← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 168

Sashe 23

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Tun daga bakin gate Zainab tana parking ta hango Nabeela, tana tsayawa da motar ta ƙaraso da sauri tace "Zeey ya muka yi dake?"
Maimakon ta tanka mata key ɗin motar kawai ta bata tace "Whatever! Ni raina a ɓace yake please."
Da kallo Nabeela ta bita harta shiga ciki bata iya bin bayanta ba, A ƙofar shiga taga Mummy, kusa da ita kawai taje ta rungumeta tace "Mummy ni kam me yasa mutane basu da kirki ne?"
"Ki ajiye batun mutane kin san yau me kika nemi ja mana a gidan nan kuwa? Tunda Dad ɗinki ya dawo yake faɗa, me nace miki akan in zaki fita? Ba nace ki tabbatar kin sanar min ba?"
"Oh yeah! Na tuna amma inda naje yana da muhimmanci ba wai yawon banza naje ba Mummy kin dai sanni."
Ajiyar zuciya tayi tace "Shi yasa nace ki dinga sanar mini ɗin ai tunda kin san Babanki ba yarda zai yi ba."
Zata yi magana taji an daka mata tsawa "Uban wa ya baki izinin fita ba tare da sanina ba? Sannan tun kafin ki dawo ba na sanar dake ba ke babu fita ke kadai ba? Ko kina tunanin wasa nake yi?"
Idanunta ne suka yi raurau tace "Dad nasan nayi laifi amma......"
"Amma me? Ke wato ba'a isa a faɗa miki magana kiji ba ko? Daga dawowarki ko jira baza kiyi ma mu gama murnar zuwanki ba zaki dawo da halin naki ko?"
Hawayenta ta share don tasan inta tambaya ma ko zata mutu ba barinta zai yi taje ba shi yasa ta sulale ta fita ta ɗauka zata dawo da wuri kafin ya dawo amma babban uzuri ya hanata, cike da faɗa yace "Wuce ciki kuma wallahi kika sake gigin fita ba da izinina ba kin san sauran don shirmen da kika yi a baya a unguwar nan da maganar da kika janyo mini a yanzu bazan sake ɗaukanshi ba.”
Idanunta ne suka ciko da kwalla tayi ɗakinta da gudu kawai ta faɗa kan gado, Mummy ce tabi bayanta tana shiga itama ta shiga ɗakin, kusa da ita ta zauna tasa hannu kawai tana shafa bayanta alamar lallashi, cike da takaicin abinda ya faru ta ɗago tana hawaye tace “Mummy nasan nayi laifi amma aƙalla a tambayi ina naje ko? Sannan asan dalilin daya sa na fita, ban san me yasa Daddy yake yi mini haka ba….”
Hannu tasa a saman bakinta tace “Dalilin kenan, Zeey bakinki ba zai yi shiru ba? In mahaifinki na magana ba zaki yi shiru kice ayi hakuri ba? Kin bari ɗabi’ar turawa ta shiga kanki kin manta da wacce muka baki?”
Kallan Mu8my tayi tana share hawayenta tace “Mummy kema kin san ba haka bane tun kafin na tafi karatu muke samun saɓani da Dad sam baya yi mini uzuri.”
Ajiyar zuciya tayi tace “Taurin kanki ne baya so, in har kika saukar dashi zaku zauna lafiya, sannan bakinki, ki taimaka ki daina faɗar duk abinda ya fito daga cikinshi.”
Kallon Mummy kawai take yi tama kasa magana sai hawaye kawai da take zubarwa, share mata tayi tace “Yanzu in kinaso ku shirya gobe Najib zai zo don sunyi magana da mahaifinshi ki tabbatar kin bashi hakuri kun daidaita, Zee dan Allah kar ki ƙara jawo mana matsala.”
Tana kaiwa nan ta miƙe ta fita ta bar Zeey a zaune kawai tana hawaye.

*****
Abu ce ta shige cikin ɗakin ta yau kwanan Jamila ne tasan kuma yanzun nan zata lalaɓo ta fara ce mata ta bata kayan mata ita kuma yanzu babu abinda zata iya bata tunda dai kambun Fatima ya rushe dole ne ta ƙwace Malam ya dawo gareta. Daga waje take jiyo kiran da Jamila ke mata cikin magana irinta raɗa “Abu! Taimaka ki miƙo mini saƙon da Hajiyar Sokoto ta aiko miki.”
Kwafa tayi tasa hannu ta ɗauko gutsiran tuwon alkama da sukai, tasa a ƴar farar leda ta shiga murza tuwon sai da ya fashe sannan ta ɗauko zuma ta zuba a ciki ta sake murzawa kafin ta ƙulle ledar, fitowa tayi tana dariya tace “Ke ina can ina nemo miki maƙal-maƙal kina nan kina nemana.”
Washe baki Jamila tayi ta amshi ledar tace “Kai Abu Allah dai ya bar mini ke ya raya mana Kamalu mu sha biki.”
“Ameen gashi nan kisa da audiga kin dai sani abu shar kayan mu ba wasa.”
“Heee! Ai har wani tsuma nake dole mu dawo da Malam hanunmu.” Tana faɗa tana fita waje cike da jin daɗin abinda ke faruwa “To kar dai muji ihun Malam yana sambatu.” Jamila sheke da dariya jin kalaman Abu tace “Ke dai wlh baki ji kisa audiga a kunnenki.” Ta ƙarasa maganar tana fita.
Abu ta ja tsaki da harara tace “Banda rainin wayau ɗakin Baqeer kin ƙwace kin bawa ƴaƴan ki kin haɗa Kamalu na da shi yanzu kuma mijin kike son ƙwacewa, wannan kuma kin yi kaɗan wallahi.” Ta juya tana cigaba da masifa a ranta.

*****
A rikice Baba ya shigo cikin ɗakin lokacin Baqeer na zaune ya sa karatun Al-Qur’ani a waya kawai yana sauraro yana yi yana kallon Kamalu wanda har lokacin yake kwance yana bacci har Salim yazo ya taimaka mishi yayi wanka yaci abinci yayi sallah a zaune amma bai tashi ba,  jin yadda Baba ya shigo a rikice ne yasa gabanshi ya shiga faɗuwa, ba dai wani wurin za’a ƙara kai shi ba ko?
“Waye wannan kamar Bello?”
Kalaman Baba daya juyo kenan a kunnuwanshi yana maganar yana miƙa mishi wayarshi, hannayenshi biyu ya miƙa duk da yasan bazai iya amsa da hannun daman ba. A guje Kamalu ya tashi ya afka banɗaki don yasan yanzu Baba zai ci mutuncinshi.
Da mamaki yake kallon hoton dake jikin allon wayar “Ba Bello bane ko kuwa idona me ke yi mini gizo?”
Kallon Baba yayi sannan ya sake kallon rubutun ƙasa da aka rubuta wanda yaci gasar zanen da akayi a yanzu haka a garin Abuja.
Da sauri ya kalli Baba wanda ya ke kallanshi cike da takaici yace “Duba da kyau me aka rubuta a kasa?”
“MBB?”
Kallan Baba ya sake yi da sauri wanda ya fizge wayarshi yace “Ya maka kyau! Gashi dai abokinka ne yayi amfani da sunanka ya maye gurbinka kuma alamun da ya bayyana a fuskarka ya tabbatar mini baka sani ba, sanda nake hanaka nuna mishi sirrinka kaji magana ta? Allah ya kara yanzu gashinan ai duniya ta juya ma baya.”
Yawun bakinshi Baqeer ya haɗiya yana jin wani abu mai ɗaci na sake taso mishi “Yanzu ga ka nan a kwance shi kuma fa? Gashi can ya maye gurbinka, ka fake da wata karaya ka kasa taɓuka komai, sai kayi ta zama a nakashe baƙin cikin da ka sakani baka fara ganin komai ba, malalaci kawai.”
Yana kawi nan ya juya ya fita, hannu Baqeer yasa a sumar kanshi yana jin wani irin zafi na taso mishi, ya maida hannun saman ƙirjinshi dake yi mishi wani irin raɗaɗi, idan Bello ya faɗa mishi zai maye gurbinshi yasan ba zai hana ba tunda idan ma bai je ba wani dai za'a tura to amma me yasa ya ɓoye mishi cewa shi zai je gasar a madadin shi? Ba dai shima gudunshi yake yi ba saboda abinda ya faru? Ko kuwa abinda Baba ke yawan faɗa mishi ne ya tabbata akan ya daina yarda da abokai? Iska ya shiga furzarwa da sauri cikin ƙarfi sakamakon jin da yayi numfashinshi na neman ɗauke wa.
Umma ce ta shigo da sauri don tunda taji kiran da Baba ke yi mishi tasan ba lafiya ba, karshe ma jinshi tayi a tsakar gida yana sababi akan ai dama shi yasan hakan zai faru, gashi nan kuma abinda yake tsoro ya afku, cikin sauri ta nufi ɗakin ganin halin da yake ciki yasa ta ɗauki littafi da sauri ta fara fifita mishi fuska wanda da ƙyar ya samu numfashinshi ya daidaita, kallonta yayi idanunshi sunyi jaaa yace “Umma na!”
Ta goge kwallarta tace “Baqeer dole kasa dauriya a zuciyarka, abubuwan dake faruwa da kai yanzu ka fara ganin su in har baka ɗauki dangana ba baza ka taɓa samun salama ba.”
Kai ya ɗaga mata yace “In sha Allahu Umma, tun jiya na fara sawa kaina wannan tunani amma Umma kina ganin Bello ma munafurtata yayi?”
Ajiyar zuciya tayi tace “In ma yayi kanshi ya yiwa, rayuwar nan nawa take? Ni ban damu da wani abu ba Baqeer ɗina nake so naga ya dawo daidai.”
Kallonta kawai yayi don bai san me zai ce ba.kuma, ta miƙe ta fita don bata son daɗewa a cikin ɗakin sanin Kamalu a ɗakin yake.
Tana fita kuwa sai gashi ya fito daga wanka yana fito, kallonshi yayi ya kwashe da dariya yace “Shalele yaya? Abubuwan sun ƙi daidaituwa ne?”
Baqeer bai tanka shi ba ya ɗan matso yace “Yarinyar jiya ka santa ne?”
Da mamaki ya kalleshi yace “Kamar ya?”
“Naga ta shigar maka faɗa ne har da yi mini shafar soyayya shine nake son tabbatarwa ko ƙanwar abokinka ce.”
Kai Baqeer ya kawar cike da takaici, Kamalu yaja tsaki yace “Kai sai faɗin ran tsiya kace baka sani ba ne bazaka iya faɗa ba? Wallahi na dai faɗa maka in har kana son kwanciyar hankali ka tabbatar ka bani girma stupid kawai nakasashe.” Ya ƙarasa maganar yana zura kaya, sallar asuba da azahar ya haɗa sannan ya ɗauki wayarshi ya fita, dole ne ma ya shiga neman yarinyar nan lungu da saƙo don banda tunaninta babu abinda yake yi tunda ya haɗu da ita.
Takaici ne ya kamashi daya fito yaga Bashir yana ƙoƙarin shiga motar Baba wato shi sam yaran gidan nan sun rainashi, shi kenan da hawa babur, cikin tsawa yace “Kai Bashir bani key ɗin nan ka hau babur.”
Da yake duk sun san halinshi yasa bai yi mishi musu ba haka ya miƙa mishi makullin motar ya amshi na babur ɗin, fuskarshi ya sake shafa inda Zeey ta mareshi dole ne yaje ya nemota ya tabbatar inta ganshi a mota shima zata kulashi.
Chapter 23 · 0% Book details