
"Tunanin assignment ɗin daka bani ne ya hanani barci."
"Ya Baqeer ba zaka faɗa mini ma'anar assignment ɗin ba? Please👋."
Murmushi kawai yayi, bai san lokacin da ya samu kanshi a halin da yake ciki ba amma dai ya sani a yanzu Zainab ita ce farin cikin shi, ba zai iya cigaba da rayuwar da babu ita a cikinta ba. Sai dai idan ya tuna ba lallai ne ta so shi a yadda yake ba ya zama gurgu, nakasashen mutum kamar yadda wasu suke kiranshi sai yaji hankalinshi ya tashi don ya tabbata tausayi ne kawai yasa ta shigo rayuwarshi bata jin abinda yake ji a kanta a cikin zuciyarshi.
Emoji na dariya😆 ya tura mata kawai.
Tana ganin abinda ya turo ta mayar mishi da emoji na fushi😠 ta ajiye wayarta tana murmushi. Kasancewarta tare da Baqeer na sakata cikin shauƙi yana bata nishaɗi shi yasa hankalinta bai kai kan abinda ke faruwa a cikin gidan nasu ba. Da yin wannan tunanin ta nemi duk wani farin ciki da ta samu kanta a ciki ƴan mintuna ƙalilan da suka wuce ta rasa. Bata so zuciyarta ta riƙa kaita wurin da bata so amma ta kasa yakice tunanin daya ginu a cikin zuciyarta sai dai abinda ta ganarwa idonta yasa ta kasa yakice hakan, bata so hasashen da tayi ya tabbata don tasan idan har ya tabbata hakan ne ba ƙaramin tashin hankali zasu shiga ba. Kai to su ta yaya ma zasu bari har hakan ya kasance? Tashi tayi ta fita zuwa ɗakin Kabir don suyi magana saboda gaba ɗaya hankalinta ya kasa kwanciya, gara taje taji daga bakinshi cewa tunaninta ba daidai bane ko ta samu kwanciyar hankali. Tana murɗa ƙofar ɗakinshi taji ta a kulle, knocking tayi ta haɗa da kiran sunanshi. Sai da ya tabbatar muryar Zeey yaji sannan ya taso ya buɗe ƙofar, murya a cunkushe yace mata "lafiya?" Ba tare daya bata hanya ta shiga cikin ɗakin ba.
"To ka bani hanya na wuce mana ha'an, ni magana nazo muyi." Ta tureshi ta shige cikin ɗakin ta zauna akan sofa. Sai da ya leƙa yaga babu wanda ya biyota sannan ya koma cikin ɗakin ya mayar da ƙofar ya rufe da makulli. Zama yayi akan kujerar dake kallon wacce take kai yana kallon Zeey yana jiran yaji dame tazo ɗakin shi a wannan daren, itama kallon nashi take yi tana kokawa da zuciyarta akan ta tambayeshi ko kuwa dai ta ƙyale shi sai dai tasan ba zata samu nutsuwar zuciya ba idan har ba tabbatar da gaskiya tayi ba. Zamanta ta gyara ta ƙara nutsuwa saboda abinda take shirin faɗa mishi da tasan idan har zarginta ne kawai ba wai gaskiyar kenan ba sai sun samu gagarumin saɓanin da bata hango shiryawarsu kwana kusa ba.
"Kai ke da alhakin yiwa Aunty Nabs ciki ko?" Kawai ta samu kanta da watsa mishi tambayar ba tare data shirya ba ko ta tsara ta yadda maganar zata fito ba.
A firgice ya ɗago yana kallonta sai dai ya kasa buɗe baki ya amsa ko ya musanta zargin da tayi mishi. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" tace haɗe da tashi tsaye hankalinta a tashe tana nuna shi da ɗan yatsa. "Kenan da gaske kai ne kayi mata ciki Yaya Kabir?“ Da sauri yace “Zainab please! Ita ta faɗa miki? Sannan wai hauka nake yi da zan aikata hakan?”
Wani irin kallo tayi mishi cike da tuhuma tace “Unfortunately I don’t trust you, muje wurin Daddy a sakaku a gaba aji meke faruwa.”
Hankalinshi ne ya sake mugun tashi da sauri ya tsaya gabanta yace “Wai kece uwarta? Sannan nace ba ni bane a wani dalili zaki dage akan Shirmen tunaninki?”
“In ma shirme ne in ma ba shirme bane muje gun Daddy kayi bayani.”
Tsaki yaja ya koma kujera ya zauna yace “Kanku ake ji ke da Nabilan, ai dai ni nasan ba ni nayi ba so ya rage naku ita zaki zubarwa mutunci ba ni ba.” Yayi maganar cike da dauriya don kar ta gane halin da ya shiga.
Saman goshinta ta shafa yanzu kam ta tabbatar akwai abinda ya shiga tsakaninsu, din a iya saninta in har Kabir bai san komai ba in ta faɗa abu na farko da zai tambaya shine ciki? Ciki ne da ita? How? Ta yaya? Tunda dukkansu sun san wacece Nabila sannan ya kamata ma ya ɗauki maganar tata a matsayin hauka amma ganin yadda hankalinshi ya tashi yasa ta gasgata tunaninta.
Nan da nan taji hankalinta ya ƙara mugun tashi, tsoro ya ƙara kamata, cike da ɓoye tsoronta tace “Wallahi kai kasan bazan bar maganar nan ba, Ya Kabir kada dai kace mini fyade kayi mat…….” Rawar da muryarta keyi ne yasa ta kasa ƙarasawa, ganin yanayinta ya taso da sauri ya ƙara dawowa gabanta, wani mugun kallo tayi mishi kafin yayi wani tunani ta sharara mishi wani irin mari tana yi mishi wani kallon tsana da ƙyama……..
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA BIYU*
{62}