Sashe 15
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
******
Zainab ce tai wata irin miƙa sannan ta cire abinda ke rufe da idanta na sleeping mask, tunda ta shiga jirgi take bacci sai dataji an tsaya ta farka, kallan waje tai sannan ta ɗan saki murmushi, ta ɗauko madubi tana kallan fuskarta wacce ta dan gyara da zaman ɗan kwallinta.
Macece baka sai dai ba mai duhu can sosai ba, kana ganinta zakaga tsayinta irin tsaka-tsakin nan ne, batada jiki sai dai tana da shape ɗinta, sanye take da english wears na riga doguwa maroon colour har gwiwa sai wando datasa na jeans ta ɗau ra dankwali shima maroon, sai yanzu ta ɗauko wani karamin mayafin baki ta sa a saman kanta, wayarta ta zaro a gefen jakarta ta kunna, fitowa tai janye da suitcase ɗinta fara, airpod ne a kunnenta tana waya, cike da sakalci tace "Mum na iso Allah duk na gaji."
Tai maganar tana tsayawa jikin wani shop dake gun inda tasai juice na gwangwani, ƙoƙarin buɗe wa take ga kuma wayarta dake riƙe, ga jakar hannunta da kuma wanda take jaa.
Mum ce tace "Kinga wanda muka turo ɗin? Mundai tura miki hotonsa tun jiya.”
Da mamaki sai ta hangoshi yana nufo inda take, alama tamai da hannu akan ya ƙara so da sauri, aifa guy ɗin ya kara hanzari yana tafiyar niggas irinta samarin dake ji da kansu, kayan da yake sanye dashi da trainers ɗinshi kaɗai zaisa kasan ɗan masu kuɗi ne dan kuma riga t Tommy Hilfiger ne ga takamin Adidas.
Tace "Mum gashi ma ya iso."
Cike da jin daɗi tace "Please Zeety wannan karan karki wulakantashi yaran babban mutum ne Babanshi yana ganin mutumcin Dad ɗinki.”
Zeey ce ta katse ta jin tana cewa "Please ja jakar, inata jiranka kana tafiya kamar bakai breakfast ba."
Da mamaki guy ɗin yake kallanta sai dai ya amsa baisan ya nuna gazawarshi, juice ɗin ta miƙa mai tace "Ɗan Buɗe min hannuna."
Baki ya ɗan buɗe cike da mamaki ya amsa ya buɗe ta amsa daga hannunshi tana sipping tace "Yauwa Mum kikace me?"
Acan kuwa Mum ta runtse ido tace "Zeey please ya isa haka."
Sai tace "Okay sai mun iso."
Kallanshi tai wanda da alama kunya yake a ganshi yana binta a baya, dan ta kula sai saurin matsowa daf da ita yake dan su jera, kallanshi tai tace "Yauwa yama sunanka? Jamil? Jamal?"
Takaici ya sake kamashi yace "No ni sunana Najib."
Ta jinjina kai tace "Ohh! Yaushe Dad ya daukeka aiki? Hope dai personal driver ɗina ne kai dan inada abubuwan yi."
Cak ya tsaya yace "What? Driver? Na miki kama da driver?"
Waigowa tai tace "Then?"
A kufule yace "Ba'a turo miki hoto na bane?"
"Ooops! Anturomin, wai kaine dama?"
Hanci ya fara hurawa ta fara kunshe dariya tace "Sorry! Sorry! Amma kamar filter kasa a hoton ko? I’m not trying to be rude amma you look different.”
Jakarta ya tura mata daga inda yake yace "Mene?"
Wuyanta ta ɗan shafa tace "Kamin kama da driver ne da Dad ya min magana akan zai ɗaukar min kafin na dawo."
Nabeela wacce ke makale a gefe tana kallansu ta ɗan daki goshinta kaɗan tana girgiza kai tare da furzar da iska, dariya ta fara tana ƙara sowa ta dafata tana matsa kafaɗarta cikin magana kasa ƙasa tace "Ya isa yi shiru kafin ki ƙarasa lalata komai."
Zeey da ƙarfi tace "Ouch! Me nai? Jamal ranka ya ɓaci?"
"Najib nace miki sunana." Yai maganar cikin ɗaga murya, nan kawai ya juya ya fara tafiya da sauri Nabeela ta bishi tace "Dan Allah kayi hakuri bata ganeka bane, bawai wulakanci tama ba."
Ai bai kulata ba yai gaba yana huci kamar shi? Kamar shi babban yaro a maidashi wani gaja?
Waigowa tai ta zabgawa Zeey harara wacce ta ɗan ɗaga kafaɗa alamar oho.
Haka suka fito Zeey tana dariya ita ko a jikinta, a hanya Nabeela tace "Zeey wai haryanzu bazaki daina wulakanta samari ba? Sai yaushe ne zaki bar abin nan?"
"Sai sanda zuciyata ta aminta da abinda nake so, Aunty Nabs please mu bar maganar, to ya gida? Ina Nan?"
Ajiyar zuciya Nabeela tai tace "Da kin ɗauken a matsayin Auntyn da kinji magana ta ai."
Dariya tai tana danna waya tace "Ke fa dariya kike bani, nafa girmeki da 8month."
"Ko dai kin girmeni dai ni kanwar Mumyn ki ce."
Dariya sukai a tare haka suka cigaba da tafiya suna hirarakinsu sam Zeey bata tauna magana take faɗa kuma kanta tsaye sai dai kai maganar ta ɓata ma rai amma ita ko a jikinta.
Zeey ta kalli Nabeela bayan sun shigo unguwarsu tace "Please kaini shago a layin nan na sai abu."
Da mamaki tace "Meyasa baki faɗa da wuri ba? Da munje store."
"No bana san can, simple abu zan siya."
Tace "to"
****
Baqeer sun samu sun fito shi da Salim kamar yanda suka tsara sukacewa Umma wai iska zaisha a waje, sunyi sa'a Baba bai dawo ba.
Asiya kuwa ta fito ita da Habi wacce tace zasuje shagon Sidi su siyowa innarsu abu wai tsoron fita take ita kaɗai suna tafe Asiya na masifa akan ta sakata ta fito ba tare da ta yi niyya ba, suna isa turus tai ganin Baqeer daga lungun shagon, kallan Habi tai wacce tai saurin fara tafiya. Neman juwaya tai Baqeer da sauri yace "Asiya please!"
Dawowa tai ganin inba tayi da gaske ba bazai kyaleta ba.
Daga kusa dashi ta tsaya ta ɗan kauda kai yace "My luv nasan halin dana shiga ne ya jefaki cikin wani hali sai dai mu sani haka Allah ya kaddara mana ba yanda....."
Katseshi tai da sauri tace "Ya kaddara ma dai! Baqeer kalleni hanna yena da kafafuna garau suke, ko ina zan iya zuwa da kaina kuma ko me nake so zan iya zama indai nasa kaina, mena cema akan ka nemi wani aikin ka ajiye shirmen zanen nan? Cemin kai zane ma sana'a ce, to yanzu ga hannunka ya samu matsala taya zaka cigaba? Ga kuma kafarka wacce har abada a keke zaka kare kaga kuwa kaine ke dauke da kaddara ba ni ba."
Mamakin kalamanta ne suka hanashi cewa komai da kyar yace "Me kike nufi?"
Tace "Abinda kake tunani kaga please ka daina ƙirana kaje kaji da yanda zaka amshi kaddararka bani ba, aurenka zanyi ko jinyarka?” Tana kaiwa nan ta fara tafiya, cikin sauri ya fara tura keken nashi da hannun hagu dan Salim ya ɗan basu guri yana tsaye a shago yana jiransu.
Da sauri ya tsaya ganin mutum a gabanshi, Zeey bata san sanda ta fara kunshe dariya ba tana girgiza kai, ashe ta fito a shago taga abinda ke faruwa ita kuma da san abin dariya kawai ta tsaya tana kallansu.
Baya tai ta kaucemai tana sake kunshe dariyarta, Baqeer ne ya sauke idanunshi da sukai jaa a kanta, da sauri ta ware hannu tace "Oops sorry!"
Ta fara tafiya tana magana ƙasa-ƙasa "Maza sai ka rasa irin kwakwalwarsu, clearly kasan ba sanka ake ba ta kuma nuna ma tunda kai gurgu ne batayi, amma inaa kan nan ba komai.."
Karaf a kunnen Baqeer a fusace yace "Me kikace?" Yai maganar cikin daka mata ɗan tsawa.
Ƙofar mota ta buɗe tace "Sorry no time."
Ayusher Ce 🏌🏻♀️
Da
Ummu Asgar
Baqeer
#Shalele
#Asiya
# RayuwadaKaddara
#Hawayena
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600 -
Uku 1200 -
Biyu 1000 -
Ɗaya 500 -
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
Promo zai kare zuwa wani satin, garzaya kisai naki🙌🏻💃🏻
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
BAQEER🦼
NA
UMM ASGHAR
DA
AYUSHER MUHD
DADANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA
Kallon inda Asiya ta fara tafiya kawai yake yi baki a sake, jikinshi na wata irin rawa da tsuma ta tsananin tashin hankalin daya tsinci kanshi a ciki yanzun nan, shi maganar yarinyar can ma bata ɗaga mishi hankali ba irin maganar da Asiya tayi. Cikin rawar murya yace "Me kike nufi kenan Asiya? Saboda Allah ya aiko mini da ƙaddara kike nema ki gujeni? Ina alƙawarin da muka yiwa juna na duk rintsi duk wuya muna tare babu abinda zai iya rabamu, shine yanzu zaki janye maganar saboda kinga Allah ya mayar dani haka?"
Yai maganar wani siririn hawaye mai ɗumi ya biyo gefen idonshi ya silalo kan kumatun shi, yana jin wani irin ciwo mai zafi na damƙa a cikin ƙirjinshi har ma fiye da yadda yaji lokacin da aka sanar mishi da ƙaddarar data same shi, dan tunda yake rayuwa bai taɓa tunanin akwai abinda zai sashi rabuwa da Asiya ba, komai na rayuwar shi da ita yake ginawa, dame akeso yaji?